0⃣0⃣8⃣

155 14 9
                                    

💐 IMRAN HAUSA NOVEL 💐
🍀An Untold Love and Politics Story 🍀

Ina yasmiinhajara!, Wannan shafin naki ne!, Kiyi yadda kike so da shi. Nagode da irin soyayyar da kike wa wannan littafin, Allah ya amfanar dake da darussan da ke cikinta...

Yaku Masoyan wannan littafin, ina mai baku haƙuri bisa jinkirin da littafin yake samu na cigaba. Zanyi iya bakin ƙoƙarina gurin ganin an samu canji mai ma'ana ta yadda zaku dinga samun update akai akai. Nagode da Soyayyar da kuke yiwa wannan littafin!🙏. I LOVE YOU ALL!❤️



SHAFI NA TAKWAS

Amina Abdullahi ita ce Mata ga Abdullahi Abdullahi Abdullahi, kuma Mahaifiyar 'Ubaid. Asalin ta Shuwa 'Arab ne. Suna da dangantaka da Alhaji Idris ne wanda ya riƙe shi. Ya haɗu da ita ne a wani sha'anin Aure da aka yi cikin dangi wanda bayan sun fahimci juna ne aka ɗaura musu Aure. Duk da kuwa yadda ba kowa ya yarda da sanya ɗan shi a karatun boko ba a wancan lokacin musamman ma Mata, amma dai dai gwargwado karatun ta da tayi na secondary da kuma wanda take da shi na islamic ya sa take wayayyiya kuma gogaggiya a Al'amuran rayuwa.

Sai da suka shafe shekaru kusan biyar a tare ba su samu haihuwa ba, har sai da ƴan uwan Idris ɗin da suka zamto danginsa da komai na sa suka fara magana akan zai fi kyau ya ƙara Aure tunda ba shi da kowa, yakamata ya tara zuri'a, amma ya ƙi, tunanin da yayi na samun haihuwa a hannun Allah take, ko da ace Mata huɗu yake da su idan Allah bai ƙaddari zai haihu ba babu yadda zai yi da ƙaddarar Allah. Hakan yasa ya fawwalawa Allah komai, kafin Allah ya basu ɗa namiji wanda suka sa masa 'Abdullahi' kuma suke kiransa da 'Ubaid.

Wato shi a rayuwa, duk abinda ka daɗe kana neman shi idan ka same shi kana mishi son so ne, so mai tsanani da kuma bashi wata irin kula ta musamman saboda muhimmancin da abun yake a rayuwarka. Ko dan wannan dalilin ya sanya suka ɗauki son duniya suka ɗaura wa ɗansu 'Ubaid!. Babu abinda yake so batare da ya same shi ba, Babu wani gata da kowani ɗa yake buƙata wanda Ubaid bai sameshi ba a wurin iyayensa. Sai dai duk irin tarin So da Ƙauna da suke masa, hakan bai sanya sunyi sake da Tarbiyyarsa da bashi ilimi ba, both na boko da na Islamic kuma Alhamdulillahi yana da ƙwazon karatu kuma yana maida hankali sosai.

Sai da ta gama duka aikin gida tayi abincin ta zuba a warmers ta ajiye su a ma'ajiyinsu sannan ta ɗauki wanda ta zuba domin IMRAN kasancewar yanzu ana sa ran farfaɗowarsa a kowani lokaci daga yanzu, wanda satin da ya wuce haka tayi ta jigilar tafiya da abinci tana dawowa da shi kafin Doctor yake sanar musu da cewa zai ɗau lokaci kafin ya farfaɗo.

Fita tayi tayi parking space ɗin madaidaicin gidan wanda bai wuce motoci uku zasu iya parking a gurin ba, ta sanya basket ɗin a boot sannan ta tayar ta cinna hancin motan kan titi cikin tuƙin natsuwa da ƙwarewa irin na ta.

Ko da ta shiga asibitin, sai da ta fara biyawa office ɗin Doctorn da kula da IMRAN yake hannunsa, amma ganin office ɗin a kulle ya sa ta wuce ɗakin da aka kwantar da shi. A hanyar ɗakin ne ta ci karo da nurses suna tura wata Mata a Stretcher, Matar tana gurnani cikin kukan azaban abinda ke damunta. Kusan Kowa yasan ta ada, ita ce Matar tsohon ministan man fetur wacce tayi shuhura  da kuma fankama da Alfaharin kuɗi. Babu abinda ta rasa na rayuwar jindaɗin duniya. Amma yanzu ta mallaki kuɗin amma tana ganin basu da amfani a gurinta tunda sun kasa sama ma ta lapiya. Shekara biyu kenan ana fama har ƙasashen waje aka ƙetara amma abin ya faskara. Wuce su tayi tana ma ta Addu'ar samun lapiya domin yanzu gaba ɗaya ta jeme ta sauya gwanin ban tausayi.

