Chapter Eight

112 12 0
                                    


"Ya Ahmad?" Ta ambaci sunanshi a fili. Waje ta sake lek'owa to be sure sannan ta sake komawa ciki da mamaki bayyane karara a fuskarta. Kayan daya sa jiya ne tayi tozali dashi rataye a jikin hanger. Hakan ne ya sake tabbatar mata da cewa lalle-lalle a d'akinshi take. "Innalillahi na shiga uku Ya Ahmad ze yanka ni mey nakeyi a d'akinshi" ta furta a kid'ime. Blanket nata data gani akan gado ne tayi saurin janyewa ta fito a gurguje batayi ko ina ba se d'akinta, taja k'ofan tasa lock. Hak'i take sosai tana jan dogayen nishi.

Tou ma tsaya, guduwan mey takeyi bayan shi da kanshi yazo ya tada ita tayi sallah? Se anan ne events da suka faru jiya suka fara dawo mata, batayi missing detail ko d'aya ba. Bazata iya tuna lokacinda bacci ya d'auketa ba amma ta tuna komai har izuwa lokacinda suka zauna bakin gadonshi yana bubbuga bayanta a hankali.
Murmushi ne ye bayyana a fuskarta. Allah sarki ashe de haka Ya Ahmad yake da tausayi? Ashe yana da ragowan imani. In ba dan shi ba jiya da ta tabbata suma shine k'aramin abinda zatayi. How long has it been? Ta d'au the more take girma the more zata rage having nightmare d'in daren data rasa mahaifinta amma ina. Har yau har gobe sede ba ayi ruwa da daddare ba se flashback d'in ranan yazo mata barin ruwa mey tsawa mey k'arfi.

Har tayi alwala tayi sallah tunanin kalan kulawan da Ahmad ya bata jiya take. Be tsaya anan ba har d'akin shi ya barta ta kwana aciki. Toh shi aina ya kwana? Ina Nanny kuma? K'asa ta sauk'a ta lek'a d'akin Nanny amma ba ita ba alamun ta. Parlour ta lek'a inda take zaton ko wajen Ahmad ya kwana ta tarar da shi mik'e akan 3 seater yana lullub'u acikin bargo. Neman kalan tsanar da take mishi kap tayi amma ta rasa, sema wani kwanta mata a rai da taji yanayi. Tsoro ta cire ta k'arasa parlourn had'e da kiran sunanshi cikin siririyar muryanta. "Ya Ahmad?"
Bata kaiga kiran sunanshi a karo na biyu ba taga ya fito da fuskan shi daga cikin blanket d'in.
"Ina kwana?" ta gaishe shi cike da ladabi.
"Lafiya" ya amsa "mey kikeyi anan?" Ya tambayeta ba yabo ba fallasa.
"Nayi tunanin ko zaka koma d'akinka ne."
"How are you feeling?" Ya tambayeta wanda shima besan lokacinda yayi hakan ba kawai idan ya tuna da kalan tashin hankalin data shiga jiya se yaji yana tausayinta.
"Alhamdulillah much better" ta nisanta "Ya Ahmad?" Ta sake kiran shi. "Uhm?" Ya amsa.
"Thank you soo much for yestarday if not for you da Allah kad'ai yasan halin da nake ciki yanzu thank you sincerely, Allah sak'a da alkhairi." Na sosai shima yaji dad'in godiyan data mishi.
"Ameen you can go back to your room."
"Tou" tace sannan ta juya ta koma d'akinta. Be dad'e ba ya mik'e yabi bayanta. D'akinshi ya shiga ya kwanta. Bacci mey k'arfi ne ya d'auke shi. Ita kuwa Farrah ta kasa komawa bacci data rufe idonta se event d'in jiya yafara flashing mata. Se yanzu ma ta tuna da vest da gajeren wandon da take sanye dashin nan ne fa taje ta sameshi jiya. Dan rikicewa ko hijabi bata tsaya ta sa ba ta fad'a d'akinshi. Tuna hakan da tayi kuma se kunya mey tsanani ya rufeta. Shin menene wannan bak'on yanayin da ta tsinci kanta aciki?

