2

265 21 1
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabooks:JamilaUmarjanafty*

*GAISUWA BAN GIRMA ZUWA GA IYAYEN D'AKINA.*

*HAJIYA HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*HALIMA DALHA SHEHU(MAMA)*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*ANTY FIRDAUSI KABIR*
*ANTY FADILA KABIR*

*ALHERIN ALLAH YA LULLUB'E RAYUWARKU GABADAYA AMIN*

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418

*02*

Dakyar mutanen da ke zagaye damu suka samu nasaran raba hannayen Sahura da wuyana.
Ammh kafin su samu nasaran raba hannayen nata da Wuyana na jigata, domin shaka ne ta yi min da niyar da ke zuciyarta da kuma kalaman bakinta na sai ta kashe ni.
Ko bayan an samu ta sakeni karin kokarinta kuma ta kara rike wuyana. Da gaske take yi sai ta kasheni ni ko gabbaina sun yi sanyi da ba na iya ma wani motsi Adda Fati ne da Ramatu ke faman ja na.
Ammh na kasa kokarin Tallafa musu wajen kare kaina.
Kafin kace me? Gidanmu ya cika Damkam da mutanen anguwa har da Maza magidanta da Samari, ana ta faman maida zencen abunda ke faruwa.
Ko ba'a maida ba irin zage zagen da Mugun alkaba'in da Sahura ke jifana da shi kada'i ya isa mutane su gane abunda ke faruwa.
Sahura ta haukace ko na ce ta fita daga Hayyacinta ihu take yi tare da kwakwazo tana Fad'in duk mganar da tazo daga bakinta a kaina mara kyau da mugun Fata.
An yi an yi a fitar da ita daga gidanmu ammh abun ya ci tura kannenta bazasu iya ba. Sai da suka kira wasu daga chan gidan ba jimawa sai ga su ciki har da yan'uwan Salisun.
Wata mata kamar yayar mahaifiyar Sahuran ce sai da ta tsinke Sahura da kyakyawan maruka har guda Biyu. sannan ta dawo cikin hayyacinta ta koma ta zube a kasa tana sakin wani Gunjin kuka mai fitowa daga karkashin zuciya.
Buda'r bakin Matan cikin Fad'a tace" ashe baki da Hankali ban sani ba Sahura? Mijin ki na asibitin rai ko mutuwa ammh ke kina nan kina Hauka da Shirme?
In yau Salisu ya mutu babu wacce tayi asara sai ke, kin zama bazawara sannan ya'yanki sun zama marayu"
Kalamanta suka sanyayyar ma da kowa jiki ciki har da ni da nake tsaye cikin Halin Tsaka mai wuya.
Jikin Sahura sai ya yi sanyi ta koma ta na kuka Kasa kasa, Umarni taba ma sauran aka kamo Sahura daga zaune ta mike tana Sharbe kuka cikin Kaushin murya tace"Mu je gida Sahura. addu'a mijin ki ke bukata ba wannan hayaniyar ba, kina mganar zaki kasheta in kika Fad'a gaban yan Amin fa? Kika kashetan fa? Ke ma kina da Labarin kashe ki za'ayi?
Sai sahura ta kasa mgana sai Kuka, Wata kanwa ga Salisu ta na matsayin Diyar kanwar mahaifiyarsa ne Zaliha ta kyabe baki tana Fadin"To ba gwara ta kashe mugun iri ba. Ban da Abun Namiji me Salisu ya gani ajikin wannan abar da ya kasa sukuni sai ya aureta? Ta fad'a tana nuna ni sama da kasa kafin ta cigaba da fadin"Ba yadda yan'uwa ba su yi da Salisu kan ya hakura da yarinyar nan ba ammh yak'i Yarinyar da akace ko iyayanta kan Dole suke zaune da ita tun haihuwarta bala'i ke fad'a ma Ahalinta tayi auranta na Farko ta Tsiyace mijin da Ahalinsa gabadaya, ammh kasan da wannan abun kace kai ma sai ka aura ? Haba haba ai wlh ba haka nan ba ne wannan al'amarin da wata a kasa"
Karaf wata tace"Kila farar fatan ta ke Rud'an su. Ko lange langen jikin nata?
Ammh ni ban ga abun sha'awa a tare da wannan abar ba sai jaraban tsiya da Bala'i"
Sai kuma da suka Fad'an na kara bin kaina da kallo duk mganganun da suka Fad'a gaskiya suka fad'a. Ba ni da kyau na azo a gani sai farin fata ,ammh ko dirin nan na mata ba ni da shi siririya ce ni sosai kamar a hureni na Fad'i.
Sun yi ta Fad'an mganganu marasa Dad'i su Adda fati da matan gidanmu ke basu hakuri.