Duk da bata tsammanin tashinsa, murɗa hannun ƙofar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta ajiye basket ɗin abincin sannan ta zauna a kujerar da ke kusa da gadon da aka kwantar da shi wanda ta saba zama aduk lokacin da ta zo duba shi. Kallon fuskarshi tayi, ta ƙara haske tayi fayau. Duk irin halin da ya shiga na rayuwa, hakan bai hana bayyanar da kyawunsa ba. Wasu Mutane babban burinsu shine suga sun mallaki dukiya ko ta halin yaya ne, suna ganin ta wannan hanyar ne zasu samu farinciki, amma sai dai sunyi wa Rayuwa gurguwar fahimta. Duk a yanda ka tsinci kanka a Rayuwa kamata yayi ka godewa Allah, kasancewarka cikin lafiya ko baka da ko sisi ni'ima ce!, Akwai masu kuɗi da yawa da zasu iya sadaukar da dukiyarsu, sun yarda su talauce a yau domin samun lapiya matuƙar lapiyan zai samu, amma wasu ga kuɗin amma basu da amfani. Abar maganan lapiya, masu kuɗi nawa ne suke da kuɗin amma basa cikin walwala, farinciki da jindaɗin abinda suka mallaka?!. Lallai Godiya ta tabbata ga Allah shi kaɗai, da ace mutane suna yin godiya aduk abinda Allah ya mallaka musu, da sun samu sauƙin iftila'i da rikicin Rayuwa, da Allah sai ya musu Arziƙi ta inda basa tsammani!...

Hannunshi dake cikin nata ne wanda bata san ma lokacin da ta haɗe su ba taji ya motsa, hakan daya faru shine abinda ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula. Kallon hannunshi da ya motsan tayi, sai take ganin abun anya ba gizo bane kuwa. Tashi tayi da niyyar dawowa kan gadon amma sai taji ya riƙe ma ta hannun gam-gam tamkar wanda ake ƙoƙarin ƙwace mishi ita. Hakan ya sa ba tare da ta saki hannun ba ta miƙe ta zo ta zauna bakin gadon, taga ƙafafun shi suna motsawa. Ta kalli ƙafafun, sannan ta gangaro da kallon ta kan kyakkyawar fuskarsa, ta sanya hannun da baya sarƙe da nasa tana shafa lallausan gashin kansa wanda yafi kama da na Buzayen Nijar, ko kuma na indiyawa, musamman yanzu da zaman asibiti da kuma wankan da ake yiwa masu lalurar rashin lapiya irin na sa ya sa ainihin kalar fatarsa ta sake fitowa.

Idanunsa ne suka fara motsawa, kafin daga bisani suka buɗe gaba ɗaya!.
“Alhamdulillah!”. Shine abinda Mommy ta furta tana sake matsowa tana taɓa fuskarshi tana cewa “Yarona! Yarona! kana jina?!. Ya jikinka?. Ya kake ji ajikinka?”.
Shiru kake ji tamkar ba da shi take magana ba. Idanunsa na kallon ceiling ɗin ɗakin dai still. Sunyi more than about thirty minutes suna a haka kafin a hankali taga ya juyo da idanunsa ya kalleta. Wani irin ihu yayi tare da fashewa da kuka mai tsanani, yunƙurin tashi yayi zaune yana mai fusge cannulan da ke hannunsa wanda aka sanya masa drip, ya ziro da ƙafar shi ɗaya, azabtar da yaji ne ya sashi riƙe ƙafar yana sake fashewa da wani sabon kukan cikin ihu yana cewa “Dan Allah kayi haƙuri ka ƙyaleni!. Kar ka min dan Allah!😭💔. Dan Allah kayi haƙuri!, Dan girman Allah, dan girman Muhammadur Rasulullah!”. Yanda yake ta magiya cikin kukan da yake yi ya taɓa ma ta zuciya sosai, take taji wani irin tausayi da tsananin sonsa ya sake dirar ma ta lokaci guda. Hawaye na ambaliya akan fuskarta ta janyo shi ta rungume tana patting ɗin bayan shi. Ihun da yake yi ya ragu amma magiyan da kukan ne har a lokacin bai daina ba. Doctor ne ya shigo tare da nurse guda biyu, Sai da yayi da gaske kafin ya iya yiwa IMRAN Allurar bacci domin irin tsilla tsillan da yake ta yi.

Cikin wasu ƴan mintoci bacci ya kwashe shi. Bayan Doctorn yayi rubutu game da Lapiyar shi a wani littafi ne yace da Momyn, “Gaskiya ƙwaƙwalwarshi ta taɓu sosai, buguwan da yayi, da kuma ciwon da aka ji mai a zuciyar shi zai ɗau lokaci kafin ya warke. Zai iya loosing ɗin memory ɗinshi. I'm afraid to say idan abin yayi worse tafiya sai an koya ma sa. Amma ina fatan abin ya zo mana da sauƙi. Insha Allahu zai samu sauƙi ya cigaba da rayuwa kamar sauran mutane”.

Share Hawayenta Mommy tayi wanda har a halin yanzu ta kasa tsayar da su tana cewa “Allah ya bashi lapiya!”. Da Ameen Doctorn ya amsa.

Fita Doctor yayi bayan nurse ɗin da take monitoring ɗinsa ta canza masa kwanciyar da yayi, sannan ta fita. Dawowa tayi bakin gadon ta zauna wanda tun ɗazu da za'a yi masa Allura ta tashi, sannan ta sanya hannunsa cikin nata ta kwantar da kanta a gefen gadon hawayen ta na cigaba da zarya a kan kuncinta...

























Yayi muku daɗi kuna so ku ƙara ko, toh kuyi sharing anjima da yamma inyi sabon update😁...

MUJE ZUWA!...














#VOTE
#COMMENT
#SHARE

and Add to your library and OFFLINE books.

Alƙalamin real__ahmerd

IMRANWhere stories live. Discover now