Chapter Four

114 15 1
                                    

"Toh Nanny zan koma d'akina, first thing Monday morning zan yi submitting form d'in" Farrah tayi maganan had'e da mik'ewa.
"Alright Farrah zaki sake sauk'owa ko in kin haura kin haura kenan?"
  "Eh bazan sake sauk'owa ba akwai kayakina da suka kasa min inaso inyi sorting nasu se akai gidan marayu. Nakega ina gamawa zan watsa ruwa in kwanta" tayi explaining "Gobe zamu fita spa date da Lailah."
  "Toh shikenan goodnight okay?"
  "Goodnight Nanny" nan ta d'au form d'in da wayanta ta wuce. Ko kallon gefen Ahmad batayi ba kafin ya watsa mata wannan mugun kallon nashi taci tuntub'e yanzu ba shiri. Bayan ta haura sama Nanny ta zo ta sami Ahmad akan dining, kujera taja ta zauna opposite to him yayinda ta tayashi bud'e flasks d'in yayi serving kan shi.

  "Ya jikin Abba?" Ya tambayeta.
  "Ba cigaba, last week nayi visiting d'inshi gobe in zan koma se muje ko?"
  "Allah kaimu" ya amsa blankly.
  "Yauwa Ahmad inaso muyi magana da kai."
"Go ahead Nanny ina jinki" ya amsa yana kai spoon baki.
  "Batun Farrah ne."
  "There you go again" ya furta k'asa k'asa sanin sarai zata ji sa.
  "Wai Ahmad baka san aikin lada kake bane? Marainiya ce fa yarinyar nan haba mana dan Allah."
"Aikin lada kam dayawa suke Nanny ba rik'e yarinyar nan bane kawai hanyan samun aljannah na besides har yau baki gaya min inda kika tsinto taba and why."
"Dalili ya wuce marainiya ce? Wai abu kaman wasa amma you're not ready to throw away your hatred towards this girl."
  "Why would I? Tun da tazo gidan nan mumunan k'addara suke ta afkuwa mana she's nothing but a black seed."
  "Yarinya 'yar k'aramar?" Ta tambayeshi da mamaki.
  "A idonki ba? She's old enough to bear children."
  "Tunda takai aure kam ai se ka aureta" ta fad'a cike da gatsine.
"Over my dead body" ya mayar mata. "Anyways what is it about her?"
  "Batun enrolling nata a university ne. Nasan baka sani ba but tana SS3 yanzu su zasu rubuta jamb da WAEC this year. Toh mun gama shawara mun kuma cika mata jamb form d'inta tace AUN takeso."
  "Who cares about abinda takeso?"
"Kaman ya Ahmad?"
  "AUN dake Yola zaku kaita?" Ya tambaya kaman beji bayanin da Nanny ta mishi ba just now. Kai ta gyad'a mishi tana jiran jin mey zece.
Smirking yayi kad'an "da permission d'in waye if I may ask? Last time I checked ni ne guardian d'in yarinyan nan ko ba haka ba?"

  "Ikon Allah yaushe ka fara nuna interest akan lamarin karatun yarinyar nan ko abinda ya shefeta? Naga kullum idan na kawo maka zancen school d'inta dismissing d'ina kake kace kai tsakaninka da ita school fees ne kawai."
"Toh na canza shawara Nanny, maganan university ake ba secondary school ba. Bazeyi in kaita just any university ba I have to know how capable she is."
"Aikuwa kaima kasan Farrah nada k'ok'ari wallahi tunda de bata tab'a wuce 10th position ba."
Wani dariyan rainin hankali ya sakar wanda ba k'aramin karb'ansa dariyar tayi ba, yanzu dama haka dariya ke amsarsa amma ya gommace yata murtuk'e fuska koda yaushe.

   "Yanzu ko kunya bakiji ba dan Allah? Wai bata tab'a wuce 10th position ba mstww" yaja k'aramar tsuka. "I know it dama ba abu d'aya that she is good at."
"Toh munji dai dama kowa ne seya ta d'aukan position 1st kaman ka? Mu ahakan ma mun gode. Dama kar ayi shawara ba kai ne nace in fad'a maka."
  "Shawara na yaushe kuma? Bayan keda 'yarki kun gama yankewa, ni ai it's more like you're just letting me know."
"Toh naga baka nuna interest akan duk wani abinda ya shafeta."
"Wani course?" Ya tambaya bayan sarai yaji su d'azu. "Biochemistry tace takeso."
Gyaran murya yayi "First of all 'yarki baza ta je AUN ba and second of all she won't be studying biochemistry either. Nan Baze zan sa a nema mata admission kuma engineering zata karanta" yayi bayanin with a straight face.

Fuska cike da mamaki Nanny ta tsaya tana kallonshi sannan daga bisani ta tambayeshi dalili.
  "Do I need a reason? Kina fa mantawa ni ne guardian d'inta."
  "It is only fair ka sanar dani reason d'inka" har anan bata fasa mamakin mugunta irin na Ahmad ba. "Because abinda nakeso ta karanta kenan" ya amsa a takaice "Ba ni ke biya mata school fees ba kuma ni zan cigaba da biyan na university'n ba? Don't you think it'll be only fair ta karanta course da nakeso tayi?"
"Kaji tsoron Allah fa Ahmad kai wa yake tak'ura maka a gidan nan? Kokuwa da kazo shiga university Alhj da Hajiya sunce seka karanta abinda sukeso? Ina ce baka choice akayi?"
"Dama akwai wanda ya isa ya tak'ura min a gida na ne kam? Abba da Umma kuma sun riga sun san I'm a bright student but I can't say thesame about your daughter."
"Gidan Abbanka de ko?"
"At least na Abba kikace ai ko? Ba kuma Abban wani ba Abba na."
"Kana kan bakanka kenan?"
"Unless kina so ki d'au nauyin karantunta from now on se in barku kuyi abinda kukeso kinga ko ba komai nima kud'ina zasu rage ciwo" ya amsa carefree. Numfashi taja cike da takaici ji take kaman ta gaura mai mari. Mutum ra'ayi kaman mey. In ba fitina ba da neman ya k'untata wa Farrah har yaushe ya fara damuwa da al'amarinta da ze ce sam ga abinda zata karanta? Sanin idan ya duk'ufa akan abu ba a iya sauya mishi ra'ayi yasa kawai ta sauk'o daga bala'in da take shirin mishi. "Tou naji bazata je AUN ba amma dan Allah ka barta ta karanta course of her choice."

HayateeyWhere stories live. Discover now