5

248 24 3
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.

*05*

*GUSAU_ZAMFARA.*
_Area:Tudun wada_
*Lahadi, 10:40am*

"Wai wani shegen ne ke min burutun a shashe na da Safiyar Allah nan?
Ta fad'a cikin kufula da takaicin yadda aka maida ita banza tana ta mgana ita kad'ai.
Kokarin mikewa take daga zaunen da take lokaci d'aya tana Laluban sandar ta, tana cigaba da fad'in"Ko wani d'an jakar uba ne ya bari na fito mu ga juna yau sai na Deb'e masa albarka"
Ta samu mikewa kan kafafunta, ta kuma samu nasaran ganin Sandarta ta karfe a gefenta sai dai kamar akwai sauran rina akaba, tunda sai faman lalube take yi kamar ganinta na da rauni.
Garin lalubenta ne hannunta ya kai kan wani bakin gilashi ta dauko shi tana fad'in'"kaji rashin tabbas na Abun nasara yanzu gilashi na fuskata na nemesa na rasa. Mtswww aikin banza da wofi"
Bum! Taji kamar an fad'o dakin nata a rashin sukuni a zafafe ta saka gilashin nata cikin Masifarta da tun tana matashiyarta ya zame jiki har tsufanta tace"Nace wai waye zai zo ya Dameni da burumtu ne? To ko waye in bai yi mgana ba Allah ya tsinee..."
 
"Innani ni ce".

A kafad'a da wata sanyayyiyar murya mai cike da yarinta da kuruciya. Wacce aka kira da Innani ta d'ago kanta a masifan ce tana yamutsa Tace"Ke ce wa? Baki da suna ne? Ina na ke iya gane muryoyin yaran gidan Sulaimanu, ku rika wani make murya kamar wasu ya'yan gyare"
Ta fad'a lokaci d'aya ta na kara gyara zaman gilashin da ke fuskarta sosai ya cika mata fuska kir kuma ta sauke ganinta kan yar yarinyar dake gabanta sanye da Hijabi mai ruwan kasa. Kanta na kasa tana wasa da yatsun hannunta.

"Sultana ce. Sultana ce Innani"

Baki Innani ta washe kafin tace"Au ki ce Sulsana ce ta wajen Salamatu ko nace Matar MAGAJIN GIDA. uwargida Sarautar mata a gidan Abubakar Saddiqu alkawarin  Allah sai ya cika da yardan Allah, ya ki nan yar nan taho ki zauna kusa da ni"
Ta fad'a tana ya fito ta da Hannu. Jikinta kamar ba karfi ko na ce wacce ta tashi matsananciyar jinya ta karisa gefen Innani ta zauna. Innani ta gyara zama tana fad'in"Ke kam ki rika kama jikin ki mana Sulsana. Ayi mace kamar wahainiya saboda rashin kuzari"
Ita dai kanzil bata kara ce mata ba, kanta na kasa tana wasa da yatsun hannayentaa. Innani ta kara kallonta cikin nazarinta kafin tace"Daman kece kika zo kina min bare bare a sasana? Tsiyana da ke wauta ko rashin wayau ne ma zan ce ni Dije? Ayi yarinya sai shegen tsoron mutane. Allah dai ya yaye miki kin ji ko"
Wannan karon ne ta murmusa ammah ba tayi mgana ba, ganin haka yasa Innani ta washe wawulan bakinta da babu Hakora ko d'aya duka sun gama barewa, Daman na Roba take makalawa in zata ci abinci abubuwa masu tauri kuwa sai dai ta saka wuka ta yi gutsi gutsi da shi, Kwad'ayi ne da Innani komai na Duniya ba bu abunda bata ci. Tace da wuya ta kasheta gwara dad'i ya kasheta.

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V

Cikin Dariyanta tace"ina lafiyar ita uwar taki? In ji dai lafiyanta lau? Ina shi Baban naku? Tun asuba da ya leko muka gaisa ban kara ganinsa ba."
Muryanta a sanyaye tace"Umma tana lafiya. ABBA kuma yana bangaransa shi da Mama"
Nan da nan Annurin fuskar Inanni ya Dauke ta wani Dauke kai kafin tace"Uhm ko da naji."
Daganan tayi Dif tana faman girgiza sadan dake gefenta. Sultana sai satan kallonta ta ke yi tana danne mirmishinta. Sai jin mangari ta yi a kai lokaci d'aya Innani tace"Munahika yi dariyar taki mana a sarari yarinya sai bakar gulma kamar haihuwar Ssuwaiba.
Da sauri ta kalleta cikin mamaki Lokaci daya tana dafe kanta in da Inanni ta mangareta. Innani ta yayyako mata cikin masifa tace"Miye kuma kike kallona? Ko na fad'a a bakin yan baka ne ko ke ma kin koyi halin ya'yan Suwaiba ne  ban sani ba?Allah to ya sauwake kin cuci Salamatu da Sulaimanu domin ba haka suka tarbiyantar dake ba"
Ko gajiya da mgana Innani ba tayi, haka Sultana ke fad'i a cikin ranta.
Mirmishi ta yi kafin tace"Innani.."
Innani ta kalleta batare da tayi mgana ba, ganin Sultana taki mgana sai kuma wasa da gefen hijabinta take yi yasa Innani ta yi tsaki kafin tace"Nace miye ne kika tasani kina faman kiran sunana?
Shuru Sultana taki mgana kanta na kasa sai wasa da gefen hijabinta ta ke yi, Innani tayi sakate kafin ta juya cikin jin haushi goronta da ke cikin wani karamin kwano ta jaho,ta fara yayyankashi a saman tafin hannunta. Chan kasa kasa taji Sultana ta kara kiran sunanta"Innani.."

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now