0⃣0⃣4⃣

250 21 9
                                    


DAN ALLAH KUYI FOLLOWING ƊINA, DAƘIƘU BIYAR KACAL SUN WADATAR...

Wannan shafin sadaukarwa ce zuwaga miss_untichlobanty

"A DUK LOKACIN DA ƊAYANMU ZAI AIKATA WANI AIKI NA SAƁO, KADA YA ƘAURACEWA MUTANE SABODA KAR SU GANSHI, DOMIN DUK NISAN GANI IRIN NA ƊAN ADAM AKWAI ABINDA IDANUNSHI NA KAI AMMA BAYA IYA GANINSHI. YAYI TUNANIN WANDA ZAI SAƁAWA YANA GANINSA, KUMA GANINSA YA WADACI KO INA A FAƊIN HALITTUNSA, BABU ABINDA KE ƁOYEWA GANINSA, BAYA ANAGAJE BALAI BACCI. MU SANI, KUNYA DA TSORON UBANGIJI TARE SUKE TAFIYA DA IMANI. IDAN ƊAYA YA SAMU NAƘASU, BABU SHAKKA IMANI YAYI RAUNI."

SHAFI NA HUƊU

Fitowa naga sunyi daga cikin kangon su Takwas kowannensu sanye da manyan kaya har da hula, uku daga cikin su hannunsu ɗauke da trolley irin na sa kaya manya suna ja har suka kawo bakin titi. Kyawawan mintuna goma basuyi ba wata mota ƙirar Golf ta haya ta zo gilmawa babu kowa acikinta. Tsaidashi sukayi tare da mishi bayanin inda zai kaisu, mamaki abun ya bashi domin sanin cewa wurin da suka ambata mai zasu sauka, daji ne babu gida ko guda ɗaya a wurin.

Ko mintuna ashirin basu kai ba suka isa wurin, suna sauka 2pac ya sanya hannunsa acikin Aljihu ya fito da kuɗaɗe masu yawa, batare da ya ƙirga ba ya miƙawa Drivern. Ƙin karɓa yayi sai ma sokoko da yayi baki hangame yana kallonshi. Haushi abun ya ba 2pac wanda hakan ne ya sanya shi watsa mishi kuɗin ya juya ya nufi inda sauran suke tsaye a bakin titi. Wani irin tsoro ne ya ɗarsu a zuciyar Drivern ganin irin irritating look ɗin da 2pac ya mishi yasa ya sa giya ya figi motar da gudu ya bar wajen.

Suna ganin tafiyar drivern golf ɗin suka shiga cikin dajin. Tafiya suke yi da sauri har sai da suka isa can ciki inda dukansu suka tsaya a ƙarƙashin wata bishiya doguwa mai yawan ganyanyaki da ta bawa wurin wani irin inuwa mai ni'ima. Ajiye trolleys ɗin sukayi suka buɗe su. Wani irin tsoro ne ya daki zuciyata sakamakon yanda idanuna suka ci karo da trolleys biyu cikin uku ɗauke suke da bindigu ƙirar AK 47 da pistols da kuma wasu ƙananan wuƙaƙe. Ɗayan trolleyn kuwa ɗauke yake da wandunan khakin Sojoji da kuma farar riga sai rawaninnika wanda suka kasance ja da baƙi aciki.

Shiryawa sukayi kowanne daga cikinsu sanye da Wandon Khakin sojoji da kuma farar riga top a saman ta, fuskarsu a rufe take babu abinda ake gani sai idanunsu yayin da kowannensu ke riƙe da AK 47 sai kuma pistol da ƴar ƙaramar wuƙa da ke maƙale a kugun kowannensu.

Sake fitowa sukayi bakin titi kowannensu ɗauke da wani irin babban ice suka tare hanyar. Ko minti biyar basuyi da tsayuwa ba wata bus ta hudo kai asukwane cikin matsanaicin gudu a akan titi. Ƙoƙarin kaucewa itacen Drivern yayi amma ɗaya daga cikin ƴan fashin ya fasa tayoyin gaban motar da harsashin bindigarsa. Take Drivern yayi nasarar taka burki. Lamarin da yasa mutanen da ke cikin bus ɗin suka shiga tsananin firgici, kowannensu da abunda bakinsa ke furtawa na neman tsarin Allah daga sharri.

Drivern ne ya soma fitowa yana cewa "Lapiya naga an tare hanya kuma nazo wucewa kun fasa min taya?!" Yayi tambayar cikin aro dukkan wata jarumtar da ta rage masa domin shi duk ɗaukarsa sojoji ne duk da cewa yasan anyi fashi akan hanyar watannin da suka gabata, amma wani iko na Ubangiji bai taɓa haɗuwa da ɗaya daga cikin ƴan fashin ba sai dai ya ji labari....

Katse mishi tunani 2pac yayi yana mai cewa "Ka cewa kowa ya fito!"

Babu Musu ya ce su fito domin sai yanzu ya fuskanci su waye su. Fitowa suka yi ɗaya bayan ɗaya kowa da abinda yake saƙawa a ransa, babu abinda suke yi a zuciyarsu sai ambaton Allah. Cirko cirko sukayi a gefe guda, Mata uku ne sai maza takwas har da Drivern, kallonsu kawai ya isa yasa kasan irin tarin tashin hankali da kowannensu ya shiga.

Kowa da kowa ya fito da abinda ya mallaka, ya zo ya ajiye anan a gaba na ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda ya ɓoye wani abu, babu shakka zan fasa kansa da wannan bindigar". Ya ƙarasa faɗar hakan yana mai harba bindigar sama.

IMRANWhere stories live. Discover now