Chapter Six

117 15 0
                                    


"Mazaaaa" ya kirashi going in for a shake.
"Yane meya kawo ka da tsakar rana haka?" Ahmad ya tambayeshi bayan da suka gaisa.
"Meeting da mukayi is close by nace barin yi branching inga abokina" ya amsa tare da zama.
"Ka kyauta. Yane tou ya ake ciki?"
   "Lafiya k'alau fa ya aiki?"
"Da godiya ya naka?"
"Alhamdulillah, yaya Hamrah?"
"Tana nan" ya amsa ba yabo ba fallasa.
"As aminin ka yaushe zaka kaini ne mu gaisa da amaryar tamu?"
"Wai amarya haka nace maka zan aureta? Kai dad'i na dakai you're way faster than your shadow, ce maka akayi daga ganin sarkin fawa se miya tayi zak'i?"
"Kai kuma dad'i na dakai wannan shegen ego nakan, bafa haka ake soyayya ba dole ne ka sauk'ar da kanka ka kuma k'ask'antar da kanka idan kana son soyayyar mace if not zaka sha mamaki."
"Tou love expert" yayi maganan had'e da fita daga tiktok sede wani hanzari ba gudu ba idon Mahmood yaga wata kaman Farrah ta ciki.
"Wa nake gani kaman k'anwarka Farrah?" yayi saurin tambaya.
"Oh" Ahmad ya numfasa had'e da kai duban shi kan wayan nashi "Itace" ya amsa "Page nata ne ya fito min a tiktok" yamai bayani. Cike da zumud'i Mahmood yace a nuna mishi ba musu Ahmad ya mik'a mai wayar nan yabi ya kalla sama-sama. "Maza wannan k'anwar taka fa ba k'aramin traffic zata ja ba idan ta shiga university Allah."
"Wannan d'in? Mstwww."
"Allah kuwa."
"Yanzu ina tsari a irin wannan videos? Karta damu zata sauk'esu ne tass."
"Kai de maza ina ruwanka ba abinda yara around her age sukeyi ba kenan? Allow the little girl to enjoy life."
Da mamaki Ahmad yake kallonshi "Yanzu ko wani k'ato ya shiga page nata ya kalla videos d'innan does that sound okay with you? Kalli fa har wa'inda ba d'ankwali."
"Hoho" Mahmood ya shiga teasing d'inshi "Kishinta kake?"
"I beg your pardon. A dalilin mey zanyi kishinta I'm just generally speaking ko sister'nka ce naga irin abinda takeyi a social media kenan I'll definitely call her out so karma kace zakayi twisting words d'ina" yayi bayanin kanshi in a stern voice.
"Tou naji, Farrah de Tabarakallah Allah ya mata baiwan kyau."
"Ina amfanin kyau ba tsafta? Kasan k'azantarta kuwa ko shara bata son yi se zafin kunna turaran wuta."
"Ka yarda tana da kyan kenan?" Yayi maganan cike da gatsine.
"Toh inde kyau ne waye bashida?"
  'Yar dariya Mahmood yayi "Gaskiya ma shaa Allah nawa kace shekarunta again?"
  "How will I know ni na haifeta ne? But guessing from her class baza tafi 17 ba."
  "Gaskiya se kun sa ido akanta-"
"Can we please talk about something different?" Ahmad ya katse shi "Yaushe Farrah or whatever ta zama topic of discussion?" Yayi maganan ranshi na neman b'aci.

"Maida wuk'an abokina, gyara kayanka fa be zama sauk'e mu raba ba. Dan kawai zance kusa ido a kanta inta shiga university kar a b'ata muku kyakkyawar yarinya shine nayi laifi?"
  "Toh a b'ata d'in mana ina ruwanka? Nima meya sani aciki? Damuwanta dana mamanta."
  "Mamanta wa kenan Nanny?" Mahmood yayi maganan yana dariya "Bade kishin relationship nata da Nanny kake ba maza?"
  "Mstww ni ina ruwana kaga mik'a min wayana" yayi maganan had'e da fisge wayanshi. By now dariya sosai Mahmood yake "Gaskiya akwai kallo a gaba Hamrah ta shirya kai de wato duk abinda kakeso baka so ka raba shi da kowa."
  "Eh mana nothing good comes out of sharing." Hira suka d'an tab'a daga nan suka je sukayi grabbing lunch tare. Dawowan Ahmad gida keda wuya. Yau ma se wuraren goma da rabi ya dawo. Lokacin kowa ya kwanta bacci illa Farrah dake faman koyan wani tiktok challenge. Wani k'ara cikinta ya saki ko abinci tak'i ci tun Nanny na binta har tagaji ta fita daga harkanta.

Sanye take da shorts da vest. Wayanta taja ta fito waje bata damu da d'auko lullub'i ba saboda taga sha biyu ake nema inba jaraba ba kam ba abinda ze sauk'o da Ahmad k'asa warhaka. Kitchen ta nufa ta bud'e fridge in search of what to eat. Sausages ta ciro nan da nan ta kunna gas ta d'iga man gyad'a akan frying pan sannan ta d'au wayanta tana d'an danne dannenta kafin yayi zafi. K'amshin turaran Ahmad ne ya bugi hancinta hakan yasa tayi saurin d'ago da kanta cike da fargaba. K'aran muryanshi ta ji yana doso kitchen da alama yana kan waya ne. Rasa inda zata b'uya tayi. Tayi nan tayi chan ahaka har ya isketa a kitchen d'in. Da sauri ta sunkuya k'asan counter.
  Wato bata dena yawo da k'ananun riga cikin gidan nan ba ya tambayi kanshi lokacinda yaganta. "Hamrah ina zuwa will call you back" ya ce had'e da katse wayar. Wani azababben yunwa yake ji shima dake beci dinner ba rabonshi da abinci tun lunch. Ganin sausages take soyawa ya gane indomie take shirin dafawa. Bece mata komai ba yafita ya koma parlour ya zauna. Bayan da ta tabbata ya fita ta fito daga b'uyar nata da sauri tayi turning sausages d'in karya k'one. In akwai abu d'aya da Farrah ta k'ware a iya girkawa tou shine indomie. In ta tashi yiwa indomie d'inta ado wane fried rice. Slicing ingredients d'inta tayi ta d'aura ruwa acikin tukunya. Nan da nan ta gama garnishing indomie d'inta k'amshi har palour yana dukan hancin Ahmad. Seda ya bari tagama girkin dab tazo hawa sama ya tsayar da ita. "Farrah" ya kira sunanta chak ta tsaya tunda tasan kanta Ahmad be ta6a kiran sunanta ba daga yace mata "ke" se "heyy" most of the times ma fad'a mata abinda yakeso kawai yake yi ba tare da yayi addressing d'inta ba.

HayateeyWhere stories live. Discover now