16

171 17 1
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

_Masu bukatar a tallata musu Hajojojinsu cikin Farashi Saukakakke 09069067488_

*16*

*GUSAU.*

Dakyar Innani ta bari Sultana ta yi sati daya a gidan mahaifinta tare da yan'uwanta.
Dafe ta yi ta kasa ta tsare yarinya taje domin ganawa da mahaifinta sannan ta samu zama da yan'uwanta, Ammh innani ba ta bari ba, ta na tare da Sultana kafa kafa kamar wacce za'a yi ma wani abun cutarwa.
Daga matan har shi kan shi Shitun ba su da mafita sun fi kowa sanin Halin Innani don ta fito ta tara su ta tsine musu to abu ba ne da zai zama mai wahala awajenta ba.
Hakanan suka rika Hakuri da ita ammh abu kad'an sai ta yi Allah ya isa akan Bakincikinsa da na matansa ya kashe mata Hauwa kulu akwai Hisabi Tsakaninsu Ranar gobe kiyama.
Sannan ta hana Shitu ya gana da yarsa da ya saka a ka kirata zai ga Innani tare da ita kafa kafa. Sai masifa ta ke yi ta na fad'in uban me zai kuma gayamata? Ba ta son iskanci da neman mgana da munafunci.
Dole Shitu ya kama kansa ya na ji ya na gani Sultana ta koma batare da mgana ta tsakanin Uba da yarsa ta shiga Tsakaninsu ba.

Sannan ranar da zasu koma Gusai Abba ya Turo Direba ya Dauke su Mallam Shitu iya karfinsa ya yi ma Innani da Sultana Hidima ammh sai Innani ta rika fad'in" Dama baka wahalar da kanka ba Shitu. komai da ka sani Sulaimanu na yi ma yarinyar nan babu abunda ta nema ta rasa, Sulaimanu da ka ke gani kudi garesa shiyasa ba mu rasa komai ba."
Ammh ta na jin kannen Sultana na fad'in zasu zo suyi  mata Hutu wani Lokacin in suka samu Hutun makaranta karaf Innani ko tace"A'a ku yi zaman ku, wannan ai dora ma mai kokari wahala ne. wato kun ji nace Sulaimanu na da kudi shine za'a zo kwada'yi ko? To shima ba shi da komai Rufin asirin Allah ne ina ma laifi an Dauke muku wani Laluran? Wannan yarinyar Sulsana ko bante ubanku bai taba siya mata ba Sulaimanu ne da Salamatu. Allah dai ya biya su da Aljannah"
Shitu da Matansa da suka amsa da Ameen Innani dai ta rika masifan kada su so zl sulaimanu ba shi da komai sai Rufin asirin Allah.
Ammh tace su bari Bad'i in an tsaida lokacin bikin Magajin gida da Sulsana sai su zo.

Ba wanda yasan da labarin yanzu za'ayi auran Sadiq da Sultana ammh zuwan Innani Shinkafi labari ya bazu a kunnen kowa.
Har gidan su Baba Sammani da ta je duk haka ta rika ce musu bikin Magajin gida da Sulsana bad'i in sha Allahu. Shitu ma daki ta saka shi ta na fad'a mai cewa gwara ya fara Tanadi tun yanzu Sulaimanu dai ya yi masa na Allah ya yi masa na Annabi. In kuma ba na Shed'an ya ke jira ba sai ya nemi kudin aurar da yarsa Ina za su iya? Tunda shi Ubanta ya na raye? Daman ya mutu ne sai su Dauki na Musulunci su yi."
Shitu dai mamaki ya kamasa ya san da mganar auran Abubakar da Sultana ammh bai san da mganar nan kusa ba. Suna yawan mgana da Abubakar yaro ne mai hankali natsuwa da sanin yakamata wanda ko Alhaji Sulaiman ba su cika mgana da shi kamar yadda suke yawan mgana da Sadiq ba.
Ya na da tabbacin Innani ta zauna ta Tsara mganarta. Shiyasa a lokacin ya kalli Innani ya na fad'in"Ammah Innani Alhaji Ya fad'amin sai Sultana ta gama makaranta za'ayi bikin Lokacin shima Abubakar din ya gama karatunsa har ya kama aiki."
Ai sai Innani ta Zabga masa Dakuwa kafin tace"Allah ya tsine ma karatun albarka. Ka ji min ja'iran ci da lalacewa irin ta Shitu? A na mganar sunnar ma'aiki ka na mganar karatun Bokon tusa da tsiya? Maza ka yi istigifari domin ka yi sabo wajen Ubangiji."

Shitu dai ya ga abun mamaki ta wani bangaren kuma bai yi mamaki ba Tun kuluwa na raye sun sha zuwa Innani ta saka su a gaba ta yi masa wankan Tsarki. Wani lokacin tun Safe ta ke musu Dirar mikiya ka yi mgana ta tattara Tsinuwan bakinta a kanka shiyasa da yasan halinta sai yaci mganin zama da ita. Haka sauran matan masa ma tunda ba yau suka san Innani ba.
Haka suna mota da zasu koma Innani sai faman ciye ciye ta ke yi. ta na cewa su Hassu ba su da kirki sai ga shi ita ba ta kai musu komai ba ammh duk abunda suka bata sai da ta amsa. Aya ko ta yi tiya uku Wacce Innani ta zo da shi. Tsohuwar nan yar bala'i ce ba ta da hakora ammh sai Uban kwad'ayi da son abun duniya. Innani fa har goriba da rake ta ke sha, Wuka ta ke samu ta yi ta kankarewa ta na afawa a baki da hakoranta na Roba ta ke Taunawa.
Yanzu ma Aya ta ke ci sai faman mayau mayau ta ke da baki Direba ya fara Gudu Innani ta fara salati ta na Ihun ya rage gudu. Kuma ba fa gudu ya ke yi ba. Innani ta rika masifa har ta na kukan sai ta gayama Sulaimanu zai kashe masa uwa.
Sai Direba ya juyo ya na fad'in"Innani ba fa gudu na ke yi ba. a tamanin fa na ke tafiya."
Innani ta dake ta karfi tace"Allah ya Tsine ma maka kai da tamanin din. ni zaka raina ma wayau? In ni ba tsohuwar ka bace ka raina ni ai ka Daraja Furfuran tsohon ka ko?
Ya na jin haka bai kara mgana ba Sultana da ke ta kuka tun tahowarsa ta kallah cikin kufuluwa tace"Ke kuma kukan Uban me ki ke yi?
Sultana ta kalli Innani cikin Takaicinta kafin tace a hankali"Sati uku Fa Umma ta ce zan yi Innani.."

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now