1

701 42 1
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabooks:JamilaUmarjanafty*

*ZAN SADAUKAR DA WANNAN LABARIN NA TSAKA MAI WUYA ZUWA GA KARAMTATTUN MUTANE GUDA BIYU, MASU MUTUMCI DA DATTAKO*
*HAJIYA HABIBA ABUBAKAR IMAM IKIRA(YAYATA) TARE DA*
*AUNTYSIS(MYANTY)*
*YADDA KUKA KARRAMANI A NAN DUNIYA DA KARAMCIN KU, INA MUKU FATAN KUMA ALLAH YA BAKU ALJANNAH SABODA KARAMCIN KU, ALLAH KUMA YA SHIRYA MUKU ZURU'ARKU TARE DA DAIDAITAN DUKA LAMURAN KU NAGODE MUKU SOSAI*

*GARGAD'I*

*LABARIN TSAKA MAI WUYA HAKKIN MALLAKA NA JAMILA UMAR JANAFTY NE,  A GUJI SARRAFASHI TA HANYAR TAB'A SHI KO SAUYA SHI ZUWA WANI MANUFAR DA BANI DA MASANIYA, YIN HAKAN KAMAR SAB'A MA DOKAR HAKKIN MALLAKATA NE. A KIYAYE*

*MANUNIYA*

*LABARIN TSAKA MAI WUYA KIRRARREN LABARINA NE, DUK ABUNDA AKA CI KARO DA SHI YAYI KAMANCECENIYA NA SUNA, HALLAYA, GARI KO DABI'A TO A YI HAKURI AN SANE DOMIN ARASHIN LABARIN, BA DOMIN NUNIYA KO TOZARCI GA WANI KO WATA BA*
*NA GODE*

*GODIYA GA*

*KAWATA SURAYYA DEE*
*NA GODE MIKI, UBANGIJI YA YARDA DA KE, SANYIN IDANIYA NA KE MIKI FATA TARE ZAMAN LAFIYA MAI DOREWA A RAYUWARKI TA HAR ABADA.*

*TUKWAICIN LABARIN TSAKA MAI WUYA ZUWA GA*

*AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINA)*
*KHADIJA SALISU YUSUF(UMMINA)*
*HAFSAT MUSTAPHA(SAHIBATUNA)*
*ZAINAB MUHAMMAD CHUBADO(CHUBA)*
*MARYAM JUMARE*
*HALIMA YUSUF GWARZO(BESTY)*
*FIRDAUSI FEEDHOM(MY MENTOR)*
*NUSAIBA IBRAHIM USMAN(ALHERI RADIO ZARIA)*

*FATAN ALHERI GA MARUBUTA*

*ANTY SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI*
*SANAZ DEEYAN*
*MARYAM AMINU(KITTY)*
*NANA HALEEMA(MASOYIYATA)*
*AISHA ADAM(AYUSHERCOOL)*
*AYSHER DANSABO LEMU*
*HALIMA HZ(RIVAL)*
*HASINA AUTAR MANYA*
*NAZIFA SABO NASHE*
*NI'IMA SULAIMAN(NIMCY)*
*RAMLAT ABDULRAHAMAN MANGA(MAI DAMBU)*
*FARIDA ABDULLAHI(FEDDYNBASH)*
*SISTER LUBNA SUFYAN*

*FATAN ALHERI MADALLAH DA KU NA GODE*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*01*

*SHIMFID'A*

*KADUNA_Zaria*
_Samaru_
Dogon gida.

