0⃣0⃣2⃣

347 25 8
                                    

NOTE: Wannan labarin ƙirƙiraren labari ne. Suna, wurin aiki, kamanni, da gidaje da komai abubuwa ne waɗanda marubuci ya ƙirƙira. Idan wani abu yayi kamanceceniya acikin labarin da rayuwar wani, ina roƙon koma waye da yayi haƙuri.



Wannan shafin sadaukarwa ce zuwaga nimcyluv








SHAFI NA BIYU

Wani irin bugu zuciyarsa keyi yana jin wani tashin hankali na kusanto shi. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa shiga irin wannan tashin hankalin ba. Tabbas yana matuƙar jinjinawa iyayenshi da irin ƙoƙarin da suka yi wurin bashi ilimin addini daidai gwargwado, ga kuma ilimin boko da ya samu, wanda sanadiyyar hakan ne yakai matsayinda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa mafarki ba.

Tunawa yake yi da ƙissar Annabi LUƊ da kuma irin Azabar da Allah ya musu da suka kauce da ga hanyar Allah wurin aikata mafi munin laifin da Babu irin wa'azi da tunatarwar da Annabi LUƊ din bai musu ba amma son zuciya da saɓawa maganar Manzon Allah ya kaisu ga aikatawa wanda hakan ya ja musu fushin Allah aka kifar da su. A Tahirin Al Qur'ani gaba ɗaya banda na FIR'AUNA, babu wata ƙissar da take tsoratar dashi da sashi ganin girman Allah irin ƙissar Mutanen Annabi LUƊ. Sai dai kuma yanzu a shirye yake da yayi koma mene ne indai har zai samu muƙamin siyasar da yake nema, domin babu abinda yake so a rayuwarsa kaman yaga yana mulki, yana jujjuya mutane a ƙarƙashinsa, yana faɗa ana ji, yana da ikon da babu mahalukin da ya isa ya nuna masa yatsa!

Boka yanzu babu wani mafita sai wannan?" ya faɗa a matuƙar sanyaye muryarsa na rawa.

"Wannan ita ce kaɗai mafita!. Kayi maza kaje ka aiwatar, domin yin hakan shine mataki na farko da zai tabbatar maka da samun kujerar ka!"
Bokan ya faɗa a zafafe yana girgiza sandar da ke hannunsa yayinda sautin shawo da mujiya da yanda iska ke kaɗa ganyanyakin bishiyoyin da ke wurin ke bada wani sauti na ban tsoro acikin kunnensa.

"Ka tashi ka tafi!, lokacinka ya riga ya fara!".

Tashi yayi ya fita ƙafafunsa na kakkarwa suna lumewa a kowani taku da zai yi saboda laushin ƙasar.

Fitowa yake yi daga bukkar Bokan yayinda Wata Zuciyar ke gargaɗinsa akan girman laifin da yake shirin aikatawa.

'Babu wani matsayi da zaka kai a rayuwa ba tare da yana rubuce acikin littafinka tun fil azal cewa zaka kai ba. Babu wani Arziƙi da zaka samu ba tare da yana rubuce a cikin littafinka cewa zaka samu ba. Babu wata Ɗaukakar da zaka samu ba tare da yana rubuce cewa zaka ɗaukaka ba. Karka yi shirka kar kayi Hassada. Karka yi duk abinda zaka ɗorawa kanka Alhanki akan abinda a duniya zaka sameshi kuma zaka barshi. Kadinga tunanin lahirarka. Ka dunga tunanin gobenka. Ka daina kallon ƙanƙantar laifi, ka kalli girman wanda zaka saɓawa.....'

Saurin kawar da Nasihar da Mahaifin nasa yayi masa kenan tun samun matsayin Chief of Staff da Gomnan Jahar ya bashi shekaru uku da suka wuce. Gashi yanzu zaɓen 2003 na ƙaratowa, yana neman takarar ɗan Majalisar wakilai a gundumar su, gashi abokin hamayyarsa na jim'iyyar adawarsa ya fishi yawan mutane da kuma cancanta, musamman yadda mutanen gundumar zukaga irin rawar da Chairman ɗin ya taka a matsayinsa na Chairman na gundumar a ƴan shekarun da suka gabata.

Buɗe Sabuwar Motarsa yayi ƙirar Audi A4 2003 model ya shiga ya kulle ƙofar. Wani irin furzar da iska yayi yana murza key ɗin Motar ya fara tuƙawa cikin ƙwarewa yana fita daga ƙungurmin dajin. Yana hawa kan titi ya figeta da wani irin Mahaukacin Speed yayin da yake jin kansa na ƙoƙarin tarwatsewa saboda tunanin da yake addabarsa....

Shin zai samu nasarar aiwatar da ƙudirinshi kuwa?.
Shin wanene shi?





DAN ALLAH KUYI FOLLOWING ƊINA, DAƘIƘU BIYU KAWAI SUN WADATAR.


































#VOTE
#COMMENT
#SHARE
#FOLLOW

IMRANWhere stories live. Discover now