Chapter Nine

126 14 0
                                    


"Subhanallahi ciwon kai?" Nanny ta tambaya had'e da maido da kallonta akan Ahmad "Bade migraine naka d'innan ke neman tashi ba?"
Ahmad was too stunned to speak. Ya ma rasa mey zece "Eh?" Zalla ya iya furtawa.
"Eh Nanny yace in kai mishi warm water sama ya ajiye kan goshinshi" Farrah ta sake cewa.
"Toh yi sauri mana Farrah. In danne maka ko zaka yi da kanka?" Nanny ta tambaya had'e da dawo da kallonta akan Ahmad da har anan ya kasa dena mamaki.
"Zan yi da kaina" bakinshi da yayi nauyi tun d'azu ya furta idonshi na akan Farrah har anan. So yake ta juyo ta kalleshi ta mishi bayanin wannan k'aryan nata data sanya shi aciki amma jin k'wayoyin idanunshi akanta tak'i juyawa ta kalleshi. "Ka haura sama Ya Ahmad zan taho maka da ruwan d'umin" tace had'e da wucewa kitchen da sauri.
"Eh bismillah Babana barin d'an kalla Indian series d'ina nikuma Allah sawwak'e" Nanny tayi maganan tare da k'ariswa parlour ta d'au remote daga kan centre table.

   Ahmad was left with no choice, haka ya haura sama zuwa d'akinsa. Safa da marwa Farrah ke tayi a kitchen d'in, yanzu ta d'iba ruwan zafin ne dagaske takai mishi? Ko ta banzar da maganan? Bata kaiga kawo wani tunani a ranta ba Nanny ta k'wala mata kira.
"D'ibo ruwan zafin ne har yanzu ko se kan nashi ya fara ciwo sosai tukuna zaki kai mishi?" Nanny da ta ji Farrah shiru tun d'azu ta tambaya daga parlour.
"A'a Nanny gani nan" Nan da nan ta d'auko bowl tasa ruwan zafi ta sirka ya zama warm sannan taja kitchen towel d'aya ta yi hanyan d'akin Ahmad. Sede ko da ta isa bakin d'akin nashi ta kasa knocking. Tsaye tayi wajen tana tunanin mafita. Daga bisani kawai ta d'aga hannu tayi knocking sau d'aya. Seda ya d'aukeshi kusan minti biyu sannan ya taso daga kan study d'inshi inda yake zaune yazo ya bud'e k'ofan.
Ko d'aga ido ta kalleshi ta kasa bowl d'in kawai ta mik'a mai "Gashi" ta fad'a kanta a sunkuye.

   Tsayuwa yayi yana kallonta dan har anan bata isheshi da kallo ba. Is it that dan taga ta girma yanzu maza suna cewa suna sonta left and right shine take jin kansu d'aya ne a gidan nan ko kuwa shi ne ya sake mata fuska dayawa har wannan rainin ya shiga tsakaninsu? Yaga a da ko magana bata iya mishi banda gaisuwan da shima ya zama mata dole. Amma yanzu har k'arya zata shirya ta sanya shi aciki? Lallai he's been going easy on her.

