0⃣0⃣3⃣

264 21 2
                                    


NOTE: Wannan labarin ƙirƙiraren labari ne. Suna, wurin aiki, kamanni, da gidaje da komai abubuwa ne waɗanda marubuci ya ƙirƙira. Idan wani abu yayi kamanceceniya acikin labarin da rayuwar wani, ina roƙon koma waye da yayi haƙuri.

Wannan shafin sadaukarwa ce zuwaga @AishaMaaruf1


Kuyi Haƙuri da yadda zaku dinga ganin rubutun!🙏. Sabon shiga ne dole sai an dinga yi ana min uzuri. Ina fatan zaku fahimceni!


SHAFI NA UKU

Sharara gudu yake yi akan titin Katsina zuwa Zaria fiye da yadda jirgi ke gudu akan titi kafin ta tashi sama. Kasancewar lokacin sanyi ne yasa duk inda ya wuce yake baɗa ƙura. Har yanzu Zuciyarsa cike take da tarin waswasi, kanshi na mishi wani irin sarawa, yayin da aikin da ƙwalƙwalwarsa ke yi sosai ya sanya yake jin zuciyarsa na zafi, tana tuna mishi munin laifin da yake yunƙurin aikatawa.

Shi kanshi yasan zuwa gurin bokan babban laifi ne wanda zai sa baza a karɓi ayyukansa ba har na tsawon kwanaki arba'in. Yarda da Boka kuma shirka ce babba domin jingina buƙatuwa ne ga wanin Allah Maɗaukakin Sarki. Sannan aiwatar da mummunan laifin Luwaɗi babban kaba'ira ce wanda zai janyo wa mutum fushin Allah, da rashin yardar mutane. Ah ah! ta ya mutane zasu san abinda na aikata bayan ba a jihata zan aikata ba?!. Kama haɓarsa yayi, Toh idan kuma wani ya ganni fa?!. Tsoro ne sosai ya kamashi musamman ganin yadda mulki ya dawo hannun farar hula yayin da ƴan jaridu suke yin tafiyayya ko ina a faɗin ƙasar domin ganin sun samo rahoto. Toh kuma.... Tunawa yayi da maganar Bokan da yake cewa

"......Akwai hatsari akan hanyar. Sai dai kai zaka ƙetareta komai rintsi. Idan ka jinkirta kuwa, kai da samun wannan kujera har Abada!"

Ƙara gudun Motar yayi har ya kaita ɗari da tamanin, domin yayi imani cewa tabbas zai samu biyan buƙatarsa. Tabbas zai zama ɗaya daga cikin masu ƙarfin iko da mulki haɗi da kuɗi a faɗin Nijeriya. Duk da cewa shi ɗin ba mai mugun son kuɗi bane, amma yana tara kuɗaɗe na ƙara ji da isa da izza!

Tunaninsa katsewa yayi sakamakon Slow down da yaji Motar nayi. Wani irin tashin hankali ya shiga mara misaltuwa, domin kuwa har yaci awa ɗaya da rabi cikin awa huɗu.

Fitowa yayi ya buɗe Bonet ɗin Motar yaga tayi zafi gashi ruwan ya kusa ƙarewa sai uban tiriri take yi. Dafe kanshi yayi yayinda idanunshi suka kaɗa suka yi jajir. Tunanin irin daɗewar da Motar tayi a ajiye yayi wanda sai yau ya sa aka cire tamfol ɗin da ta rufe Motar aka wanke Motar, tun bayan odar su da Gwanman ya bayar aka bawa Manyan Goverment official na daga kwamishnoni da makusanta gwamna. Gashi a daji ne balle yayi tunanin samun ruwa. Harɗe hannayensa yayi ya jingina da Motar kana ya tafi duniyar tunani....

*****************

SABON ZARIA

Kamar yadda Rahotanni suka yawaita a kudancin Nijeriya a wannan lokaci game da ta'addancin garkuwa da mutane, haka arewaci ke fama da ta'addancin fashi da makami. Duk da yawan rahotannin da ake yawan samu game da fashi da makamin, tsiraru daga ciki ake damƙewa a kaisu gidan maza, bayan an shiga kotu na wasu ƴan watanni zaka gansu a cikin gari suna shawaginsu.

Sai dai kuma an baza Sojoji ko ina da ina a faɗin jihohin tun bayan Security meeting da Gwamnoni suka yi da shugaban Ƙasa a Birnin Tarayya domin tabbatar da tsaro, Adalci da cikakken damukraɗiyar ƴancin Rayuwa da tsare dukiyoyin Al'umma. Check point check point akayi na sojoji a hanyoyin dazuka yayinda acikin gari kuwa aka yi ta bada numbar da mutane zasu kira su bada alert ga security idan sunga ana wani abinda ba dai dai ba domin tabbatar da tsaro.

