0⃣0⃣5⃣

177 12 0
                                    

DAN ALLAH KUYI FOLLOWING ƊINA, DAƘIƘU BIYAR KAƊAI SUN WADATAR...







💐IMRAN HAUSA NOVEL 💐

🍀An untold Love and Political Story 🍀



🌸HANYA TA FARKO DA KAKE FARA GIRBAN SAƁONKA SHINE ƘASƘANCI!🌸




SHAFI NA BIYAR

Nufoshi yayi gadan gadan yayin da IMRAN cikin tsoro da firgicin da ya shige shi ya fara ja da baya yana mai dafe bango cike da rashin ƙwarin jiki.

A halin yanzu kam ɓangare mafi rinjaye acikin zuciyarsa tafi bashi shawaran ya janye ƙudirinsa, kada ya aikata laifin da Allah zai yi fushi dashi, ya sa zunuban mummunan aikin su katangeshi daga samun abinda yake nema amma sai dai kash!, ya kasa hana gaɓoɓin jikinsa aikatawa.

Cikin rashin sa'a IMRAN yayi tuntuɓe da dutse ya faɗi ƙasa. Ƙarasowa yayi da sauri ya juya IMRAN daga riginginen da yake ya koma ruf da ciki. Ciki tsantsan rashin imani ya soma aikata zunubi mafi muni da Allah baya So. Wani irin razanannen ƙara IMRAN ya sake wanda hakan ya sa shi toshe mishi baki, cikin mintinan da basu fi goma ba IMRAN ya fita daga cikin hayyacinsa, numfashi na barazanar ɗauke masa saboda toshe masa baki da yayi.

Sai bayan mintina kaman ashirin ne Mutumin ya fara dawowa cikin hayyacinsa. Da sauri ya zame daga kan IMRAN ɗin da yake kwance tamkar babu rai acikin jikinsa, ga jini na fitowa daga jikinsa yana malala yana jiƙashi, babu wani sassa na jikinshi da yake nuna akwai rai ajikinshi hatta ƙirjinshi. Da sauri ya fice ya shige Mota yayi wa Motar key tare da cinnata kan titi da gudun tsira, Zuciyarsa na dukan uku-uku.

Ko tafiyar cikakken minti goma bai yi ba Motar Sojoji ta sha gabansa a haukace. Da sauri ya taka birki tare da ƙara sawa Motar lock. Bayan minti biyu ya ji an ƙwanƙwasa masa glass, ko da ya juyo bai yi mamaki ba, ɗan guntun murmushi yayi tare da sauke glass ɗin Motar a hankali. Idanunshi na haɗuwa da na wanda yake gani a gaban shi yaji wani irin tsoro da firgici sun dirar mishi lokaci guda.

Mutumin dake tsaye cikin Kaki na Sojoji cikin murɗaɗdiyar surar dake nuna jarumta, cikar haiba gami da kwarjini ya dubeshi cikin yanayi na faɗaɗa murmushi akan fuskarsa yace da shi

"Honourable Zahraddeen Farar aniyar!"

"Leutenant Muhammad Bello Bamalli!"
Hon. Zahraddeen ya amsa mishi cikin yanayi na ruɗewa. Bindiga Pistol Lt. Muhammad Bello ya zaro daga jikinsa tare da nunawa Hon. Zahraddeen cikin dakewa yace dashi
"You are under arrest!".
Wani irin Zabura Hon. Zahraddeen yayi, Zuciyarsa na tsananta bugawa. Zai yi motsi kenan ya ji ƙarar bindiga wanda hakan ya ƙara rikitashi. Cikin wata iriyar kausasshiyar murya Lt. Muhammad Bello ya ce da shi "Kana motsawa zan fasa kanka!".




















Inai mai bawa ɗaukacin Masoya littafin IMRAN haƙuri bisa rashin ji na da bakuyi ba kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon abubuwa na makaranta da suka sha min kai. Zan dinga posting mai tsayi kuma akai akai. Ku cigaba da kasancewa tare da ni....

















#VOTE
#COMMENT
#SHARE
#FOLLOW






IG:@real__ahmerd

IMRANWhere stories live. Discover now