0⃣1⃣0⃣

211 18 8
                                    

FOLLOW ME PLEASE🙏, IT WON'T TAKE YOU MORE THAN 2 SECONDS.





💐IMRAN💐
ƘIRƘIRARREN LABARI✔️

~Wannan shafin sadaukarwa ce zuwa ga Amiratuoo . Har yanzu na kasa gano kalaman da suka fi cancanta gurin nuna godiyata agareki. Ke ɗin ta musamman ce, ke ɗin tabance. Nagode sosai da irin karamcin da kikai min. Allah ya bar ƙauna!.
Itace Marubuciyar shahararren littafinnan JASMINE, idan mutum bai karanta ba yayi missing. Sannan yanzu haka ta fara updating sabon littafinta mai suna ALAƘAR MU.




SHAFI NA GOMA

Dawowar A.A Abdullahi kenan daga Masallaci yin Sallahr Magrib yayi daidai da isowar Amina bakin gate tayi horn kamar ta san da mutum a gurin, buɗe ma ta ɗan matsakaicin gate ɗin yayi ta shiga ta faka Motar ta wanda dama ba tare da wani tunani ba idan ta zo sai dai ta sauka da kanta ta buɗe gate ɗin tunda basu da mai gadi, zata iya ƙirga sau nawa ta taɓa yin horn Jummala ta zo ta buɗe ma ta, akan Abban Ubaid kam wannan shine karo na farko, tunda duk inda zata je indai ba wani sha'ani ake a dangi wanda yakamata ta kwana ba, bata wuce ƙarfe shida bata dawo gida ba, Abban Ubaid kam sai ya kai bayan Magrib ko Isha'i kafin ya dawo, idan ya dawo da wuri ne ya dawo ana gab da Sallahn Magrib.

Tana fitowa Abban Ubaid na ƙarasawa gurin ya rungumeta yana ma ta sannu da dawowa. Bayan ya raba ta da jikinshi ne ya riƙe hannunta yana faɗin...

“Sannu da ƙoƙari, ya jikin ɗan naki?. Dafatan dai ya sake samun sauƙi?...”

Ya jero mata tambayoyin ba tare da buƙatar amsar ɗaya kafin ɗayan ba. Hakan ta lura ɗabi'arshi ne tunda ta san shi. Dama ɗazun da ta kirashi da rana da buƙatar ya ɗauko Ubaid daga Makaranta ta faɗa mishi farkawan Yaro da kuma halin da yake ciki.

“Ya samu sauƙi Insha Allah tunda ya farfaɗo. Doctor dai ya mishi Allura yace yana buƙatar ya ƙara samun Hutu. Da alamun abinda ya faru da shi gagarumin abu ne da ya matuƙar taɓa mishi zuciya, faruwan abinda nake jin cewa ashekarun shi yayi ƙanƙantar da zai fara fuskantar su...”.
Ta dakata tana ƙoƙarin saisaita yanayin ta da mai da hawayen tausayin Yaron da ya cika idanunta yana yunƙurin zubowa. Duk da ƙoƙarin da tayi hakan bai hana hawayen bin gefen idanunta yana silalowa ba. Daddy ne ya sa hannu ya tallabo fuskarta yana sanya babban yatsar shi gurin goge hawayen, rungumeta ya sake yi yana tapping bayanta yana faɗin

“Allah ya bashi lapiya. Allah ya sauƙaƙa mishi ƙaddarar da zai fuskanta nan gaba a rayuwa”.

Da "Ameen!” Mummy ta amsa kafin ta raba jikinta da nashi tana zagowa gurin booth ɗin Motar ta buɗe tana fito da Basket ɗin abincin da ta tafi da shi asibitin domin Yaron, har ta bar asibitin bai farfaɗo ba yasa ta tafi da shi kawai, tunda ta kira Jummalan ta yi ma ta bayani akan kwanan da zata yi a asibitin da kuma kan abin da zata girka musu da daddaren, ta ba AlMajirai wannan ɗin kawai tunda suna zuwa watarana, ko kuma ta bawa Jummalan idan zata tafi ta biya ta gida ta baiwa Innarta. Da wannan tunanin suka shiga cikin gidan Abban Ubaid na taimakawa wurin buɗe ma ta Ƙofa suka shiga da Sallama. Ɗaki Daddy yayi yayinda Mummy kuwa ta wuce kitchen ta tura ƙofar da Sallama abakinta Jummala na amsa ma ta.
“Sannu Jummala. Sannunki da gida”.
Ta faɗi tana gani daidai lokacin ne Jummala ta gama girka abinda take girkawa tana sauke shi daga kan electric.
“Sannunki da dawowa Mummy...”. Ta faɗi tsakanin kashe Electric ɗin. Da 'Mummy' take kiranta tun lokacin da ta fara aiki a gidan lokacin Mummy nada cikin Ubaid, ita kuma a lokacin tana Junior secondary school Wanda Rasuwar Mahaifinta shine sanadiyya.
Gashi yanzu har ta gama ta zana SSCE bata da halin cigaba. Tana da burin karatu don ta zama wani abu a rayuwarta, ta tsaya da ƙafafunta kuma ta taimaki Innarta da ƴan Uwanta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 01, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

IMRANWhere stories live. Discover now