Shudewar awa d'aya sannan balataliyarsu ta bar gidanmu sai gidan ya yi tsit sai dai tashin yan kananun mganganu.
Ni dai juyawa nayi kafana na taku daya bayan d'aya cikin sanyi da wani irin yanke kauna zuwa Dakin Amma. Duk girman tashin hankalin da zan shiga Amma ce mace ta farko da kan Fad'omin araina a irin wannan yanayin.
Ina shiga Dakin Duhu ne ya fara mamaye ganina, ana cikin wannan halin waye zai tuna da kunna yar karamar Fitilar mai chaji din da Adda Fati ce ma ta siya mana ita. Sakamakon Dakin namu falle daya ne karami yasa ina shiga ko da Duhun dakin nasan mazaunin katifar Amma chan na nufa kai tsaye gabana na Fad'uwa.
Sai dai naji gwiyoyina sun yi sanyi ne sanda na isa gefen katifar na ji tashin nishin Amma da kuma rawan sanyi mai had'uwa da sautin karan Bugawar Hakora.
Cikin Daburcewa na Fara lalubanta da Hannayena Lokaci daya ina fadin"Amma..! Amma..!
Jin muryata yasa ta Dago daga kifewar da tayi a tsakanin Wuyanta zuwa cikinta, Da sauri itama ta fara mikomin hannunta guda Daya ta na so ta tab'ani cikin ikon Allah naji Hannunta cikin nawa,sai na kara Firgita jin Dumin hannunta Rau har ya Gauraye da Sanyin na wa Hannun
Bakina da Jiki na rawa da Tuni na manta da Halin da nake ciki na Fara fad'in"Amma jikin ne ya tashi?
Ta shi muje asibiti jikin ki ya Dauki Zafi"
Na ke fad'a cikin Fitan Hayyaci, na mike kenan da karfin gwiwata Amma ta yunkura ta mike zaune Lokaci D'aya tana riko hannuna, sai da na dagata na juyo ina kallonta ta cikin Duhun Dakin muryanta a shake tace"Dawo ki zauna Hasiya"
Musu ba Halina bane balle Musu da Amma sai na dawo gefenta na zauna ammh ban saki hannunta ba Zafin jikinta na shiga jikina ta Dalilin hannayenta da ke cikin nawa na Jimke.
Sai da ta ja gauron numfashi sannan ta kira sunana cikin karyayan Sauti na amsa mata da Sauri cikin Fargaban jin yadda take sauke numfashi, ina tsoron tashin hankali ammh na fi tsoron Tashin hankalin tashin Ciwon Amma da bai da mgani.
Tayi ta wahala ko mun je asibiti sai dai su bata allurai da Ruwa shikenan ya lafa mu dawo gida ammh ni kad'ai nasan a irin yanayin da Amma take kwana ta na tashi in ciwon ta ya tashi.
Shiyasa nake a firgice ko tari mai karfi naji tayi sai Hankali ya tashi matuka.
Cikin Tattausan lafazi ta fara fadi'n"Kiyi hakuri da Kaddaran ki Hasiya. Watarana zaki ji dad'i in sha Allahu"
Kallonta na ke yi ina laluban Fuskarta ta cikin Duhun Dakin, tunani ya tafi nesa da mganar ta ina tunanin yaushe ne Ranar jin Dad'in?
Sai naji mganar Amma daga sama tana Fad'in"Kada ki sake ki saka Tunanin da mutane suke yi a kan ki. Kada ki kuskura ki yarda da su karya suke yi. Abunda suke Alakanta ki da shi Jahilci ne ba Farar Kafa a addini mu Kambun baka kada'i Annabin Rahma ya sanar damu, ko maita babu shi a addininmu saboda haka kada ki damu da duk abunda ke faruwa, Allah ne ya Saukar ma Abubakar duka kaddarorinsa. Sannan shi ya kara Dauro ma Salisu na shi Jarabawan, Ba ke ba ce Hasiya ke baki isa ki zama silar kaddara ko Jarabawan bayin Allah ba. Ba ke ba ce baki da wannan Hurumin komai da ke faruwa da sanin Allah kuma ikon shi ne"
Ta karishe Fad'a tana faman jan Numfashi Lokaci daya Jikinta na kara makarkyata. Na rude hankalina ya kara tashi sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Amma jikin ki na rawa ga shi Zazzabi ya rufeki ki bari mu je asibiti"
ko da ba na ganinta nasan mirmishin nan nata na karfin Hali tayi min kafin ta saki hannayena ta koma ta kwanta tana fadin"Bafa wani abu Hasiya.. dubamin dai panadol na sha Zazzabin zai sauka"
Kafin ta gama mgana ma na bazama Bangon yammah na Dakin saboda Tsabar yadda nasan kowacce kusurwa na Dakin yasa ko cikin Duhu nasan inda muhallin komai ya ke. Wata jaka ce tawa a rataye nan nake saka Tarkacen magungunan Amma in ciwon ta ya tashi kafin mu tafi asibiti.
