0⃣0⃣7⃣

200 19 4
                                    

💐 IMRAN HAUSA NOVEL 💐
🍀An Untold Love and Politics Story 🍀

Har wa yau dai wannan shafin sadaukarwa ce gareki yake ma'abociyar karamci, domin kece a kullum ke ƙarfafa min gwiwa game da rubutu na. Nagode sosai da sosai AishaMaaruf1!

_Godiya ta musamman dai zuwa ga Masoya wannan littafin da suke ƙarfafa min gwiwa domin cigaba da rubuta wannan littafin, nayi muku Alƙawari baza kuyi nadamar karanta shi. Sannan ina mai baku haƙurin rashin update akai-akai amma yanzu na dawo fully Insha Allah!. Nagode!🙏._

SHAFI NA BAKWAI

Zaune yake a katafaren ƙayataccen office ɗin wanda yaji well furnished Turkish furnitures masu matuƙar tsada, ga sassanyan classic Airfreshner dake tashi haɗe da AC. Kai da gani kasan wannan ko a shahararrun ƴan kasuwa ne ba ƙaramin kuɗi mutum yake dashi da zai yi affording ɗin irinsu ba. Wani ɗan ƙaramin triangle blue board ne ƙarami mai majingini ajiye akan table ɗin mai ɗauke da fararen rubutun turanci masu sheƙi, “Dr. Shehu Umar Galadima” shine sunan da ke rubuce ɓoro ɓoro sai kuma a ƙasan rubutun sunan aka rubuta “Executive Governor of Katsina State”. Dudduba neat files ɗin da ke gabanshi yakeyi gaba ɗaya yana ƙoƙarin mai da hankalinshi akai amma abin ya ci tura, tunanin yanda abubuwa suke tafiya yake, gashi Zahraddeen yana so kawo mai tashin hankali acikin shirin da ya daɗe yana aiwatarwa. So yake ko ya sauka akan mulki ya zamto yana da faɗa aji a jihar. So yake sai abinda yake so shi za'ayi. So yake ko da ace bai sake samun wani muƙami ba ya zamto yana riƙe da akalar da zai iya juya Al'amuran jihar. Ya riga ya gama tsara komai ta yadda ba sai Zahraddeen ya kai kanshi irin waɗannan abubuwan ba, ya riga ya gama shirinsa tsaf na sai waɗanda yake  so ne kaɗai zasu iya hawa mulkin. Buɗe ƙofar office ɗin da akayi shine abinda ya dakatar da shi daga tunanin da yake yi. Hon. Zahraddeen ne ya shigo bakinshi ɗauke da sallama. Amsawa yayi ba tare da ya ɗago ba yana cigaba da duba tulin files ɗin dake gabansa. Zama Hon. Zahraddeen yayi a kujera yana tauna maganganun da zai faɗa mishi kafin ya fitar da su.
“Nayi maka komai Zahraddeeni, Meyasa kake so ka ɓata Career mu?”. Tambayar da yayi masa kenan cikin sanyin murya ba tare da ya ɗago ba.
“A gafarce ni ranka shi daɗe, banyi tunanin abin zai kaiga haka ba”. Ya bashi amsa kanshi a ƙasa hannayense a haɗe gaba ɗaya jikinshi ya gama yin sanyi.

Ɗagowa yayi ya sanya hannayensa biyu akan tebur ɗin yana mai tokare haɓarsa da su ya kalleshi “Kasan me kayi kuwa?!. Babban abinda ke damuna da kai shine komai zaka yi ba ka shawara da kowa, amma ni duk da tazaran shekaru dake tsakanina da kai, da kai nake shawara kuma mafi akasari ana cimma nasara. Ban san meyasa baza kayi amfani da ƙwaƙwalwarka kayi tunani, kayi nazari akan abinda zai biyo baya ba. Abokin kuka, ai shi ake gayawa mutuwa. Ban san meyasa bazaka ɗaukeni abokin shawara ka faɗamin damuwarka ba. Duk jami'an tsaron da muke da su amma ka fita ba tare da tsaro ba, kaja ƙananan Mutane sun tsare ka suna maka tambayoyi, cikinka ya ɗori ruwa ka kasa yin wata kataɓus har da ma barazana!, Mtsswww!...”. Ya ja tsaki yana mai sauke hannayensa ya juya a kujerar yana mai ƙara fuskantar sa.

Gaba ɗaya jikinsa ya gama yin sanyi. Gumi sosai yake haɗawa domin ba ƙaramin shakka da tsoron Gwamna yake yi ba, duk da ACn da aka ƙure ya sanyaya office ɗin.
“Kayi haƙuri Your Excellency”

“Me kaje yi kai kaɗai ba tare da tsaro ba?”. Gwamna ya tambaye shi fuskar shi a haɗe. Ɗagowa yayi ya kalleshi ya tabbatar da babu alamun wasa a fuskar shi, ya sauke kan shi ƙasa yana tunanin ƙaryar da zai haɗa mai, gaba ɗaya a duburburce ya fara cewa,
“emm...em....Dama...”

“Dakata! Kaga nayi kama da wanda zaka yiwa ƙarya?!”. Gwamna ya dakatar da shi cikin tsawa.

Shiru yayi hannunshi da ya haɗe guri guda suka soma gumi.

IMRANWhere stories live. Discover now