Chapter Seven

110 15 0
                                    



    Ba tare da b'ata lokaci ba washegari Nanny ta kira uncles d'in Ahmad ta sanar dasu halin da ake ciki. Na sosai sukaji dad'i tun ba yau ba suke shirin suga auren d'ansu. Nan da nan suka sa rana akan Lahadi za a je akai gaisuwa. Nanny na sanar da Ahmad ya kira waya ya sanar da Hamrah.
Hamrah dad'i kaman tasa ruwa a k'asa ta sha. Babu k'arya tana son Ahmad. Son da idan bata aure shi ba batajin zata iya cigaba da rayuwa. She loves him to the bones. Koda ya gaya mata ta kasa b'oye farin cikinta. Har yake neman tsokanarta yake cewa anya kuwa bayan auren nan bazata rufe shi a gida ta hanashi yawo ba. A k'arshen wayan ta ce mishi tana son su fita lunch date yau so from work zata zo ta d'aukeshi in ya amince. Suna gama wayan ta ruga d'akin Umma (mahaifyarta) tun daga bakin corridor take k'wala mata kira.

"Toh ki gama min sunan ki huta" cewar Umma dake zaune daga bakin gado a d'akinta. Dattijuwa ce kyakkyawa 'yar siririya base mutum ya tambaya ba kallo d'aya zaka mata kasan bafulatana ce. Ashe anan Hamrah ta samu kyan jikin da take dashi. Tabarakallah. "Ummaaaaaa" takirata had'e da fad'awa jikinta. Rik'ota Umma tayi "tou 'yar auta wannan farin ciki meya faru haka?"
"Umma yanzu muka gama waya da Ahmad."
"Ehen?" Umma ta tambaya out of curiosity.
"Yace Sunday ze turo magabatansa azo ayi gaisuwa" ta k'are tana tsalle.
"Ah ah abu yayi kyau kai ma shaa Allah shikenan Allah ya amsa min addu'ata zan ga auran 'yar auta ta kafin in mutu."
"In shaa Allah har jikokinki sekin gani Umma."
"Toh Allahu yasha Mamana ina wayata mik'o min in kira Babanku in sanar dashi yanzu yanzu." Nan da nan ta d'au wayar ta mik'a mata. "Nima barin kira Ya Khadija, Ya Fatima da Ya Faisal duk in sanar dasu."
"Toh auta."
   Duk yayyunta sun san irin soyayyan da takeyiwa Ahmad dan haka duk suka taya ta farin ciki. Hamrah fa ba wasa tun a ranan aka fara duba Instagram ana neman furnitures da sauran kayan gida. Se chan dare labari ya iske Farrah. Ita celebration da takeyi ma guda biyu ne. D'aya na kusan rabuwa da Ahmad d'aya kuma na taya Hamrah. Ita ina ma ace asa auren in less than 3 months Ahmad ya fita a rayuwanta for good. Ba na kad'an yake tak'ura mata ba a gidan nan. Right at the moment ta canza sunan Hamrah a wayanta ya koma coolest sister in law

   *** Yau ranan ya kama Asabar, kasancewan batada lectures tun 8 Esther tazo ta tada Farrah kaman kullum. D'akinta ta share tayi mopping sannan ta wanke ban gida tayi wanka ta sauk'o k'asa ta samu Nanny suka gama had'a breakfast. Bayan sun karya take sanar da Nanny cewan yau Lailah zatazo mata yini. Tana so su fita ice cream date. Ba gardama Nanny ta bata izini. Ashe duk Ahmad yana jinsu.
  Around 12 Nanny ta shirya Mal Isuhu ya kai ta unguwa. Nan Ahmad yasa Esther ta sauk'o mishi da takalmansa had'e da kiran Farrah. Polishing takalman yasa tayi, abinda ya dad'e be sata ba. Bakin nan Farrah ta turo shi kaman ze tab'a bango.
   "Allah sarki Ya Ahmad k'awata fa tana hanya so kake tazo ta sameni ina goge maka takalma?"

