Chapter Five

129 20 1
                                    


  "Wani abu kike b'oyewa ne da bakiya so yaje yayi figuring out?"
   "Mey zan b'oye nikam" tayi maganan fuskanta a murtuk'e tana turo baki. Gabad'aya ta rasa meke mata dad'i. Taya Nanny zata mata haka bayan tafi kowa sanin halin Ahmad.
  "Idan notes d'inki complete bakiya rashin ji shi Ahmad d'in mahaukaci ne da ze miki masifa ba gaira ba dalili?"
  "Ai kinfi kowa sanin halin shi Nanny ko bakayi komai ba seya nemo laifin da ze baka."
  "Tou so kike inyi cancelling appointment d'ina kenan ko mey?"
  "No amma ni karki ce mishi yaje min open day bana so maganin bari kada a fara."
  "Too bad Farrah na riga na fad'a mishi."
  "Nannyyyyy!!!" Ta kirata tamkar zatayi kuka "Dan Allah kice wasa kike."
  ""Dagaske nake mana muna wasa dake ne?"
  "Ahapss nasan ma ba amincewa zeyi ba koda kin tambayeshi" ta fad'a tana kwantar da hankalinta.
    "Toh kuwa ya amince" Nanny tayi assuring d'inta.
"Nanny ni bana son wannan expensive joke nakin Allah" sede fa expression dayake fuskan Nanny beyi kalan na mutumin da yake wasa ba. 

   Matsowa jikinta tayi tare da manna fuskanta jikin saman hannun Nanny. "Dann Allah kice min wasa kike, taya zaki min haka Nanny?"
  "Wallahi dagaske nake kuma da kinsan wahalan dana sha kafin ya amince yace ze je miki da bazaki zauna kina wannan shirmen ba."
  "Har wani jan aji yake dama nace yaje min ne ba duk ke bace ki had'a ni da Mal Isuhu ma mana fisabilillah."
  "Farrah bana son surutan banza kina ji na ko?"
  "Tou meyasa baza ki bani ko head ups ba?"
  Wai kam mey kike b'oyewa ne?"
"Nanny wallahi Ya Ahmad zemin ba dad'i some of my notes are not complete idan yaji wallahi har mari ze iya b'alla min a bainan nasi" ta sanar da ita cike da tashin hankali.

  "Yaushe kika fara wasa da studies d'inki Farrah? Keda ya kamata ace yanzu zaki sake dagewa amma dan kinga kun kusa gamawa se kika fara wasa ko?"
"Nanny wallahi ba haka bane yanzu ni ya zanyi?"
"Ya kuwa? dole ki biya laifin da kikayi ai ba wani ya hanaki updating notes d'inki ba. Ni matsa mun" tayi maganan had'e da janye hannunta daga jikin Farrah. Da wuri ta sake rik'o hannun.
   "Dan Allah Nanny stop him wallahi kin fi kowa sanin halin shi" ta shiga rok'arta.
"Tare da shi zaku fita gobe in kika sake kika sa shi latti kuma ni ba ruwana" ta fad'a a takaice tana mey share maganan da Farrah tayi.
"Wallahi Nanny kin dena sona a gidan nan yanzu."
"Seda safe ko?" Nanny ta sanar had'e da mik'ewa "ki samu ki kwanta da wuri" tana kaiwa nan ta yi ficewanta.
"Ya Rabbi" Farrah ta furta had'e da ad'awa kan gadon tana mey nazarin yadda zata b'ullo ma wannan al'amari. Chan ta janyo wayarta ta shiga kiran Lailah wanda seda ya kusa yankewa ta d'aga. "Bestyyyy" ta kirata cike da jin dad'i "Babe now is not the time for this."
"Yane wani abu ya faru ne?"
"Hmm, baki san d'anyen aikin da Nanny ta jik'a min ba."
"Meya faru bani labari" Lailah tayi inquiring.
"Wai kinsan wa ze je min open day gobe?l
""Nanny?"
"In itace ai bazan yi complaining ba."
  "Tou waye?"
  "Lucas fa! Of all people!" Ta sanar da ita tamkar zatayi kuka.
"Lu- Lucas fa kikace how??"
  "Kede ki tambaya."
  "Kekam bani labari how? Har ya Nanny tayi convincing d'inshi ya amince? I thought you are the last person he'd want to waste his time on."
  "Exactly" nan Farrah ta kwashe labarin komai ta bawa Lailah. Mamaki ne ya cika Lailah har ya akayi Nanny tayi convincing Ahmad ya yarda zezo?

   "Besty ko de mugunta yake shirin miki ne?" Ta tab'e baki "Kinsan neman dama yake ya k'untata miki. Kede taki jarabar dayawa take."
"Wallahi nima ina ji ajikina wani ramin mugunta ya tona min Allah kad'ai yasan meyake shirin mun."
"Wayyoo! gashi gobe full house kar Lucas ya disgaki gaban Affan dai" ta k'are maganan tana dariyar mugunta "mstww ni ina ruwana da wani Affan? Na tab'a ce miki yana gabana ne? Shi d'ayanshi yake one sided love d'inshi. Ni yanzu duk ba wannan ba how can I prevent muguntan da Lucas yake shirin min gobe?"
"K'arfe nawa Nanny zata fita gobe?" Lailah ta tambaya.
"Kaman 8 tace."
"Toh idan har kina son rufin asuri wallahi karki sake ki bi shi ku taho school gobe."
"Mey kike nufi?"
"Kiyi k'aryan rashin lafiya precisely period pain kice ko motsawa bakiya iyayi."
"Nanny zata san k'arya nakeyi tana tracking cycle d'ina a wayanta."
"Shine ai seta tafi sannan zaki had'a k'aryan."
"Lailah kin tabbata? Kar in sake jefa kaina cikin wani trouble d'infa kinsan halin Lucas."
"Toh kina da wata shawara ce?"
"Babu wallahi na buga ta ko ina na kasa thinking of a way out."
"Then muyi yadda nace dan nima jikina na bani zezo ya shuk'a miki rashin mutunci ne kawai goben nan."
"Toh shikenan bestyyy I'll see about it Allah taimakeni."
"Ameeen you got this."
"Tou se munyi magana anjima."

HayateeyWhere stories live. Discover now