Chapter One

365 35 2
                                    

 
    Assalamu Alaikum beautiful people. I'm so pleased to announce to you all that Hayateey is finally here and kamar yadda na sanar daku it is going to be a paid story amma the first 10 pages are going to be free.

Regular fee is N500 while VIP is N2000.
For regular zan na posting once daily, kwana biyar a sati banda weekends. while for VIP zasu dinga samun pages 2 everyday amma a Weekends instead of 2 pages post sau d'aya ne a rana.

Kindly pay into this account number
2275076407
Maryam Hussaini Anas
UBA

And send evidence of payment to this number 09046684501

MAITAMA PHASE 1 ABUJA, NIGERIA.
10:21pm

Ruwan sama akeyi mey mugun k'arfi wanda bayan k'aran sauk'an ruwan nan ba abinda mutum ke iya ji. Yarinya ce 'yar k'arama kwance akan king sized bed da aka kafa a tsakiyan kaftareren d'akin. Kanta ta duk'unk'une acikin bargon da take lullub'e dashi. Kallo d'aya mutum ze mata yasan a razane take. Idonta ta matse gam yayinda tsoron nata yake sake tsananta. Wani mugun tsawa aka sakar wanda hakan ya sanyata sakin k'ara.

"Abba!!" Ta k'urma ihu a firgice yayinda ta mik'e zaune tana hak'i. Kai ta had'e da guiwa tana sumbatu. Kana aka saki wani tsawan wanda yama fi na d'azu firgitarwa. Ba shiri ta sauk'o daga kan gadon ta shige k'ark'ashin gadonta had'e da ta toshe kunnuwanta. Hawaye ta shiga zubarwa ba shiri. Ruwan saman aka cigaba da kwararowa mey mugun k'arfi wanda yake sake firgita ta. Ba a dad'e ba sega shigowan k'ara daga bakin k'ofa, acikin seconds aka murd'a handle d'in aka bud'e k'ofan. Switch d'in d'akin aka kunna, wata mata ce ta bayyana daga bayan k'ofan. "Farrah!" Matar ta kira sunan da yayi kama da na yarinyar. Cigiyar d'akin ta shiga yi tana neman Farrah. Kaman wacce tasan inda yarinyar ke b'oye, ta lek'a k'ark'ashin gadon inda ta sameta duk ta rud'e. Janyota tayi da k'yar ta mayar da ita kan gadon. Bargon ta hura ta rufe su tare yayinda ta kwantar da Farrah da har yanzu bata fasa jin tsoro ba a jikinta. Gagam Farrah ta matse matar. Bayanta matar ta shiga bugawa a hankali.

"Nanny Abba" 'yar k'aramin muryanta ya fad'a cike da tsoro.
"Shhh it's going to be alright" Nanny ta tabbatar mata.
"Nanny kice mishi ya dawo dan Allah kar ya tafi yabar Abba."
"It's okay Farrah everything is going to be alright" Bayanta Nanny ta cigaba da bugawa har izuwa lokacin da ruwan ya d'an lafa. Bacci mey d'ankaren nauyi ne ya saci Farrah. Itama Nanny daga nan bacci yayi awon gaba da ita. Ba Nanny ce ta tashi ba se wuraren 6:30AM na safe. Nan ma sanadiyyan k'onk'osa k'ofan da akeyi ne ta farka. Carefully ta janye Farrah daga jikinta sannan ta mik'e ta bud'e k'ofan.

  "Just as expected" saurayin dake faman buga k'ofan tun d'azu yace. Magana d'aya yayi amma hakan be hana fito da tattausan muryanshi ba. Murya ne wanda ko akan layi kaji shi seka juya ka duba daga inda ya fito, ba don komai ba se don irin k'ara mai dadi'in da yake dashi.
"Ahmad-"
"Don't tell me ko Sallah bakiyi ba kina renon wanchan abun" ya nuna Farrah da ido had'e da katse Nanny. Dan k'arshen walak'anci mutum yake kira da abu.

"Ahmad for goodness sake" Nanny da tokarin da yakeyi wa Farrah ya isheta ta furta "In kana yiwa Allah kayi tafiyanka, yarinyar nan bata samu cikakken bacci ba jiya ba."

"Ke! Tashi!" Ya ce da Farrah cike da tsiwa tamkar be ji abinda Nanny tace ba just now.
  Nan take Farrah dake bacci ta farka sanadin tsawan da yayi. Idonta be sauk'a a ko ina ba se kan Ahmad dake galla mata harara. Wani na iya cewa ta kashe mishi iyaye ne dan wannan tsana se haka. Kaman wanda taga mala'ikan mutuwa ta juya mai baya da wuri had'e da kulle idonta gagam cike da tsoro. Wani tsuka Ahmad yaja "Har yaushe zakina babysitting wanchan abun?" Ya jefa wa Nanny tambayar had'e da dawo da kallonsa a gareta.

"Ahmad Babana meyasa kake hakane fisabilillah? She's just a child, kuma so kake ka ce min ka manta da halin da ta ke ciki ne? Ka fa san kalan nightmares da suke damunta idan ana ruwa cikin dare amma ka dunga acting kaman baka sani ba kata surutu idan ka ganni a kanta, bana jin dad'in hakan. Yarinyar nan fa k'anwarka ce."

HayateeyWhere stories live. Discover now