8

206 21 0
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*08*

Ranar Jumma'a tun safe suka shirya tafiyarsu a son samun Sadiq ma tun 6:30am na safe su bi motar Katsina. Ammh nukun nukun Tahir yasa sai dai suka wuce takwas na Safe a zariya.
Kamar shima bai son Halin Tahir ba, da yace su had'a kayansu waje d'aya ya yarda da batunsa.
Sai da ya gama zama ya shirya musu kayansu na tafiya a karamar akwatinsa. Da duk abunda zasu bukata na tafiyan kwana Hud'u, Ammh Tahir da iskancin sai bayan an gama shiryan kayan ya ke fito da Tsirfe tsirfe daga yace ya manta ba'a saka masa kaza ba, sai ya ce ba kaza zai je da shi ba Sadiq yaji kamar ya cire kayansa ya sauya jaka. Sai dai makaran da suka yi yasa ya yi Hakuri Tunda ya san Halin Tahir ya had'a kaya da shi.

Motar katsina suka samu Direct sai sun je ne zasu Hau na cikin garin Daura. A motar KST irin mu cin mutane sha takwas din nan ne, Tahir gaban Mota ya shiga. Shi kuma Sadiq baya son matsuwa sai ya shiga kujerun baya na daga su sai Direba.
Sun Dauki Hanya aka fara Hirarraki na cikin motar haya na abubuwan da ke faruwa a kasarmu.
Tsadar Rayuwa da yadda komai ya sauya sai kuma aka gangaro kan yan sace sace da ake fama da shi na Mutane a hanyoyin mu na tafiye tafiye.
Sadiq na jinsu bai saka baki ba. Saboda shi bai cika saka baki a irin wad'anan hirarrakin ba. Ammh Abun mamaki Tahir har yana zakewa ana Hiran yan kidanafin ya Dage yana ta zagin su yana Fad'in cewa ai yan iska ne sai sun ce a  basu kudin fansa an gama Biyansu kuma sai su kashe rai. Duk a motar Tahir ya fi kowa Zakewa muryansa tafi ta kowa amsa kuwwa acikin Motar.
Har yana wani Tada jijiyan wuya Sadiq na ta so ya Juyo su had'a ido ya yi masa gargad'i ta cikin idanuwansa ammh ina Hira ta Rufe masa ido. Yasan mafita daya ce itace wayar Tahir yasan ba ta subucewa daga Hannunsa.
Da Sauri ya tura masa da sako kamar haka "Tahir.. Tahir wlh ka kiyayi kanka ka na Daga murya in akwai su acikin motan nan fa?
Ganin Sakon Sadiq yasa Tahir ya Dawo cikin Hayyacinsa. Sai ga bakinsa ya yi gum wani na gefensa har ya na tabosa irin acigaba da Labarinan ammh ina Sai Tahir ma ya fara barcin karya ganin Dannan wayar tasa ma bazai fisheshi ba.
Kuma ya na kama bakinsa sai Hirar ta Sauya daga baya ma kowa ya cigaba da Harkan gabansa Daman Tahir ne uban yan Zakewa.
A haka har suka isa katsina sha d'aya na Safe daganan suka sake samun motar Daura.
Sai daya saura na rana suka iso Daura. Gidan su Tahir babban gida ne, na ginin kasa Inda yayyensa da matansa ke ciki da Sauran iyayansu da kawunansa. Tahir maraya ne ba uwa ba Uba hannun Kakarsa ya taso Hajja.
Suna sauka da kayansu yaran yayyyen Tahir suka kyalla ido suka gansu suka zura cikin gida da Gudu suna murna Fad'i suke yi"Ga Baba Dahiru chan yazo. Hajjo ga Baba Dahiru."
Kafin su ce me wasu yaran sun yayyayemesu har sun dauki akwatinsu zuwa cikin gida. Sai dai suka bisu a  baya suna shiga gidan Shashen Hajja na daga ciki ne sai sun wuce shashen matan gidan.
Suna shiga sai tashin oyoyo Dahiru ke tashi sai dai kaji ana oyoyo Baba Dahiru mutanen Zaria.
Sadiq Dariya ta kusa Shakesa yana kannewa da ganin yadda Fuskar Tahir ke yi in akace masa Baba Dahiru. Sai da suka gaggaisa da su sannan suka karisa Shashen Hajja. Allah Sarki tunda taji zuwansu ta kasa zama ta na Tsaye kofar dakinta tana Duban Hanya Tunda an shigo da kayansu dakinta.
Suna shigowa ta washe bakinta cikin Tsananin Murna ta ke fad'in"Maraba da bakin Zazzau. Ah'a har da Saddiqu a she? Maraba lale da Saddiqu"