Tun wayewar garin ranar Asabar nake cikin Fargaba da tsoro, Wani irin sanyin jiki da faduwar gaba. gabad'aya gabbaina sunyi sanyi, gabana kuma bai daina tsananta fadi ba. Duk lokacin da na tuna halin tsaka mai wuyar da nake ciki.
Fargaba na da tsoro sun karu ne tunda naga sha biyu na rana ta gota, sai na kasa zama duk yadda naso natsuwa ya samu muhalli a jikina da zuciyata na kasa.
Sai faman Safa da marwa nake yi a tsakiyar Dakin Maman Boy, tunda a dakinta na shirya cikin Riga da zani na Atamfata English mai kalan Duhuwa. Sabuwa ce domin duka duka bai fi sau uku na taba sakata ba, kuma sau d'aya na tab'a wanketa.
Tana daga cikin kayan aure na da Abubukar, ban yi kwalliya ba saboda ba na cikin wannan sukunin, Daga ni sai kanwata Habiba ne a Dakin da Safe itama d'azu shigowar Ramatu ta jata sun fita tare.
Dakin mu nake son na leka ammh kuma Kafafuwana sun yi sanyin da sun kasa daukata zuwa Tsakar gidan namu.
Tsorona  na raguwa ne in na tuna da yau Amma ta tashi jikinta da Sauki har tayi wanka ta saka kayanta masu kyau, tunda yan gidan su marigayi Alhaji Mammandi limancin kona sun zo, gidan da aka haifi mahaifin Babanmu kenan.
Duk da ina da tabbacin suma din ba domin taya Amma murna suka zo ba, sun zo ganin yadda za'a kare ne kamar yadda Hasashen su ya saba gaya musu a kaina. Ina jin Hayaniyar su Adda Fati a tsakar gida duk da ba wani taro zasu yi ba, ammh dai suna Dafa abinci saboda makota da yan'uwan da za su zo ko ba da yawa ba.
Kamar ma sun gama ne saboda naji ana mganan matan gidan duk su kawo kwanukan su, Hassana ta zo ta Dauki kwanon Maman boy. Sanda ta shigo sai da ta ce min"Sannu Adda HASIYA.."
Sai da ta fice ne na dawo hayyacina domin nayi zurfin acikin Tunanin da nake yi, kowani Dakika na Bugawar agogon dake kafe a dakin Maman Boy tare ya ke da Bugawar zuciyata.
Gif gif! Gabadaya a tsorace nake na kasa kuma addu'a a fili nake fad'in"Ya Allah! Ya Allah!."
Daganan sai bakina ya yi nauyin da nake gaza fad'in komai.
To me zan ce?
Ko me zan roka?
In dai rayuwar da nake ciki ita ake Kira TSAKA MAI WUYA to zan iya cewa ni Hasiya tun haihuwata nake cikin Rayuwar Tsaka mai wuya.
A kan idanuwana Karfe d'aya ta Buga, daidai da wani irin fad'uwa da gabana ya yi Ras!.
Kafafuwana suka fara rawa, Tsoro nake ji ina ji ajikina kamar abubuwan dake faruwa a kaina ba Canfi ba ne, sannan ba Kuskure ba ne. Da gaske ni ina da Kashin da Rab'ata kada'i kan iya Sanadin Ruguza rayuwaka da Dama.
Hannanuna guda d'aya na saka na Dafe kirjina da nake jin yana tasowa kamar zuciyata zata fito. Wlh ina jin Tsoro, tsoro nake ji tsoron da ya bayyana har a cikin jikina zuwa saman Fuskata.
Ramatu ce ta fad'o dakin da gudunta ko Nauyin cikin jikinta da ya tsufa bata ji, Gud'a ta daidaici kunnina na Dama ta Rangad'amin da ya yi sanadiyar da naji ni kamar na suma ne, wani irin Shuuu! Naji na wucewa na cikin kunnuwana, ban dawo cikin Hayyacina ba naji muryanta cikin Zak'i daman Ramatu akwai zak'in murya tana Fadin"Ta zama..ta zama matar Salisu"
Kin zama..kin zama Amaryan Salisu. An daura auran ki yanzu Hasiya, Salihi ya shigo da gudu yana fad'a'"
Kalamanta sun yi daidai da lokacin da sanyayyin kafafuwana su ka gazamin sai na bi umarninsu wajen zubewa a kasan ledan Dakin Maman Boy da karfi, ina haki kamar wacce tayi Gudun Tsere.