*****
Gari na wayewa Nanny ta kira Mal Isuhu yazo ya d'auketa. D'akin Farrah ta wuce straight tana bud'e k'ofa ta tarar da ita akan gado tana bacci. Wani ajiyan zuciya ta sauk'e ganin Farrah is peacefully okay. "My baby" tayi maganan had'e da shafa fuskan Farrah. Gyara mata kwanciya tayi sannan taja k'ofan ta rufe. D'akin Ahmad ta lek'a next, baccin shima taga yanayi. Mayar mishi da k'ofan tayi ta dawo d'akinta. Wanka tayi ta d'an kimtsa d'akinta. 8:30am ta fita kitchen ta shiga had'a musu breakfast.

Pass 9 Farrah ta tashi ta share d'akinta. Ta sauk'o d'aukan mop suka had'u da Nanny. Da gudu taje tayi hugging nata bayan sun gaisa Nanny ke tambayarta ya tayi jiya da bata nan.
"Nanny Ya Ahmad did the unthinkable" ta sanar da ita. "Kinsan naje d'akinshi ne kawai saboda ba kowa a gidan se shi but I wasn't expecting any help from him sanin halinshi. But then se ya bani mamaki, he was so patient kaman ba shi ba, bakiji hak'urin daya ta bani ba yana soothing d'ina."
"Ahmad d'in?" Nanny ta tambaya cike da mamaki ba don Farrah ce ta fad'a mata da kanta ba da setace k'arya ne. "Ahmad fa kikace?"
"Shi dai kinsan a d'akinshi ma na kwana shi kuma ya kwana a parlour seda asuba bayan daya tadani sallah nace ya koma d'akinshi nima zan koma nawa."
"Ahmad d'in dai?" Har anan Nanny ta kasa yadda da abinda takeji. Ahmad da ba abinda ya tsana sama da sharing bed d'inshi ne wai ya bawa Farrah gadonshi ta kwana? Lallai Farrah tayi sa'a.
"Allah sarki Ahmad Babana" Nanny tayi maganan tana me jin dad'in hakan da yayi. A rayuwa ba abinda take so kaman taga Ahmad yana jan Farrah a jiki, bata son wannan zaman annabi da kafirin da sukeyi "Allah mishi albarka, Allah muku albarka gabad'aya."
"Ameeen Nanny."
"Se a rage mishi rashin kunya daga yau ko?"
"Ai Nanny bana mishi rashin kunya aiki ne de kawai in ya sani bana son yi kuma daga yau nima zan canza."
"Yauwa mamana yi mana setting table ga breakfast na gama."
"Tou dama zanyi mopping d'akina ne."
"Karki damu zan miki yanzu had'a mana table."
Da "tou" ta wuce ta shiga tafiya ko kallon gabanta batayi. Ji kawai tayi ta yi karo da abu wane dutse d'ago kan da zatayi taga Ahmad ne tsaye a kanta. Baya taja da wuri tana murza goshinta inda ta buga a jikinsa. "Good morning Ya Ahmad" ta gaishe shi. Kai zalla ya gyad'a mata sannan yabi gefenta ya wuce.

"Good morning Nanny" yayi maganan yana dosan fridge, ruwa ya ciro ya bud'e ya shiga sha. "Ka tashi lafiya?" Ta amsa fuskanta d'auke da walwala "Lafiya alhamdulillah jiya ruwa kuma ya rik'eki."
"Eh wallahi ya d'awaniyan ka na jiya kuma? Farrah ta ban labari, Allah bada lada ya maka albarka I am honestly so very proud of you." Murmushi kad'an ya saki "Ameen Nanny it was nothing. Breakfast yayi ba?"
"Eh kabani minti biyu yanzu zan fito dashi Farrah ta riga tayi setting table kaje ka zauna."

HayateeyWhere stories live. Discover now