Chapter Two

155 20 1
                                    


"How did you get a hold of my number?" Ya tambayi nurse d'in wanda seda ta had'iye miyau saboda yadda Ahmad ke magana da tsiwa ta wayan. "Well- well your sister read it out to me."
   "For the last time she's not my sister!" ya daka mata tsawa seda ta nisantar da wayan daga jin ta. "Don't you dare call me again regarding any issue about her" yana kaiwa ga nan ya katse wayan. Shiru ne ya d'au wajen. Nurse d'in mamaki yama hanata magana.
  "But did you just say he is her brother?" Ta tambayi Lailah fuskanta d'auke da mamaki.
  "I suppose!" Lailah ta amsa itama mamakin take, bata d'au rashin imanin Ahmad da tsanar da yake yiwa Farrah har ya kai ga haka ba. Wato in ma mutuwa zatayi ta mutu he doesn't give a damn.

  "What to do now?" Nurse d'in ta kewayo da tambayanta ga Farrah da already dama tasan hakan na faruwa tunda suka sake suka kirashi. Ita yanzu bama wannan ba tunanin turanchin da zataje ta mishi a gida yau take dan if care is not taken seya kusan b'allata. Shin ina Nanny ta shiga? Tayi tunani a ranta.

  "Lay down for a bit I'll contact the school if there is any available vehicle we'll then take you home" nurse d'in ta sanar da Farrah tare da mik'ewa ta bar bay d'in. Ajiyan zuciya Lailah da guiwanta suka gama yin sanyi tayi "Farrah I'm sorry ban d'au rashin taus-"

   "Ni ai na gaya miki kika k'i jina, yanzu how are you going to get me out of this trouble? I've told you times without number ko mutuwa zanyi shi be damu ba I'm not his responsibility kawai dan ba yadda ya iya dani ne daya dad'e da korata daga gidansa" daga yadda take magana mutum ze san she's badly affected by d'abi'un da Ahmad yake nunawa akanta.
  "I'm sorry Farrah lay down bari school zatayi figuring out mey za ayi da ke."

*~.  D'NEL COMPANY AND ENTERPRISES.

   Zaune yake acikin fankacacen office nashi da AC ke tashi kaman hauka amma da alama shi hakan dai-dai ne a wurinshi tunda yake zaune comfortably aciki. Rik'e yake da mouse a k'ark'ashin tafin hannunshi ya duk'ufa akan abinda yakeyi cikin desktop dake gabanshi. Rolling sleeves d'in rigan shi yayi wanda hakan yayi exposing veiny muscled hands nashi. Ma shaa Allah idan akace kwana yake a gym babu wanda ze musa hakan saboda how well builded he is. D'ayan hannunsa ya d'aga ya ajiye kan fuskanshi yana shafe kan sajen daya kwanta lub a fuskansa. Da alama wani tunani ne ya carke mishi. Wata tsuka yaja sannan daga bisani ya ja wayanshi yayi dialing layin Nanny sede har ya tsinke bata d'aga ba. Wata tsukan ya sake ja had'e da kiran layin mal Isuhu inda yake ce mai switched off. "Argh!" Yayi letting out. "So what if she dies? It's not like she's my responsibility. Evergreen spring field? Where the hell is that?" Yayi maganar a fusace. Wulli da wayan nashi yayi akan table yana mey cigaba da abinda yakeyi sede ya kasa focusing. Kallo yakai ga agogon dake d'aure a hannunsa yaga 2:15pm. Mik'ewa yayi ya janyo suit d'inshi dake rataye a jikin hanger had'e da jan car key d'inshi da waya yafice. Parking lot ya nufa ya tada motanshi be ratsa ko ina ba se makarantar su Farrah with the help of google maps. Wannan ne karo na farko daya fara taka k'afansa cikin makarantar nasu dukda cewan shi yake biya mata school fees amma be tab'a damuwa ya tambayi Nanny wani makaranta take ba, iyaka in term yazo ya turawa Nanny kud'i shikenan. Number'n nurse d'in ya kira wanda be dad'e ba ta d'aga ba tare da ya bata daman magana ba yace, "Where is she? Tell her to step out I'm at the admin block" nan ma be jira jin response d'inta ba ya kashe. Itade mamaki take har yanzu "Your brother is here" tace da Farrah "Lailah see her out he's at the admin block."
  Miyau Farrah ta had'iye cike da tsoro da fargaba. "Nurse please call him back and tell him I've already left please."
  "What do you mean you've already left Farrah? He is already here I can tell how furious your brother is do not add to it."
   "Nurs-"
"Farrah please get up" ta katse ta. Ba yadda Farrah ta iya don dolenta ta mik'e tana d'aure da cardigan da Lailah ta bata. Jakarta Lailah ta dauk'a mata suka fice. Ba kalan addu'an da batayi ba kafin suka isa inda Ahmad yake jiransu. Ga de motar da tint amma ahakan ma ji Farrah take yana watsa mata kallo. "Ki bud'e min k'ofan baya please" tace da Lailah lokacin da suka iso jikin motan.

Hayateeyحيث تعيش القصص. اكتشف الآن