Hawaye na ji sun cika kwarmin idanuwana, na dago ina kallon Ramatu da ke kallona ina jin hayaniyar fad'in an daura aure daga matan dake tsakar gidanmu, Ramatu nake kallo kamar ban ji daidai ba nace"An daura? Da gaske Ramatu an Daura aure na da Salisu?
Na fad'a cikin Sigar kokwanto da Tambaya.
Mirmishi ta sakarmin mai cike da kaunar da take yi min tun ranar da ta fara ganina. Gefena ta zauna itama ko Cikin jikinta bai damunta, cikin son kwantar min da Hankali ta Dafa Kafad'ata tana fad'in"Da gaske an Daura auran ki da Salisu. Kuma in sha Allahu wannan auren mutuwa ce zata rabashi Hasiya"
Sai ta d'an dakata tana lura da kuma nazarina ganin na Runtse idanuwana hawaye suka zubomin sharr! Kamar an Bud'e famfo.
Da irin baiwar da Allah ya bata na Tattausan lafazi ta kira sunana cikin Zakin muryanta "Hasiya..Hasiya D'ako ki kalleni don Allah"
A raunane na D'ago ina kallonta kuka na son kwacemin. Da sauri ta saka hannunta guda d'aya tana sharemin Hawaye da suka bata Farar Fuskata.
Cikin irin kalaman ta Tausasawa ta cigaba da Fad'in"To kuma me meye na kuka? In sha Allahu wannan auren sai ya shafe mganganun mutane a kanki Hasiya sai yasa sun yi nadaman kiran ki da mabambamta sunaye"
Kalamanta suka sake Raunana ni. Cikin karfin Hali na Bud'e bakina nace"Ramatu anya gaskiya kike fad'amin? Ta ina bak'in bakin Fentin da tun haihuwata yake bibiyata sannan kuma kice zai gogu a lokaci d'aya?
Na fara girgiza kaina Lokaci d'aya Hawaye suna zubomin nace"Ki na dai Fad'amin hakane saboda naji Dad'i kuma saboda kada na damu"
Na karishe fad'a cikin gunjin kukan dake fitowa daga kasan raina.
Gabadaya na fad'a jikin Ramatu na saki kuka na, sai naji cikin jikinta ya Tokare ni,Sai kuma naji sanyi ya mamayeni na Dora hannuna saman cikin ina Fad'in"Ko ban yi aure ba..ko ban haihu ba. Na tabbata yar da zaki haifa ko d'a zai kira ni Mama watarana Ramatu"
Duk dauriyan Ramatu sai da naji Muryanta na rawa tana fad'in"In sha Allahu ki Dauka duka ya'yan da zan Haifa naki ne Hasiya"
Ta fad'a tana rumgumeni gabadaya sai kuma muka had'e kai muna ta kuka, kukan tuna rayuwar mu tunda Fari Lokacin da Ubangiji ya hallicemu. Kai bawa ba'a bakin komai ya ke ba, kuma shi mutum tun daga Haihuwarshi a mutuwarsa yana cikin Kalubalen Rayuwa ne da Jarabawa.
Sai da muka yi kukan mu muka gaji sannan muka yi shuru shima Maman Boy ne ta d'ago labule ta ganmu muna ta Rafzan kuka. Baki ta rike kafin tace"To kuma miye na kuka? Aure dai ai an Daura shi sai dai Fatan Allah ya fidda auren ku a bakin yan bani na iya"
Tana gama fad'in haka ta saki Labulan D'akin ta juya, kalamanta yasa muka saki juna tana sharemin hawaye nima ina share mata Fad'i take yi"ki kwantar da Hankalin ki in sha Allahu babu abunda zai faru"
Kaina na Dagamata ba domin na yarda da ba abunda zai faru d'in ba.
Ko sauran Lokutan baya da abubuwan ke faruwa ba sani nake yi ba kawai zuwa suke yi ba zato ba Tsammani.
Hira Ramatu ta cigaba da yi min saboda na warware, sai na bi yunkurinta ban gwale mata, ina biye mata cikin Hirar nata.
Habiba ce ta kawomana Jalop din shinkafar da suka Dafa, da ruwa tace in ji Adda Fati har zata fice na daga ido ina kallonta cikin Dashewar murya nace"Habiba Amma fa?
Ta juyo tana fad'in"Amma na lafiya,wani abu za'a karb'o miki a abu a wajenta ne?