Sadiq ya yi mirnishi ya karisa har gaban Hajja shi da Tahir ya rankwafa zai gaisheta ta saka Hannu ta rikosa tana Fadin"Haba Saddiqu mike mike..Ku shigo ciki maraba"
Tahir ta kallah kafin tace"Dahiru maraban ku da zuwa'
Tahir ya hura hanci kafin yace"Hajja wani irin Dahiru don Allah? Sunana Tahir..Sunana Tahir Hajja Ahto"
Hajja ta make kansa tana Fad'in"Tafi d'an nema Dahiru muka sani mu dai ba wani Attahir ba"
Me Sadiq zai yi in ba Dariya ba ya juyo yana kallon Tahir kafin yace"Dahiru shiga gaba mu je"
Tahir ya balla masa Harara shi kuma yana Dariya ya bi bayan Hajja zuwa cikin Dakinta.
Allah Sarki yar tsohuwar nan ta kasa zama saboda su kawo musu wannan kawo musu wannan Farinciki ya kasa barin Fuskata sai faman tambayansu take ya karatun ya'yan nan?
Tahir na jin Haushin Daman sunan da ta daina kiransa da shi yace"Hajja sau nawa zan fad'a miki mun gama karatu Hidimar kasa muke yi yanzu..?
Hajja ta ce'Yo ina ce duk karatun ne ko?
Tahir bai kara mgana ba Sadiq ya bari da kara yi ma Hajja bayani. Ta washe baki kamar ta gane tana fadin"Yauwa na gane yanzu. Saddiqu ya wajen iyayen naka da sauran yan'uwanka? Ina kakarka?
Sadiq yace"Duk suna gaishe ku Hajja."
Daga nan suka bude hira tsakaninsu, Hajja da karfinta ba kamar Innani ba, Domin a shekarunta kasa da na Innani ne, ba ta wuce 70 haka shiyasa da karfi a jikinta sannan jiki ya saba da Wahala tuntuni ba kamar Inanni ba, duk dai itama ta yi zaman kauye ammh bata cikin Wahala.
Ruwa kawai su ka sha sai Furar da ta Dama musu saboda jumma'a ne yasa suka yi alwala zuwa masallacin jumma'a suka yi sallah. Sai wajen uku suka dawo gidan chan suka had'e da yayyen Tahir suka gaggaisa suka kuma Dungumo zuwa Dakin Hajja a tare da aka gama cika shi da abinci kala kala na tarbansu.
Sadiq ya saba zuwa gidan su Tahir tun suna makaranta ya saba da duka Ahalin Tahir kamar yadda shima ya saba da na shi Dangi. Kowa a gidan su Tahir yasan waye Sadiq kamar yadda Sunan Tahir ya yi tambari a gidan su Sadiq, tare suka had'u suka ci abinci Shi dai Sadiq Dambun Zogale ya ci Tahir kuma ya ci Taliya da Miya da Nama,Sadiq Naman kadai yaci saboda Nama na daga cikin abunda ya fi so duk Duniya.
Sallar La'asar ya tada su suka tafi masallaci bayan sun fito kuma ba su dawo gidan ba, sun had'e da abokan Tahir tun na kuruciya suka zauna akofar gidan su Tahir suna ta Hira sai da aka kira sallar mangariba sannan suka tafi masallaci ba dai su suka dawo gidan ba sai bayan Sallar Isha'i.
Suna shigowa suka iske kanwar Tahir mai bi masa Zulaihat tazo har da Girki ta yo musu.
Tana ganinsu ta washe baki tana Fadin"Yaya Dahiru sai yanzu? Tun dazu nazo Hajja tace kun je masallaci'
Tahir ya ware mata ido kafin yace"Ke.. ina wasa da ke ne? Ba na gayamiki ki daina kirana wani Dahiru ba Sunana Tahir"
Hajja na saman Darduma ta na lazimi tace"Kaji tsirfan banza, da Dahiru ubanka ya yanka maka Rago. Shi muka sani kuma Shi zamu cigaba da kiran ka"
Sadiq ya yi mirmishi yana Rufe baki ganin Tahir ya yi wani Fuska yana Huci Jikin Zulaihat ya yi sanyi sai ta Juya tana kallon Sadiq kafin tace"Yaya Sadiq sannun ku da zuwa"
Ya amsa mata cikin sakewa yana Tambayanta ya gida da yaran.
Tahir da kansa ya gaji ya saki Fuska, ballatana da ya Zulaihat tace alele ta yi ta kawo musu sai ya warware suna ta fira ballatana da yayyensa suka shigo suma aka had'e ana ta Hira ko da ba ma su kudi ba ne ammh akwai kaunar junansu da kyakyawan zumunci a Tsakaninsu.
Sannan da shakuwa da kaumar junansu musamman Tahir da suke ganin shine karamin su Tunda Zulaihat ta yi aure ta gina na ta iyalan.

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now