  "Mamaki kike? Ba Lucas ba ai bakiga komai ba."
  Miyau tayi saurin had'iyewa. Ta ina yaji sunan nan? Kawai tunawa da last call da sukayi da Lailah tayi. Inda take sanar da ita cewa Ahmad zeyi aure tace ai Lucas ma zeyi aure. Karde lokacin yana kitchen tayi wayan? Innalillahi! Ta shiga uku. Baki na rawa tace, "Ni yaushe?"
  "Ask me again. K'awarki dake tayaki b'arnan ce zatazo ba? Tazo ina nan ina jiranta itama" Gabanta ne ya mugun fad'i tafi kowa sanin halin shi yana iya disga mata k'awa idan tazo. Mafita yanzu shine ta kira Lailah tace mata tayi cancelling fitowan kawai dan gashi Ahmad ya gane suna ce mishi Lucas a bayan idonshi. Ba tare da b'ata lokaci ba ta turawa Lailah text explaining to her situation da ake ciki. Bayan data gama polishing mai takalman yasa ta haura dasu sama da kanta sannan Esther ta sanya masa su a d'aki. Next ya sanyata girki wai abokinshi zezo.

"Tou ba ga abinci Nanny ta girka ba."
  "Ba shi yakeso ba tuwo yakeso" ya sanar da ita a takaice.
  "Tou ai ni bana tuk'a tuwo sede inyi miya Nanny ce keyi."
  "Tou Nanny bata nan."
"Tou baga Esther ba se yaso inyi miya Esther tayi tuwon" ta mai bayani.
  "Yaushe muka fara ce ince dake?" Ya tambayeta. Nan take ta nitsu.
  "Kayi hak'uri wani miya za ayi?"
"Kub'ewa, sauran ki jagwalgwala abincin kiga abinda zan miki a gidan nan yau."
  "Naji" kad'ai tace sannan ta juya zata hau sama.  
"Ina kuma zakije kuma? Ko hanyan kitchen d'in kika manta?"
  "Zan yi sallah ne tunda azahar ya riga ya shiga." Be sake ce da ita komai ba. Wayanta ta d'auko ta ragewa Lailah abinda ake ciki. Ita de Lailah yau Allah ya mata alamnashara da harda ita za a had'a ayi punishing. Haka tana kumbure-kumbure ta sauk'o k'asa dan dolenta ta shiga had'a kan girkin ko da tasa Esther ta mata markad'e hana Esther yayi yace ita zatayi komai. Kuka ne kawai batayi ba ranan. Ahaka har ta samu ta had'a girkin ta tuk'a tuwon d'an kad'an wane na rowa. Tazo zuba tuwon kenan cikin flask Ahmad yace sam seta malmala kuma in taso tayi manyan malmala zata gani. Dan dolenta ta nitsu ta malmala tuwon mey kyau tayi arranging table. A gaje ta hauro sama zuwa d'akinta. Ji take kaman tayi aikin d'aga block. AC'n d'akin ta k'ure, bata kaiga mik'ewa akan gado ba Esther tayi knocking bakin k'ofar d'akinta.
  "Mey kuma?" ta amsa kaman zatayi kuka.
  "Ya Ahmad na kiranki."
  "Ni wai baiwarshi ce?!" Dan lalaci kawai ta shiga rusa kuka. "Wallahi bazan sake yadda in zauna a gida ni kad'ai dashi ba, ko bikin tsofi ne gara in bi Nanny." Hijabi ta mak'ala ta zo ta iskeshi. "Gani" tace zalla.
"Gani?" Ya d'ago kai had'e da nanata abinda ta fad'a.
"Na'am" tayi sauri ta gyara kanta. "Esther ta duba store babu Chivita ga 5k anan ki fita bakin hanya ki sayo min pack guda d'aya" ya sanar da ita.

HayateeyWhere stories live. Discover now