13

177 35 5
                                    

*TSAKA MAI WUYA..!*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj

Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.

Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.

Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260..  Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus

*13*

Duk lallashin da suke yi min Ina jin su ammh kuma ba na daukan duka magangansu, domin nasan irin kalaman na su na kuma jima ina jin irin su, ammh har yau har gobe babu al'amarin da ya sauya.
Gayamin suke na daina damuwa komai da ya faru daga Allah ne.
Ni ban isa na tsara kaddaran mutane a Hannuna ba, to a irin yanayin da na ke ciki na gaji da jin irin kalamansu Tunda ba za su taba sama mun mafita ba.
Duk maganganun da suke yi ban bude baki na nace Tak ba. Kuka kawai na ke yi na had'a kai da gwiwa ina rafzan kuka. Ko ruwa ban bari ya shiga bakina ba duk ko da magiyan da suke yi min da na ci wani abu ko zan samu karfin jikina.
Haba rayuwar nan duk ta isheni in har mganar mutane ba gaskiya ba ne meyasa abubuwa suke faruwa da ni daki daki haka?
Farko Babanmu na biyu an ce ciwon Amma ni ce Sanadinsa halin da muke ciki duka Laifin na kaina, Sabo da ni Dangin mahaifin mu suka Gujemu kowama ya gujemu Abubakar ya aureni ya sakeni Salisu ma haka. Duk kuma ace haka kurum abubuwa ke faruwa dani kamar ni kad'ai ce Y'a a wannan Duniyan?
Tabbas akwai kamshin gaskiya. na fara Tunanin tunda na zama Annoba ga al'umma to banga amfanin Rayuwata ba ko na Mutu, ko kuma na yi nesa da Rayuwar da ni ke ciki. Ina ji Adda Rukayya ta kira Adda Fati sun yi mgana sannan an ba ma Amma ta na ta bata Hakuri.
Adda Fati ta dafani ta na Fad'in"Rukayya na gaishe ki. Tace a yi miki sannu gobe kila ta shigo ita da Habiba."
Ban so na yi mgana ba Saboda ba na jin yin mgana da kowa ammh a wannan gabar ina bukatar wani karin bayani, idanuwana jajir na dago ina kallon Adda Fati fuskata duk ta kumbura saboda kuka da duka cikin Dashewar murya nace"Adda Fati ban gane wani abu ba? Me yasa Adda Rukayya ta damu saboda dangin Mijinta sun Tozartani."
Adda Fati tace"Kada ki manta Rukayya jininki ne Hasiya. Duk in da aka kai aka kawo ba ta da kamarki kamar yadda ke ma baki da kamarta."
Na yi mirmishi ina jin yadda bakina ya Bushe da makogwaro na. Ban ce komai ba na maida kaina cikin gwiwoyina na suke.

Inna Talatu ne tace"Ita Halin Rukayya Wauta ne da rashiin wayau. Ammh ba ka budema miji sirrin yan'uwanka ka rika bata su a idon sa saboda gudun watarana ga shi yanzu sun yi abu kuma ya zo ya na Damunta."
Sai alokacin Amma ta saka baki jikin Raunin zuciya da na jiki tace"Kuma shi wannan dan'uwa da ka ke Tunanin wani ya fisa. To duk duniya shi ne naka akwai kuma bangaren da Dole naka ne zai iya kare maka shi. Baren bazai iya ba. Ina Fatan wannan abun ya yi sanadin dawo da Rukayya cikin Hayyacinta."
Adda Fati ta amsa da Ameen kafin tace"Kuma fa Amma ita zata iya yima Hasiya. ammh in wani ya ci zarafinta sai abun ya fi yi mata zafi kamar yadda ya faru. Wani kuma Tozarcin da suka yi har da zugan Kanwar Abubakar din nan tare da maganganun dangin mu muma."
Adda Fati ta sauke ajiyar rai kafin ta cigaba da fad'in"Tunda da bakinsu suke fad'in ga abunda suke fad'i a kan Hasiya. Har suna fad'in suma Dalilin haka suka gujemu, Kuma da gaske ne sun gujemu ba mai neman mu ko sha'aninsu wani Lokacin bama sani suna yin shi. Yanzu Baaba ta lagos sai ta zo garin nan sau biyar dakyar zata zo gidan sau d'aya to wai har gwara ita akan su Baba Tanko shi Baba Jibril karshe da shi da iyalansa ma ba su san inda muke Rayuwa ba. Sai Baba Saminu shi kuma daman tsegumi ke kawosa ya zo ya fad'i mganganu ya kara gaba gabadyansu ba mai Mu'amala mai kyau damu."
Amma ta jinjina kai kwarmin idanuwanta sun cika da ruwa cikin wani yanayi tace"Uhm. Ni kaina sun ba ni mamaki kuma lokacin da Alhaji ke Raye wlh ya yi musu komai ya samu na yan'uwan shi ne da iyalansa, ammh yanzu in da zai dawo Duniya yaga Halin da suka barmu a ciki na Tabbata zai yi bakinciki mai yawa."
Inna Talatu tace"Ai Allah ne ya kawo mu zamanin Zumuncin zamani. Daga kai sai kauri, in kana da shi ayi da kai in baka da shi kuma kai da banza duk Daya."
Amma na sharan hawaye da Gefen zaninta Lokaci daya ta na fad'in"Akwai Allah. Watarana sai Labari komai zai zo ya wuce Rayuwa zata fita daga cikin Tsaka mai wuya, komai kuma zai yi daidai in sha Allahu."

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now