Chapter Ten

299 21 30
                                    

LAST FREE PAGE.
SANARWA!!!
ASSALAMU ALAIKUM LOVES💕 dafatan kowacce tana biye dani tana kuma jin dad'in wannan labari. Kaman yadda kuka sani HAYATEEY is a paid story (littafin kud'i ne) kuma yau shine k'arshen 10 free pages dana muku alk'awari. Duk me son cigaba da karanta wannan littafi should kindly pay into this account number



Yanayin yadda posting ze kasance:
For REGULAR zan na posting once daily (sau d'aya a rana kenan) kwana biyar a sati banda weekends. While for VIP zasu dinga samun pages 2 everyday, a Weekends kuma maimakon pages biyu post sau d'aya ne a rana. A takaice regular pages 5 a sati VIP kuma pages 12 a sati.
Thank you 💕

Babu wadda zanyi ma Allah ya isa don ta fidda mun book saboda nasan Allah shine ma ishi, kuma ina da yak'inin mutanen dana tara ba zasu fidda mun book ba, idan kuma sun fidda ina da kyakkyawan zato a kan duk wadda ta karanta zataji tsoron Allah ta biyani hakk'ina.
Allah ya k'ara ma rayuwarmu albarka.




  "Meyasa zan baki details na dollar account d'ina kam?" yayi maganan had'e da bud'e k'ofan d'akinshi ya shiga ciki, be kai ga rufe k'ofan ba Farrah tasa hannu ta dakatar dashi.
"D'akin nawa zaki shiga?" Ya tambayeta sarcastically. Dad'a bud'e k'ofan ya mata "Bismillah tou shigo."
"Ayya mana Ya Ahmad please."
Daga bisani kawai abinda ya faru a tsakaninsu ranan ya fad'o mishi a rai. Zuciyansa ne ya fara wani irin bugu. Da sauri ya kawar da kallonshi daga gareta. "Ya Ahmad?" ta kira shi ganin ya nisanta tana mamakin ko tunanin mey ya shiga yi a karo guda haka.
Kaman mey aljanu kawai ya canza a lokaci d'aya "Leave Farrah" ya sanar da ita.
"Ya Ahmad Allah sarki."
"Leave before I change my mind and daga yau kar ki sake taka bakin k'ofan d'akina." Yana kaiwa nan ya buga k'ofan ya rufe wanda hakan yasa gaban Farrah fad'i. Meya sameshi a lokaci d'aya haka? Farrah ta tambayi kanta tana mey mamaki. Kode ta fad'i wani abinda be kamata tace bane? Amma kuma ai ba abinda ta fad'a da ze b'ata mishi rai. Kode sunyi fad'a ne da Aunty Hamrah fitan sa? Ji tayi gabad'aya ta rasa sukuni tun yaushe ta fara damuwa da halin da Ahmad yake ciki? Yaushe a gari? Ina ruwanta dan yana cikin damuwa? Farrah get back to your senses. Juyawa tayi ta dawo parlour ta zauna, kallon take amma hankalinta gabad'aya na akan Ahmad, maimakon taji haushin shi ya hanata abinda take buk'ata sema damuwa take ko wani abu ne ke damunsa for him to act the way he did.

   Ta b'angaren Ahmad kuwa ya kasa gane meyake ciki ko mey ke faruwa da shi. Har anan zuciyarsa bata bar dukan tara-tara da takeyi ba. Hannu yasa ya aza a kan beating heart d'inshi. Baya son wannan bak'wan yanayin. Meyasa yake tunawa da abinda ya faru ranan? Why can't he seem to get Farrah out of his mind? Kayan jikinsa ya rage ya fad'a bayi, kaman na ranan yau ma ya kunna hot shower ya tsaya a k'ark'ashi ruwa na dukanshi. Ya kusa 30mins aciki sannan ya fito amma duk da haka ya kasa dena tunanin Farrah. Da ya kulle idonsa, fuskanta yake gani haka zalika idan ya bud'esu. Missed call d'in Hamrah ya tarar, amma ina ya kasa kiranta. System d'inshi ya d'auko ya fara aikin office with the hope ko hakan ze d'auke mishi hankali daga tunanin da yakeyi.

   Bayan ya dawo daga sallan Isha ya tsaya yaci abinci suka d'an tab'a hira kad'an da Nanny sannan ya haura sama d'akinsa. Wallet nasa ya bud'e ya ciro credit card d'inshi. D'akin Farrah direct ya wuce yayi knocking wanda ba tare da b'ata lokaci ba ta amsa. "Yes?"
K'ofan ya bud'e a hankali, ganin shine da sauri ta ja hijabi ta sanya tare da mik'ewa tazo ta sameshi daga bakin k'ofan.
  "Ya Ahmad?" Ta kira shi. Hak'uri yake so ya bata for acting like an ass da yayi d'azu amma ya kasa. Why is he even feeling sorry towards her? Yaushe ya fara damuwa da feelings d'inta?
"Ya Ahmad?" Muryanta daya tashi ne ya tsamo shi daga tunanin da yakeyi. Kanshi yayi saurin kad'awa, "Abun nawa zaki saya?" yayi maganan yana mik'a mata katin. "Ya Ahmad!" tayi exclaiming cike da mamaki da kuma farin ciki.
  "Baze fi $200 (dala d'ari biyu) ba in shaa Allah" ta amsa tare da amsan katin.
  "In kin gama ki kaiwa Nanny gobe zan karb'a a wajenta" ya sanar da ita tamkar ba shi bane yagama sulleta d'azu harda ce mata kar ta sake taka k'ofan d'akinshi. In ta karance halin Ahmad tamkar mey aljanu haka yake acting atimes, one minute he's free the next minute he's angry. Nevertheless she's so happy ya sake tunani ya ara mata katin nashi.
  "Alright tou thank you so much Ya Ahmad." Be sake cewa komai ba ya juya ya wuce d'akinsa. Tsalle Farrah tayita dakawa a d'akin. Nan da nan ta d'au wayanta ta kira Lailah ta bata labari.  
  "Ah ah bestyy kibar gaya mun!" Lailah tayi maganan cike da k'in yarda.
  "Wallahi tallahi zanyi snapping card d'in yanzu in tura miki ta snap."
  "Lucas d'in dai?"
  "Shi fa!"
"Tou da alama mun kusa canza mishi suna zuwa Gabriel" tayi maganan tana dariya. Dariyan itama Farrah takeyi. "Kede bari Lucas anyi abun kai Allah sa ba mutuwa yake shirin yi ba dai dan ance idan mutum mey banzan hali yazo mutuwa yana yin aikin kirki."
  "Kede muguwa ce wallahi Lucas d'in kike wa fatan mutuwa wato? Bari yazo ya karb'i katinshi maga idonki."
  "Fatanki ya sari guntun kashi muguwa, ke! se anjima bara in zauna inyi ordering abubuwan 'yan Korea na na kafin Ya Ahmad ya sake canza shawara kinsan shi kaman mey aljanu."
  "Yanzu dagaske akan mutanen korean nan naki zaki k'arasar da kud'in nan?"
  "Yo koda kud'in aljihu na ma zan saya abubuwansu bale yanzu dana samu kud'i daga sama kede tsaya kiga aiki da cikawa, se mun sake magana" tana kaiwa nan ta katse wayar.
Kaman yadda Ahmad ya buk'a ceta hakan tayi data gama abinda zatayi da katin ta kai ta bawa Nanny ajiya.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 26, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HayateeyWhere stories live. Discover now