A cikin Duhun na Dauko mganin, ammh ganin ba na gani yasa na lalubo fitilar na kunna haske ya gauraye Dakin. Da ita na samu na Haska na Debo ma Amma ruwa cikin wani karamin kofi na kuma ballo mata panadol guda Biyu, na tada ita na kuma bata tasha sannan ta koma ta kwanta tana Fad'in"Nagode Hasiya. Allah ya miki albarka Allah ya warware miki kaddarorin da suka Zagaye rayuwarki"
a cikin zuciyata na amsa da Amin ganin ta koma ta kwanta ta na sauke Numfashi yasa na mike a kasalance na karisa wajen ma'ajiyar kayan sawanmu na dauko mata zani cikin zannuwan ta na rufa mata daga kafafunta zuwa kugunta.
Sannan ni kuma na koma gefenta na jingina da Bango ina faman kokuwa da Numfashi na. Ammh kuka ko Hawaye gabadaya sun kafe a idanuwana.
Kirjina na ke wani irin suya,ga harkarina duk ya rike nasan kuma Ulcer ce ammh ba ni da kuzarin mikewa domin na taimaki kaina Ahalin da nake ciki ba na bukatar komai ma duniya komai ya ficemin a raina.
Ina jin tashin Hayaniyar su a tsakar gida, ana ta uban maida zence da Hayaniya kafin Daya bayan daya su fara shigowa dakin Amma, ina jAdda Fati da Ramatu na tambaya ta ko jikin Amma ne ya tashi?
Da kai kawai na iya amsa musu na kasa mgana sai bin mutane da kallo, abun mamaki duk sun ki tafiya har da yan gidan su Babanmu. Su da basa kaunar su Rabemu Daurin auran ma Alhaji Tanko da ya kasance Shakikan Mahaifin mu guda daya daya ragemana, da Adda fati taje har gida ta Fad'a masa mganar Salisu lokacin da yace zai turo.
Ammh Bude bakin sa sai cewa ya yi"Ai kawai Fati ku samu Limamin anguwan ku ya amshi mganar har Daurin auran ma. Wahala ce sai an zo har nan d'in"
Ba nisa fa, ina Samaru ina Dirimi chan gidansa yake ammh a bayyane ya ke kowa baya son Rabarmu saboda ni Hasiya.
Ko su Gambo da suka k'i tafiya saboda jin kwakwaf ne da samun abunda za'a koma ana ba da Labarinsa.
Duk maida zencen da Ramatu da Adda Fati suke a kunnena ammh na kasa wani motsi, sai da naji Ramatu na waya bayan ta gama.
Na kura mata ido ina neman karin bayani sai dai kafin na kai ga muskutawa ta fara fad'in"Musbahu ne"
Gabana sai da ya fad'i na Runtse idanuwana ina jin kaina na wani Gif Gif jira kawai naji Ramatu tace Salisu ya rasu.
Ammh sai ajiyar zuciya ta kwacemin sanda naji Ramatu na Fad'in"Ya ce likito su ce karaya ce guda biyu ya samu, kafa da cinyarsa ta Dama sai kuma yan Rauninka. Ammh ya tabbatarmin da Sauki"
Bansan ajiyar zuciya ta kwacemin ba sai da naji ta fito sarari sannan da kuma kallon da kowa ya bi ni da shi. Sai na samu kaina da Sadda kai na kasa ina jin yar salama da Natsuwa kad'an suna shigata.
Bazan iya sanin iya tsawon Lokacin da na Dauka ban yi barci ba. Abu d'aya na sani shine sai da gabadaya kowa ya yi barci ya barni Har Amma ta samu barci, ta kuma kara farkawa Zazzabin ya sauka tace na bata ruwa ta sha na Dauko mata.
Bayan ta sha ta koma ta kwanta tana ce min"Hasiya ki kwanta ki yi barci kin ji ko"
Da kai na amsa mata,ba domin ina jin barcin ba, Hatta Ramatu da Innarta nan suka kwana Dakin bazai Daukemu ba ita da Adda Fati Dakin Maman Boy suka kwana Tunda ita Mijinta Direba ne baya nan.
Nasan ba ni da kokarin Ibada bar ni da Khamsil Salawati da nake yi a kullum, ammh bangaran Dagema Sallar Dare da Sauran Ibadu ina da wannan Raunin Shiyasa har barci ya Daukeni gabanin asuba ban iya tashi na Raya wannan daren ko don rokon Sauki daga wajen Allah a kan Halin Tsaka mai wuyar da ta ke ciki.
Tare da Fatan samun waraka ga Salisu ni ba ma Aurena na ke ji ba.
Lafiyar Salisu ta fi damuna fiye da aurena da ni da shi.

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now