10

188 20 0
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V

*10*

Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi haifaffan garin Shinkafi ne da ke Jahar Zamfara.
Asalin sunan Innani Dije ne kuma ta yi aure aure kamar uku kafin ta auri Abubakar mahaifin Sulaimanu, Innani Tun tana matashiyarta irin matan nan ne masifaffu tijararru an yi mata irin auran gida tun da fari ta rika guje guje auren ya lalace bai je ko'ina ba.
Iyayen Innani masu kudi ne, ko a baya Tunda suna Noma sannan suna da Tarin Dabobbi.
Innani itace Matar Abubakar ta biyu ko da akayi auran su taje ta iske shi da uwargidansa kuma uwar ya'yansa Barira. Wacce ta yi ta hauka sanda za'a auro mata Innani tunda a lokacin Mallam Abubakar ya nuna matukar kaunar Innani a Zahiri kuma ya ke nunawa da ya sanya tsananin kishinta a zuciyar Barira.
sannan sanda zata zo iyayenta sun yi mata kayan gata na alfarma tunda ita kadai suka haifa ga shi kuma sun kwana biyu a duniya. Shiyasa dukkan gata suka tattara suka ba ma Innani komai ta ke so ta na samu har da ma wanda ba ta so duka iyayenta na cika mata shi.
Shigowarta gidan Abubakar ya sauya komai saboda ta na son shi tunda ya na lallabata ya na kuma ji da ita. Sannan kuma ya na ji da Masifarta kuma ya na yi mata abubuwan da ta ke so. Sai sanadin haka ya kara hura wutar kiyayya da Tsakanin kishi a gidan Abubakar, komai Barira ta ga Innani da shi sai tace mijinsu ne ya siya musu sannan ta na zargin shi da Nuna bambamci a tsskaninsu.
Har kuma ta jawo ya'yanta cikin kishin ba su dauki Innani a matsayin uwa ba, sai itama kuma ta ce kowa ya yi ta kansa.
Haihuwanta ta farko Namiji ta Haifa aka samu Sulaimanu, bayan shi ta jima bata haihuwa ba,Sai daga baya ta samu mace mai suna Hauwa Kulu. Kuma har alokacin Barira da ya'yanta ba saa raba'ar Innani da ya'yanta duk ko yadda Abubakar ya so ya had'a kan zuru'arsa bai samu ba har ya bar gidan Duniya.
Ya tafi ya bar Barira da ya'ya Biyar,Sammani ne babba Gaddafi ,Sai Hassu sai Husai sai karamar su Zuwaira.

Kuma ya mutu bai bar komai ba sai gidan da suke ciki ita kuma Innani sai ta koma gaban iyayenta da zama ta cigaba da renon ya'yanta a kan nata Tunanin na kada su taimaki wanda bai taimake su ba, kamar yadda Barira ta janye ya'yanta daga Ya'yan Innani ita Innani haka tayi na bakinta tace kowa ya yi ta kansa.
Haka Rayuwa ta mika Innani ta rasa iyayenta komai na su ya dawo hannunta da shi ta zama yar kasuwa mai saida Hatsi, lokaci d'aya kuma ta na kula da su Sulaiman.
Sulaiman ya yi karatun zamani har matakin Diploma a garin zamfara Hauwa kulu kuma iyakarta Jss Innani ta yi mata aure da Shitu shima dan asalin garin Shinkafi ne,ammh wajen shekaru goma da auran su ba ta haihu ba,sai ya kara aure ya haihu sai aka fara Tunanin Hauwa kulu ce bata Haihuwa mgana tayi Tambari a gari Innani ko gida gida take bi ta na Tsine ma duk wanda yace yarta bata Haihuwa.
Sulaiman kuma bazai ce ga Silar Arzikinsa ba, sai dai yasan ya fara da bin wani dan'uwan Innani da ke sana'ar Siyar da kayan wuta a garin Zamfara, Daganan shima sai ya kafa nashi sana'ar ya na saida komai na kayan wuta Daga baya da yayi karfi har na'ura mai kwakwalwa ya ke sarowa ya na Saidawa.
itace sana'an da ya fara samu da shi, Sannan da ita ya yi auransa na Farko da Salamatu yar garin Gummi ce yayarta ke auran Dan'uwan Innani anan suka Had'u. Tsakanin Salamatu da Sulaiman auran Soyayya ce tsantsan da kuma amincewar Innani tunda ta ga Salamatu Allah ya Dora mata kaunarta acikin ranta saboda Ladabinta da Biyayyarta.
A garin zamfara suka fara zama a gidan Haya da ya kama lokacin. Innani kuma ta na Shinkafi ta na gudamar da sana'arta ta saide saide hatsi, da farko wani Alhaji ne ya fara haskamai saro na'urori daga kasar waje saboda an fi samun masu inganci da taimakon Innani ya fara zuwa kasar China saro computoci kuma yaji dadin zuwa sosai Tunda ya samu riba matuka gaya.
Daganan kuma sai ya ga waje bayan China har India ya ke shiga domin Saro kayayyakin wuta. Da shawaran abokan sana'arsa suka haskamai ya fara sana'ar saida Danyan gold kuma ya shiga da kafar Dama cikin Lokaci kad'an ya samu kudin da zai rufa ma kansa asiri tare da innani da kanwarsa.

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now