15

177 22 1
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj

*15*

Cikin takun natsuwarsa ya karisa shigowa cikin D'akin.
Yadda muka zuba masa ido ne yasa ya da'n dukar da kansa ya na fad'in"Sannun ku. Ya mai jikin?
Sai suka amsa gabadaya da sauki kafin su shiga gaishe shi ya amsa cikin sakewa Adda da Inna talatu ne suka fara masa godiya.
Kansa na kasa yace"Bakomai.."
Ni ya kallah nima daidai lokacin na Dago ina kallonsa da Sauri nace"Uhm wannan yayata ce Adda Fati. Sauran yan gidanmu ce wannan kuma kawata ce."
Na fad'a ina nuna Masa Ramatu kallonta ya yi lokaci d'aya ya na fadin"Sannun ku zuwa."
Suka amsa masa sai dakin ya dauki Shuru Adda Fati sai ta katse shurun da Fad'in"A nan garin ka ke?
Kai tsaye ya kalleta kafin yace"A'a."
Daga haka bai kara cewa komai ba.
Inna talatu tace"Angode sosai Allah ya saka maka da alheri."
Bai amsa ba kansa na kasa sai dai ya na ta faman mirmishi.
Karisawa ya yi ya duba Amma na d'an lokaci kafin yace min zai tafi.
Adda ta fara jero masa addu'o'i ita da Inna Talatu.
Baya amsawa sai dai yace bakomai kawai ammh da Inna Talatu tace"Allah ya jikan magabata. In iyayenka na raye Allah yasa su gama lafiya. In kuma ba sa raye Allah ya ba su Aljannah."
Ya na gabda zai fita ya juyo cikin mirmishi sannan ya amsa da"Ameen Ameen Nagode."
Daga haka ya fice Ramatu ta zungureni ta na fad'in"Ki raka shi mana"
Kallonta na yi sai ta gyad'a min kai daidai Lokacin da Adda ke kara fad'in"Hasiya bi shi mana. Ki kara masa godiya."
Maman boy da gulma tace"Wlh kuma daga gani asibitin akwai cacan kudi. Tunda ba ta gwamnati ba ne"
Jin haka yasa na bisa da Sauri har ya kai Haraban asibitin ya na tafiya. Sai na kasa kiran sunansa illah sauri sauri da na rika yi har na cimmasa.
Tsayawa ya yi ya na kallona kafin yace" Me yasa ki ka fito?
Kaina na kasa nace"Na zo ne na kara maka godiya."
Mirmishi ya yi kafin yace"Godiyar nan ta isa hakanan HASIYA.."

Kallonsa na yi cikin mamakin kiran sunana da ya yi sai ya ware min ido ya na fad'in"Ko ba sunan ki kenan ba?
Kai na gyad'a masa cikin kunya alamun hakane cikin yar mamaki ya kalleni ya na fad'in"Hasiya sunane? Sunan ba Asiya ba ne?
Kai na girgiza masa kafin nace"Hasiya ne sunan."
Shima cikin girgizamin kai yace"To ko dai sunan Fulani ne?
Kallonsa na yi kai tsaye kamar yadda ya ke kallona. Ya ga mahaifiyarmu da zanen Fulani a gefen bakinta, Da kuma gefe da gefen fuskarta.
Sannan yaga Adda Fati da nace yayata ce itama sai yaga yanayinta kamar na Fulani ko buzaye so ya ke ya tabbatar.
Na rasa me zan ce masa ne yasa nace"Amma ce bafullatana. Baba kuma bazazzagi ne, Sunan Hasiya kuma kanwar Baba ce da ta rasu, sai ya maida min sunanta."
Kai tsaye yace"Kenan ki na jin Fullanci.?
Kai Tsaye nace"ba na ji fa sai abunda ba'a rasa ba."
Mirmishi ya yi kafin yace"Na sha kina ji ne nace ki koyamin. ni ban iya kowani yare ba."
Baki na bude kafin nace"Wlh ni ma ban iya ba."
Yadda na yi saurin rantsewa yasa ya yi mirmishi kafin yace"Ban ce ki rantse ba. Yanzu ammh gida zaki koma ki yi wanka ki huta ko?
Ni ban yi wannan Tunanin ba sai da ya fad'a sai na kara bin kaina da kallo yarkace yarkace kamar yar gudun Hijira.
Sai naji kunya na dukar da kaina ina wasa da gefen zanin Amma da na yi Lullubi da shi.
Shi ko bai damu ba kai tsaye yace"Gaskiya ya kamata ki je gida ki Huta."
Da toh na amsa shi har mun yi sallama akan gobe zai dawo ya kara Duba Amma da jiki. Na juya zan koma cikin asibitin sai ya kawai naji muryansa cikin kaushi ya kira sunana.

"Hasiya.."

Da sauri na juyo ina fad'in"Na'am.."
Ya na daga in da ya ke yace"Ki kwantar da Hankali zata warke kin ji ko?
Sai na gyada masa kai. Mirmishi ya yi ya juya ya fara tafiya sai ga shi na Tsaya har sai da ya bace ma ganina.
Mirmishi na yi acikin raina nace"Daman ma su suna Abubakar suna da kirki da jin kai."
Cikin asibitin na koma na iske duk sun fito waje Adda Fati ne ke tare da Amma aciki sai na karisa kusa da Ramatu na zauna muka kara gaisawa.
Nura na tambaya tace min da Safen nan ya wuce na gyada kai ina masa Fatan isa lafiya.
Noor ta ke ba ma Nono sai da ta gama na karbeta ina yi mata wasa. kallona ta yi kafin tace"Ya jikin ki ke ma?
Kai tsaye nace"Ni ai na warware."
Da sauri tace"Sai kumburin Fusakarki bai sabe ba."
A hankali nace"Zai washe shima."
Ramatu tace"Ki ci abinci ga shi nan na Fito miki da shi."
Na amsa mata da toh.
Tazo da filet da cokali sai na Dibi abincin naci Faten wake ne da kifi kadan ma naci saboda cikina ba ya min dad'i.
Ramatu tace"Yakamata ki je gida ki yi wanka ki sauya kayan jikin ki."
Kai Tsaye nace"Shima haka ya ce."
Ramatu tace"Shi wa?
Cikin sigar mamaki. Mirmishi na yi kafin nace

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now