Wani kango ne a wurin domin a lokacin tsirarun gidaje ne a faɗin unguwan wanda za a iya ƙirgasu. Babu abinda ke tashi a wurin sai warin giya, taba da wiwi dama dayawa daga cikin kayan maye wanda ni kaina ban sansu ba.

Ko da na shiga ciki, wani Matashi na hango wanda a ƙalla bazai zarce shekaru ashirin da biyar ba yana shan sigari, ga zuƙeƙiyar kwalbar giya a hannusa. Wasu na hango sunkai su bakwai abin mamaki manya waɗanda zasu zarce shekaru Talatin da ɗoriya a ƙalla.

Waya ce tayi ƙara a hannun ɗaya daga cikinsu, cirowa yayi daga Aljihu yana duba kan screen ɗin wayar amma buguwar da yayi bai hanashi gane wanda ke kiran ba. Tasowa yayi cikin sassarfa ya ƙarasa zuwa ga Matashinnan da yake gefe, miƙa msihi wayar yayi yana duƙar da kai ƙasa yana cewa cikin murya mai cike da maye
"2pac Yallaɓai ne fa ke kira"

Karɓa matashin da aka kira da 2Pac yayi ya danna wurin amsawa tare da kara wayar a kunnensa yana cewa
"Barka da Safiya Yallaɓai".
Ta ɗayan ɓangaren ne naji ance "A ina kuke a hanlin yanzu?!" cikin very serious and concentrative voice.

"Muna Sabon Zaria ne". ya faɗa cikin muryar da babu wasa fuskarsa a matuƙar murtuke babu alamun wasa acikinsa.

"Kamar yadda mukayi daku kwanakin baya, ya fito shi kaɗai ba tare da convoy ba. Ku gaggauta tare hanyar zariya kuyi fashi a wurin!"
Cikin ruɗewa yace "Yallaɓai akwai fa sojoji a hanyar!, ta ya ya kake tunanin hakan zai yiwu?!"

Dariya yayi cike da mugunta da izza irinta masu mulki yace "Shin kamanta cewa yau ake Passing out ɗin kuratan Sojoji?. Kuma bayan haka ma suna da security meeting da manyansu. Ku gaggauta fita ku fara aikin!, ina so ne ku kawo min shi a mace! Ku tabbatar ya mutu babu sauran rai acikin jikinsa. Ku salwantar da rayuka matuƙar kuka fuskanci hakan shine kaɗai zai iya sa musamu nasarar ɗaukan ranshi!..."
Tsayawa yayi kaɗan wanda yake magana a ɗaya ɓangaren yana gyara muryarsa, with all serousness ya cigaba da faɗin "...Karku bari ku wuce awa biyu a wurin!"

"An gama ranka shi daɗe!"

"Ina fatan akwai kayan aiki?"

"Eh Yallaɓai" ya faɗa cike da ladabi. Koƙarin datse kiran shi wanda ake kira Yallaɓai dake ɗaya ɓangaren yake ƙoƙarin yi yaji 2pac yace "Yallaɓai ya maganar Kuɗin?"

"Kunsan dai bana wasa. Kuyi aikin ni ma zan cika muku Alƙawari. Idan kun gama ku sameni jibi a Hotel ɗin da muka saba haɗuwa a jihar Lagos"

"Angama!"

Kiiit ya katse wayar yana mai miƙewa a take. Ƙarasa kurɓar giyar yayi sannan ya yi wurgi da kwalban. Fashewar kwalban shine abinda ya dawo da waɗancan dake gefe daga duniyar da suka lula. Ba tare da ya kallesu ba yace "Ku shirya yanzu zamu fita operation!". Ya faɗa cike da rashin tsoro.
Gaban kowa sai da ya faɗi amma tsananin tsoronsa da suke yi ya hana kowa yin magana acikinsu.






































KUNA SON GANIN SABON UPDATE CIKIN GAGGAWA?. KU ADDABENI DA COMMENT DA VOTE KUMA KUYI SHARING DOMIN NUNA SOYAYYARKU GA WANNAN LITTAFIN.








DAN ALLAH KUYI FOLLOWING ƊINA, DAƘIƘU BIYAR KACAL KAƊAI SUN WADATAR.










#VOTE
#COMMENT
#SHARE
#FOLLOW

IMRANWhere stories live. Discover now