   "Shigo ki ajiye da kanki" taji muryanshi ya fad'a. Kai ta d'ago cike da tsoro ta sauk'e akanshi. "Ko kin manta kaina yana ciwo kike so in karb'a da kaina?"
  Shiru tayi har anan ta kasa cewa komai banda raba idon da takeyi. 
   "Hausa ne kika dena ji?" Ya tambayeta. "Ki shigo ki ajiye nace."
  "Ya Ahmad dan Allah kayi hak'uri" tayi saurin cewa.
  "Hak'urin mey kike bani kuma? Hak'uri kam ai nayi shiyasa kika ga ban tona miki asiri a gaban Nanny ba nayi covering up lies d'inki."
  "And I'm very grateful for that Ya Ahmad but dan Allah kayi hak'uri."
  "Shine fa nace ki shigo."
  "Ya Ahmad nide dan Allah kayi hak'uri" har anan tak'i shiga ciki kaman yadda ya buk'aceta.
  "Farrah you're wasting my time ko so kike inje in samu Nanny in irga mata komai?" Ganin fa dagaske yake tayi saurin dakatar dashi kafin yayi stepping a foot out of the room. "A'a zan shigo zan shigo dan Allah kar kayi abinda Nanny zata ji." K'ofan ya dad'a bud'awa creating more space for her. Miyau ta had'iye sannan a sanyaye ta shiga ciki ta tsaya tana kallon k'asa. Firgita tayi dataji ya mayar da k'ofan ya rufe. Tunanin mey Ahmad yake shirin yi mata ta shiga yi.
  Cike da k'asaita ya taka ya koma wajen study nashi ya zauna yana kallonta. Har anan Farrah tak'i d'aga kai ta kalleshi. "Jeki juye ruwan a bathroom" ya buk'aceta.
  "Ya Ahmad I'm sorry."
  "Inzo in karb'a in zubar da kaina ne?" Ya tambayeta had'e da d'age gira d'aya.
  "A'a zanyi zanyi dan Allah kayi hak'uri" da sauri ta nufi wajen bathroom d'in ta bud'e ta zubar da ruwan ta fito.
  "Zan iya tafiya?" Ta tambayeshi cikin siririyar muryanta. "You think haka kawai zan rufa miki asiri? You have to pay for the price of course" ya jaddada mata yana wasa da ball pen dake hannunshi.
  "Ya Ahmad tun d'azu fa nake ta baka hak'uri, kayi hak'uri mana."
  "Kefa kikace you'll do anything I ask of you koba haka ba?"
"Hakane" ta amsa tare da had'iye miyau. "Where is your phone?" Ya tambayeta out of nowhere.
  "Wayana?" Ta maimaita bade shirin seizing mata waya yake ba? Yes taca ta gommace ya mata seizing waya daya fad'awa Nanny amma kuma se yayi dagaske?
  "Ina yake?" Muryanshi ne ya tsamota daga tunanin da takeyi.
  "Gashi nan" ta amsa cikin k'aramin murya had'e da sa hannu a pockets nata ta zaro wayan. "Ya Ahmad dan Allah kayi hak'uri kar ka min seizing waya na tuba bazan sake ba" ta shiga rok'anshi.
  "I'm not about to seize your phone" ya sanar da ita wani haii taji a ranta ta shiga godewa Allah.
  "Come closer" ya buk'aceta. Cike da rashin fahimta tayi kaman yadda yace. "Closer" ya sake buk'atar ta har seda ta iso inda yake zaune. "Unlock your phone and pass it to me" ba gardama ta bud'e tayi kaman yadda yace. Tiktok nata ya bud'e yakai kan profile nata. "Gashi goge dukka videos d'innan take each and everyone of them down" ya sanar da ita had'e da tura wayan ta side dinta.
   Ido ta zaro cike da k'in yarda "Eh?" Taya ma yasan tana tiktok? Bade video nata ya tab'a fito mishi a fyp ba har ya ganta yasan tana tiktok. Wayyooo ta shiga uku. Bade Ya Ahmad ya kalli duka tiktok videos nata ba?
 
  "Don't let me repeat myself" ta ji muryanshi. Kallonshi take cike da mamaki har anan. Yanzu fisabilillah tiktok videos nata duka yakeso ta sauk'e? Ya ko san views da likes nawa take samu a videos nata da ze ce ta goge? Shin mey had'inshi da videos nata? Eh tasan akwai wa'inda ko d'ankwali bata da amma yaushe ya fara damuwa da abinda takeyi da rayuwarta?
  "Ya Ahmad dan Allah kayi hak'uri" tayi maganan tamkar zatayi "Dan Allah karka sani goge videos d'ina na amince ko wanki ne kasani inyi maka I'll do anything but please don't make me delete my tiktok videos please."
  "I thought by now kin san halina, I don't do things to please you Farrah, ko ki goge da hannunki ko in goge kuma inyi seizing wayanki and go ahead and tell Nanny everything, you choose" yayi threatening d'inta.
  Ji Farrah take kaman ta rufe shi da duka inda zata iya shin wani irin mutum ne shi? What will he benefit from making her delete her videos? Fuskanshi ne ko nata? Itade ta lura duk wani abinda ze sata acikin b'acin rai shi yake son yi. Allah sarki videos nata, just yesterday wani video nata yayi hitting 1million views yanzu ahaka yake so ta goge? K'walla ne ya ciko mata a ido a tunaninta wai idan Ahmad yaga tana hawaye ze tausaya mata ya canza ra'ayi sede ba haka abin yake ta fannin Ahmad ba. Dad'i yakeji idan yaga tana kuka hakan is only proving to him taji zafin abinda ya mata, burinshi kenan kuma dama ya k'untata mata. He just finds joy in making her suffer.  Ganin fa kukanta baze canza wa Ahmad ra'ayi ba kawai ta d'aga wayan. "Akan table d'in zaki goge ina ganinki" ya sanar da ita sarai yasan tana iya changing privacy settings nata instead of ta goge. Ido ta d'ago tana kallonshi tana mamakin yadda yayi reading mind nata dan da ya barta privacy settings nata take da niyyan canzawa seta b'oye videos d'in instead of deleting them. Batada wani mafita kuma yanzu haka ta mayar da wayan kan table d'in ta shiga goge videos d'in one by one Ahmad yana kallonta. Tazo kan top 3 most liked videos nata da tayi pinning taji fa bazata iya gogesu ba.

HayateeyWhere stories live. Discover now