0⃣0⃣6⃣

181 13 3
                                    

DAN ALLAH KUYI FOLLOWING ƊINA, DAƘIƘU BIYAR KAƊAI SUN WADATAR...




💐IMRAN HAUSA NOVEL 💐

🍀An untold Love and Political Story 🍀

This chapter is dedicated to my lovely caring Mom❤️. Allah ya dawo min dake lapiya...

SHAFI NA SHIDA

Kasancewarsa Mutum ne mai dakakken zuciya, ba ƙaramin abu  ba ne yake bashi tsoro, ya sa yayi saurin daidaita natsuwarsa. Kallon shi yayi hannunshi na kan steering ya karkaɗa kansa tare da sakin wata dariya cikin dakewa yace da shi “Kai wani irin Jahili ne?. Wacce dokar ce ta bawa wani soja damar yin arrest, uhmm?. ko an gaya ma ka nima jahilin ne bansan komai ba kamar ka?. Ka gaggauta sake min hanya in wuce idan ba so kake ka rasa aikinka ba a yau yau ɗin nan!”. Ya ƙarasa faɗa yana mai tada motar. Ƙoƙarin buɗe ƙofar fannin Driver Lt. Muhammad Bello yayi wanda cikin sa'a ta buɗu, “I'm not really arresting you, akwai investigations ne da ake so ayi a kanka wanda idan hakan ya tabbata babu shakka zaka shiga hannu!”.

Wani irin duka zuciyarsa tayi, a iya tunaninsa dai ba wani abinda yayi, amma kuma lokacin da ya tuno lamarin Yaronnan da ko sunanshi bai sani ba sai hankalinsa ya tashi. Amma kuma da ya tuna cewa babu wata evidence sai ya ɗan ji hankalinsa ya kwanta. “Zan biku muje a Motata, ka sa wani ko ɗaya daga cikinku ya shigo mu tafi tare. Amma fa kasani, akwai barazanar rasa aikinka matukar a binciken aka gano babu laifina a ciki!”.
Duk da irin jarumtar Lt. Muhammad Bello da gwagwarmaya da kuma tashin hankalin da ya fuskanta a baya waɗanda suka fi wannan ma, amma kuma sai yaji na wannan abu ne na daban domin a duk mutane masu taurin kai da ya gamu da su a rayuwarsa, babu wanda ya taɓa mai barazanar rasa aikinsa!. Ya so yayi gardama akan sai dai wani ya shiga motar ya kai masa ita, amma kuma a wannan gaɓar gwara ya lallaɓa shi don ya san shi Mutum ne mai kafiya tun suna College, ba kasafai ya fiye sauka akan maganarsa ta farko ba, balle kuma yanzu da yake matakin Shugaban Ma'aikata na Jaha!

Ba tare da wani ɓata lokaci ba yayi appointing Sojoji biyu da zasu shiga motar Honourable, sannan suka sa shi a gaba suna binsa a baya kowa da saƙe saƙen da yake yi a ransa.
Babban Ofishin Security investigations suka isa inda akayi directing ɗinsa wani dark room da babu komai aciki sai kujeru biyu suna fuskantar juna sai kuma wani babban tebur a tsakaninsu, babu wani waɗataccen haske face wani ƙwan lantarki wanda yake launin ja a setin inda kujerun suke. Sojan da ya shigo da shi ne ya ja masa kujera ya zauna, yayin da ya kasa tuna dai dai da dalili guda ɗaya rak da ya kaishi ga shiga  wannan gurin. Ɗora hannayensa yayi akan teburin dake gabansa yana mai ƙurawa kujerar da ke fuskantar sa ido, har tsawon mintina Uku yana a haka yaji an buɗe ƙofar an shigo tare da sallama. Cikin natsuwar da ba ta kai har zuci ba ya amsa tare da juyowa dan ganin mai shigowar, hanjin cikin sa sai da suka kaɗa, wani irin firgici ne ya ziyarce shi lokaci guda, bugun zuciyarsa ne ya tsananta, amma kuma hakan bai bayyana ƙarara a fuskarsa ba sai mai tsananin lura da sā ido ne ko kuma wanda aikinsa ya danganci hakan ne zai iya fahimta. Ba kowa bane face Inspector General of Police Haruna Abdullahi Shinkafi shi da kansa!.

Maida kansa yayi yana kallon teburin dai dai lokacin da Inspector ya ƙaraso ya zauna a kujerar ya zama suna fuskantar juna. “Barka da wannan lokaci” inspector ya faɗa yana mai ƙare mishi kallo. Aro Jarumta Honourable yayi tare da sake gyara zaman hannunsa dake kan teburin yana cewa “Yauwa barka”.
“Sunana Inspector General Haruna Abdullahi Shinkafi. Nasan bazaka rasa jin labarina ba”. inspector ya faɗa yana mai ƙare mishi kallo. Girgiza kai yayi kawai alamun eh wanda ya sa Inspector ci gaba da magana kamar haka “Dafan kaine Honourable Zahraddeen” tsakankanin satan numfashi ya amsa da eh.

“Ban taba tunanin cewa a well behaved and discipline government official kamar kai za'a sameka kana deals irin wannan ba. Kadubi duk yadda Gwamna ke sonka, ka dubi yadda ya ke saka kana wakiltanshi a wurare wanda wannan aikin mataimakin shi ne. Ka dubi irin Alfarma da kake samu daga Federal ana baka contract. Ka dubi irin Albashi da kake ɗauka ya isa ya ishe ka rayuwa. Me yasa kake so ka ɓata Career ka ta siyasa?. Ace wai yau an samu da hannunka dumu dumu acikin ayyukan ta'addanci?. A haka Shehu Galadima yake so ka zama Gwamna nan gaba?..”.

IMRANWhere stories live. Discover now