Chapter Three

123 19 1
                                    


   "Are you not eating?" Ya tambayi Nanny yana binta da kallo.
   "I'll amma ka gama first, zamu haura sama da Farrah" ta sanar dashi "Farrah ina kike muje ko?"
  "Yauwa za a kai duka motocin service" ya sanar da ita daga bisani. Da mamaki ta tsaya tana kallonsa
  "Why all of a sudden?" tayi saurin tambayanshi yayinda Farrah dake lab'e daga bakin k'ofan kitchen take sauraransu.
  "Baza a iya kaiwa gobe bane Ahmad?"
  "In za a iya kaiwa yau why wait until tomorrow?" Ya tanbaya yana picking chips da fork dake hannunsa.
  "Farrah ce takeso taje gidan k'awarta" ta sanar dashi hoping ko hakan zesa ya canza shawaranshi.
  "Na rik'e k'afanta ne?" Ya tambayeta had'e da d'ago kansa daga kan plate dake gabanshi izuwa kan Nanny dake kallon shi cike da mamaki. Why is she even surprised? Sarai ta gane mugunta ne kawai irin nashi ba wani abun ba. Da yabar Farrah ta fita taji dad'i ya gommace ya sake kai motocin garrage, dududu befi 3 weeks akaje akayi servicing d'insu ba amma yake sake zancen kaisu servici again.

  "Ahmad why are you being like this?"
"Nanny please" yayi saurin katseta "bana son surutu idan ina chin abinci you know that." Bata sake ce mishi komai ba tayi wa Farrah ido da nufin su haura sama. Farrah de takaici ya gama mata yawa ji take kaman taje ta kifa mishi mari. Shi shikenan banda mugunta ba abinda ya iya fisabilillah. Kallonsa take tun daga bakin k'ofan kitchen din. Sarai yaji tana binshi da kallo amma ya dake, daga bisani kawai ya d'ago kanshi sukayi ido hud'u. Wani mugun kallo ya watsa mata wanda tuni yasa ta sunkuyar da kanta har tana neman chin tuntub'e. Satisfyingly ya maido da kallonshi akan plate d'inshi yana mey cigaba da chin abincinshi.

****
"Kiyi hak'uri kinji Farrah na? Gobe in shaa Allah zakije gidansu Lailah ai de baze bar motocinshi su kwana a garrage ba komin rintsi yau za a sake dawo dasu."
"Nide na rasa meyasa yake min haka it's not like ina mishi rashin kunya ko wani abu Nanny."
"Nanny loves you my baby and that is all that matters kinji? Ki manta da sabgan Ahmad da gangan yake yin komai, sooner or later zeyi realizing gaskiya shima." Kai ta gyad'a a hankali dukda tasan cewa fa da k'yar idan Allah ze k'addaro mata da ranan da ita da Ya Ahmad zasu fara shiri. Dan neman magana irin na Ahmad ko da aka gama servicing motocin aka ce za a dawo dasu gida cewa yayi a bari su kwana a garrage saboda yasan ba inda za sa. Washegari ma se kusan 4 aka kawo motocin. Farrah har ta cire tsammanin zata fita se kawai taji k'aran bud'e gate. Nan da nan Nanny ta tayata shiri Mal Isuhu yayi dropping nata off a gidansu Lailah.


      **~~
   Haka kuma rayuwa ta cigaba da kasance musu a gidan. Ahmad sede beji Farrah zatayi wani abu ko zataje wani waje ba, se yayi abinda ze iya don ya hanata cimma burinta na ranan. Bak'in hali ba wanda be iya ba, Nanny har ta dena mishi magana saboda ko tayi ba jinta yake ba. Acikin watanni uku Ahmad yagama shiri yayi processing visa d'inshi ya wuce United Kingdom inda yaje yayi karatun masters d'inshi. Farrah couldn't be happier! Lokacinda ya tafi karatu dai-dai time d'in take shiga SS1.

   Yau shekara biyu da watanni kenan tun tafiyan Ahmad. Tun da ya tafi shi da Farrah basu sake sa juna a ido ba ko suyi magana ta waya. Da Nanny zalla yake yin voice or video call, dai-dai da rana d'aya be tab'a tambayan ko ya Farrah take ba.
  Itama Farrah bata tab'a samun kwanciyan hankali irin na lokacin nan ba. Tuni ta mulmule tayi 'yar kib'a wanda ya mugun sake fito da kyanta. Tanada k'imanin shekara goma sha shida (16) yanzu amma mutum na iya cewa takai wani sha takwas. Doguwa ce ma shaa Allah, ga wani kyau da k'warjinin data k'ara da shekaru. Son kowa k'in wanda ya rasa. Watan da zasu fara shirye-shiryen WAEC Ahmad ya fara processing dawowanshi.

   Ranan dawowan Ahmad...
    Tun safe da Nanny ta tashi bata zauna ba, tayi nan tayi chan. D'akin Ahmad tasa an share na uku kenan haka ma bathroom d'insa. Se ansa wannan bedsheet tace a cire asa wani daban. Ta de kasa zama, bayan an gama kimtsa mishi d'akinsa tsaf ta wuce kitchen  Duk wani favorite abincin Ahmad da tasani ta shiga girkawa. Farrah da Nanny ta sakalta da gata kam se pass 11 ta tashi daga bacci. Wanka ta soma yi tasa rigan shan iskanta ta sauk'o k'asa. Tun daga staircase aroman girkin Nanny yake dukan hancinta.   "Nannyyyyy" ta k'wala mata kira dai-dai lokacinda ta k'araso bakin kitchen d'in.

HayateeyWhere stories live. Discover now