K'arshen littafi na d'aya.

233 18 0
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*FATAN ALHERI DA SAKON GODIYA ZUWA GARE KU*

*AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH)*
*MARYAM JUMARE*
*NANA HALIMA(MASOYIYA)*
*HAFSAH HAFNAN(SAHIBATU)*

_*Nagode muku bisa yadda kuka yi ta Hidima da wannan littafin, HasiyarAssadiq tace ta gani kuma ta yaba, Innani kuma tace dukkan ku Allah ya yi muku albarka Amin*_

*20*

Sai bayan Fitar Tahir yaji wani mugun zazzabi ya kara rufeshi.
Nan da nan ya fara rawan Sanyi Hakoransa na had'uwa waje d'aya.
Kansa kuwa kamar zai Tsage gida Biyu Tsabagegen yadda ya ke sara masa, jijiyon kansa sun mike gabadaya Rad'au a saman kansa saboda Halin da ya ke ciki.
Idanuwansa biyu Tahir ya dawo da magangunan da ya siyo masa.
ba domi Tahir ya taimaka ya tada shi zaune ba ji ya yi kamar bazai iya ma tashi ya zauna da kansa ba.

Tea mai kauri Tahir ya had'a masa yace bazai sha ba , shi kuma ya lallabeshi kan ya samu ya sha saboda ya samu sha mgani.
Dalilin haka yasa ya sha kad'an ammh ji ya yi ba dad'i kamar ya na shan mad'aci saboda bakinsa da ya zama wani takaf kamar wanda ya yi shekaru cikin jinya.
Tahir ya ballo masa magungunan Paracetamol ne sai maganin maleria d'in nan mai warin kudin cizo. Shi ba ya son magani ya fi shiri da Allura ammh Bala'in Tahir yasa sai da ya sha magungunan gabadaya sannan ya kyalesa ya koma ya kwanta Lokaci d'aya ya na kara taba goshinsa jin har lokacin da zafi.
Ya dad'e barci bai daukesa ba ya na jin Tahir bi ni bini sai ya lekosa ya na masa sannu tun ya na daga masa kai in yajisa har wani wahallalen barci ya Daukesa mai cike da Tararradi da zullumi.
Bai san haka ya yi barci sosai ba sai da ya farka cikin ikon Allah yaji zazzabin jikinsa ya sauka sai dai sarawan kan kad'an. lokacin da ya yunkura ya mike sai yaji ba jirin Tunda ga shi har ya iya mikewa da kansa batare da taimakon kowa ba.
Tahir ya kallah da ya kwanta a kasa wayarsa na saman cikinsa kila wajen Dannan wayar ne barci ya Daukesa bai sani ba.

Yasan ba shi da laulayin yawan ciwo sai ya jima bai yi ciwo ba, in ko ya yi Ciwo sai dai ko ciwon kai in ya yi Tsanani ne zazzabi shi Allah ya Tsare shi da ciwukan zamani irin su Ulcer ko Typiod.
Jin ya samu karfin jiki yasa ya dibi Ruwa a buta bayan ya Dauki karamar wayarsa ya kunna Fitila.
Ruwa ya zuba a karamar buta sannan ya yi addu'a ya bude kofa ya fita daidai lokacin da karfe uku na dare ta cika a wayarsa. Ba shi da tsoro daman Tahir ne ke tsoron Fitan Dare ba Sadiq ba shi da ko a gida ko karfe nawa ne zai iya fitowa Haraban gidan su in yaji wani motsi to anan ma shi ke raka Tahir in lalura ya tashe shi cikin Dare.
Kai Tsaye makewayi ya haska ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito a tsugunna a kan damdamali ya yi alwala sannan ya koma Daki har Lokacin Tahir na ta barcin bai ma san ya tashi ba.
Darduma ya shimfida bayan ya cire kayan jikinsa ya saka wata farar Jallabiya ta mutanen Saudiya. Yasan akwai sallar mangariba da isha'i da ke kansa ba shi su ya fara yi kafin ya mike ya yi salla raka'a Biyu ya jima acikin Sujjuda ya na ta addu'a sannan ya Dago ya yi tahiya ya sallame nan ma d'in ya jima ya na kirga da hannunsa kafin ya daga hannunsa sama ya na addu'a na tsawon wani lokaci sannan ya shafa.
Bai koma kan katifar ba sai ya kishigid'a saman darduma ya na jin Kwakwalwarsa ta na shiga wasu Tunane Tunanen da a dazu kwata kwata ta tsaya cak. Iya hangen nasa ya gama Hango masa aikata Rokon Amma daidai ya ke da rasa goyon bayan wasu daga cikin Ahalinsa.
In yace kuma ya shawarce su ya bata komai domin ba bu wanda zai rama masa baya acikin wannan Halin da ya ke ciki.
A cikin zuciyarsa ya cika da Tausayinsu kuma ya na so ya taimaka musu ammh bukatar Amma ta yi tsauri ta kuma saka masa wani irin Dabaibayi ne mai wuyan fita. Ga shi ya riga ya furta tun farko shi maraya ne babu yadda za'ayi kuma daga baya ya sauya mgana.
Tunanin mafita kwakwalwarsa ta Zurfafa aciki ammh sai dai har barci ya kwashe shi bai samu wata mafita mai kyau ba duk Mafitan da ya hango sai yaga bazata bulle da shi ba.
Acikin barcin nan da ya koma sai ya yi mafarki ko nace kamar Allah ne ya nuna masa sakamakon zabin da ya mika garesa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 12 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now