9

195 22 0
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.

*09*

Kowa kokarinsa ya faranta ma Sadiq rai, maganganu kawai ke tashi kowa kokarinsa ya fad'i bukatunsa Sadiq ya cika masa.
Ga Abba zaune ammh kowa ya tashi sai dai yace Yaya Sadiq ina son abu kaza. Ina son a chanzamin kaza don Allah.
Salima cikin Shagwaba ta ke fad'in"Bros wayata duk ta tsufa don Allah a sauya min wata."
Ta karishe fad'a cikin Shagwaba. Siyama ko gefen hannunsa na hagu ta makale kamar wata yarinya fuskar nan a tabe kamar zatayi kuka tace"Ya Sadiq mu ko wayar ba mu da shi. A siya mana ni da Sultana"
Dariya ya yi yana shafa kanta kafin yace"ba yanzu kuka ka gama Jsce ba? Ku bari in kun shiga SS1 sai a siya muku ko? Nakwa nakwa ta yi da Fuska ganin haka sai ya ja kumatunta yana Fadin"Haba Autan mu Smile mana. Za'a siya muku waya wannan cewar Magajin gida ne"
Jin haka yasa ta saki mirmishi ta juya tana kallon Sultana kafin tace"Sultana kin ji mu ma mun kusa zama manyan yara su Yaya Salima a daina mana wukalamci kan waya.".
Ta fad'a tana nuna ta da baki Salima ta zaburo ta na fad'in"Ni sa'arku ce da kike gasa da ni?
Yaya Sadiq ya kalleta kafin yace"Salima.."
Ta kallesa sai ya girgiza mata kai. Ta gefen idanuwansa Sultana ya ke kallo da har lokacin ko Tarinta bai ji ba.
Yarinyar nan ta na da aiki.
Innani na jin su bakam kawai tayi bata kara mgana ba.
Umma kuma da Mama suke taba Hira Abba kuma an kira wayarsa ya fita.

Tahir na gefe ya na duba wayarsa ammh kacokan hankalinsa na kan Sadiq da yan'uwansa da irin kauna da Gatan da suke nuna masa a ransa yana jin Dama ace Dama ace, Dama ace Shine Sadiq da Duniya ta jima da Shaida wannan gatan da ya ke da shi.
Big sis  Hajiya Surayya ta kalli kaninsu kafin tace"Autan Umma sati na sama Muhsin zai dawo"
Kallonta ya yi yana nazarin waye kuma Muhsin ganin haka yasa tace"kanin mijina mana da na so ku tafi waje karatu tare."
Sai alokacin ya tuna da shi cikin Mirmishi yace"Oh Allah Sarki. Sai yanzu ya gama karatun na shi?
Hajiya Surayya tace"Eh ammh zai koma ya samu kwarewa kan bangaran da ya karanta. Da yanzu ka tafi da muna nan muna shirya maka kyakyawan Tarba Shalelenmu"
Kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya yi mirmishi kafin yace"Big sis. Sunaanshi Muhsin ni kuma sunana Abubakar Sadiq. Ba zai zama Dole Ra'ayina ya zama na shi Ra'ayin ba. Shima ba lalle nawa Ra'ayin ya zama iri d'aya da na shi ba. Shi kanin mijin ki ne ni kuma kanin ki ne akwai bambamci Tsakanina da shi."
Sa'ima ce ta yi karaf tace"To gaskiya in zaka yi masters dinka waje zaka fita ka zabi duk kasar da kake so kaji?
Sadiq ya kalleta kafin yace"Yaya Sa'ima.".
Da sauri tace"A'a mun gaji da ganinka kana gararanba a tsakanin Zariya da gusai kamar wani mara gata.".
Sadiya tace"Kuma Alhalin ina Tunanin kaf set din su ba wanda ya kai shi gatan ba".
Shahida ma ta saka bakinta gabadayansu suka yi masa caa da zencen zaman da ya ke yi a zariya.
Sajida tace"Ni abun haushin ma haya fa ya ke mganar ya kama a chan wani gida suna zaune. In da ya yarda ba sai Abba ya siya masa gida achan ya zauna ba."
Sakeena ta karbe da Fadin"Autan Umma mu dai ka dawo gida don Allah wlh muna kewarka ka bar garin nan sam ni Hankalina bai kwanta da zaman ka achan ba."
Hannayensa ya Hard'e a kirji yana kallonsu yana faman mirmishi. Salima ta karishe mganar da cewa"Big bros kawayen mu duka yayyensu a kasar waje su ke karatu ni in suka Tambayeni rasa ma me zan fad'a musu na ke yi"
Ta fad'a kamar zatayi kuka Dariya ya yi har Fararan Hakoransa na bayyana kafin yace"sai kice mu su a zariya ya yi karatu kuma yana chan yana Hidimar kasa."
Salima ta Zaro ido kafin tace"Bros..".
Kai ya gyada mata alamun eh hakane sai ta jime fuska ta yi mgana su Sakina suka saka Dariya.
Tahir na gefe ya tsoma baki karo na Farko kafin yace"Sai ma kunga ire iren abincin da ya ke ciki.."
Tahir bai tsaya ba ya shiga ba su labarin irin cimar Sadiq ke yi a zariya harda Danwaken da ya ke siya yana Tafiya da shi wajen aiki.
Gabadayansu suka Bude baki suna kallon Sadiq shi kuma ko ajikinsa.
Tahir yace"Abun haushin ma masu saida abubuwan ba su da Tsafta wani abun ma baisan da ga ina aka Sarrafashi ya siya yana ci ba. Ko ni ba na irin Rayuwar da Sadiq ya ke yi kamar wanda ya fito daga Daji."
Sadiq ya kallesa kafin yaace"Daman daga ina na fito.?
Surayya ta kalli Sadiq kafin tace"Why Autan Umma?
Nan fa suka taso masa suna ta mganan gaskiya gwara ya dawo gida ya yi Bautar kasarsa. Su ka gama mganganunsu bai tankan su ba sai daga karshe Umma ta shigar masa ta na Fadin"Ku kyalemin Auta ya yi irin Rayuwar da ya ke so haba. ai ba kauce ma Hanya ya yi ba Ra'ayi ne kowa da irin na shi"

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now