0⃣0⃣9⃣

158 16 8
                                    

💐 IMRAN HAUSA NOVEL 💐
🍀An Untold Love and Politics Story
🍀

GAREKU MASOYANA!❤️
ALLAH YA BAR ƘAUNA!😍

KUSANI!, Wannan labarin dai ƙirƙirarren labari ne, komai na cikin labarin ƙirƙirarsa nayi, tha Story is fictitious!

FOLLOW ME PLEASE! 🙏, IT WON'T TAKE LESS THAN FIVE SECONDS...

SHAFI NA TARA

Da ƙyar Mommy ta samu ta tsaida hawayen da ke kwaranya a kan kyakkyawar fuskarta kuma ta samu natsuwa acikin zuciyarta da ambaton Allah da take ta yi.

Kallon agogo tayi taga ƙarfe ɗaya da rabi na rana. Sai a lokacin ta tuna da Ubaid da take zuwa ɗaukan shi daga school kullum idan sun tashi, ya ƙara abinci idan sun dawo gida sannan ta sashi yayi Sallah sannan Jummala mai aikinta wanda sai ƙarfe tara ko goma na safe take zuwa aiki gidan ta kaishi islamiyya kafin ƙarfe uku, domin ƙarfe uku ake fara karatu.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗauki waya domin kiran Daddy domin sometimes idan ba aiki sosai yakan dawo da rana domin cin abincin rana, idan zai dawo yau ne ya biya ya ɗauko Ubaid domin a halin yanzu ji take baza ta bar Yaro shi kaɗai ba sai ma tunanin da take na kiran Mahaifiyar Jummala ta fara sanar da ita cewa Jummalan zata kwana da Yaro a asibiti, sannan ta kira Jummalan, idan yaso gobe idan Allah ya kaimu da safe sai ta koma gida idan tana da buƙatar hakan.

Shawaran da ta yanke kenan sannan ta miƙe ta shiga bayi domin yin alwala ganin lokacin Sallahn Azahar ta yi.

★★★★★★★★★★★★★★★★

Wani katafaren ƙayataccen falo ne wanda ya ji royal cushions White colours. Komai acikin falon an ajiye shi a ma'ajinsa kuma komai na cikin falon fari ne tas, haka ko ina ƙal ƙal babu alamun datti, ga daɗɗaɗan ƙamshin air freshener da ya gaurayu da sanyin Acn yake bada wani irin ƙamshi mai daɗi cikin wani irin sassanyar yanayi mai birgewa. Falon ya haɗu iya haɗuwar da kai tsaye za'a iya kiransa da Aljannahn Duniya!.

Zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun falon sanye da farar jallabiya wanda hakan ya ƙara fito da asalin kyawunsa na bafulatani, gefe ɗaya kuwa tamkar wani balarabe duba da irin yadda sajen fuskarsa ya kwanta luf luf akan fuskar, ga gashin kansa da ya sha gyara tamkar wani saurayin da bai wuce Twenty five years ba, alhalin kuwa he's now heading to his 40's. Kawai tsabar hutun da yake samu ne duk dama a kwanakin nan da Gwamna yayi tafiya aiki na galabaitar da shi, wai a hakan ma dan wasu abubuwa da Deputy Governor suke yi tare, duk da cewa mafi yawa abubuwan da yake yi Deputy yakamata yayi amma kasancewar yafi yarda da shi kuma shi bai wani daɗe a siyasa ya san sirrin Gwamnati sosai ba ya sa ya damƙa ragamar kusan komai a hannunsa. Yau kwana biyar kenan da tafiyar Gwamna wanda sati guda dama zai yi, gama Breakfast ɗinshi kenan yanzu Eleven o'clock wanda dama sai wuraren Ten ne yayi tare da Matarshi ya koma parlour ya zauna yana ji kamar ba zai je state office ɗin ba yau. Karanta Newspaper yake yi silently ɗaya daga cikin securities ɗin ya shigo, ya gaida shi "Ina kwana Sir!"

Ba tare da ya amsa ba ya ɗago ya dube shi yana jiran mai zai ce wanda hakan ya sashi shan jinin jikinshi ya ce "Dr. Musa ne ya zo ya na so ya ganka Sir!".

He just want to be alone for now amma kuma fa sunyi kwana biyu ba su haɗu ba, dagangan ya kashe wayoyinshi saboda baya son abinda zai ɗaga mai hankali kuma ya san Dr. Musa yayi ta kira bai samu ba domin inba abu mai muhimmanci ya taso ba basu wani cika haɗuwa ba sai dai su yi magana ta waya, duk yadda akayi akwai wani labari ne da ɗumi-ɗuminsa yake so ya labarta mishi.

"Ku barshi ya shigo!" ya faɗa a taƙaice cikin umurni.

Shigowa yayi bayan yayi sallama sun gaisa sun ɗan jima cikin shiru ne Dr. Musa yayi breaking silent ɗin...

IMRANWhere stories live. Discover now