Sai na kasa mgana to me zan ce? Ganinta kawai nake son yi ,ban samu damar mgana ba Ramatu tace"Kin ji Habiba jeki abun ki"
Sai ta kad'a kai tayi ficewarta.
Duk yadda na so na nuna komai ba komai ba ne na kasa.
A saman fuskata zaka hango tsoro da wani irin Fargaba. Har sanda Adda Fati ta leko ta kira Ramatu kafin fitarta sai da takara jadaddamin kada na damu babu abunda zai faru.
Kai kawai na Daga mata, sanin da nayi komai zan fad'a zata ga kamar na raina kokarinta a kaina ne. Kasa zaman Dakin nayi, hankalina na wajen Amma yasa na mike dakyar kafafuwana sun yi tsami sosai.
Abincin ma da aka kawomana idon Ramatu yasa na ci kad'an ammh a kirji na ya tsaya tunda ga shi nan ina jinsa, Kirjina suya yake yi min. Daman tun a kwanaki nan nake fama da ciwon kirji da baya, nasan Ulcer d'ina ce ta tashi ammh halin da nake ciki yasa ban tsaya bi ta kanta ba.
Jan kafa take yi saboda ta yi min Tsami ga wani sanyi da jikina ya yi a haka na fito daga Dakin Maman Boy.
Gidanmu irin Dogon gida ne ba shi da Fili ko kad'an a tsuke yake ga kuma Jerin gwanon Dakuna reras fin goma shiyasa in dai ka shigo anguwan Samaru kace a kawo ka DOGON GIDA ko yaro ko Babba zai kawo ka har Kofar Gidanmu.
Ko sha'ani ake yi a kofar gida ake yi girki saboda ba fili ko a shiga makota ayi, Matan ne aure reras Goma sha uku ne a gidan Amma ce ta sha Hud'u da bata da miji. Kuma kowacce na da Tarin ya'ya kamar tsaki shiyasa kowani babban gidan albarka bayan yaran gidan ma har da na makota.
Gida kuma gidan Haya ne, shiyasa bakomai ba ne zaka ganshi cikin Tsari a ire iren gidajen da rayuwa ta kan jeho ire iren mu.
Koda na fito duk matan gidan suna waje ana ta cin shinkafa ana Hira, Yaran kuma suna ta guje gujen su, suna ta Hayaniya ni fa ba domin su Addaa fati ba, ba taro na so ayi ba, Tunda nasan da yawansu taron su ci abinci ne su koma suna Dariya da Kaddarata.
Ko Amma sai da tace bata son Taron nan Adda Fati ta roketa tace adai yi ko yaya ne yafi ace ba'ayi gayya ba.
Har ga Allah ban so ma wata ta ganni ba naso ne na sulale na shige Dakin Amma ammh ina sai da Maman Salihu ta ganni ta ko Rangad'a gud'a tana Fad'in" Amarsu ta ango"
Sai kallo ya koma kaina, nan fa suka taru a kaina suna ta min Shegentan ka da suka saba,ni dai ina kauce musu saboda hayaniyar tayi min yawa tana  kuma kara tafiya da Fad'uwar gabana.
Dakyar na yakice su na Fad'a Dakin Amma tana zaune gefen katifar da waje wajen zamanta shekaru masu yawa, bayanta an kara mata Filo guda Biyu saboda ta zauna Dakyau.
Gefenta kuma Wasu abokan wasa suke wajen Babanmu. ni sauran ma ban tsaya kallon su ba kafafuwana ke Hard'ewa kamar zan fadi ganin ina shigowa kallo ya Dawo kaina.
Suma din kamar matan gidan namu Gud'a suka saki suna kirana da Amarya sunan da in sun kirani da shi nake jin wani rauni ya lullubeni a shekaru biyun da suka gabata an kirani da suna Amarya, ammh bai Dore ba na tashi daga Amarya na koma Bazawara da wasu jerin sunayen da bazan iya fad'an su ba.
Ni dai ban tsaya biye musu ba, samun kaina nayi da karisawa in da Amma take zaune tunda na shigo ta Dago tana kallona da Mirmishin da ya kasa bace mata a saman fuskarta. Bansan na zube a gabanta ba sai da naji kafafuna sun gamu da siminti har yar kara sai da suka ba da Kas!, Cikin Fara'ar da ta boye tsoron dake kan Fuskata nace'"AMMA.."

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now