7

196 23 0
                                    

*TSAKA MAI WUYA.*

*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V

Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.

Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.

Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260..  Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus

*07*

Shi Sadiq a kan Quantity Surveying ya samu shaidar Degree d'insa na farko.
Ma'ana sani kan harkan shimfid'a Titina da sauran su.
Shiyasa ya ke bautar kasar sa a Dismento Nigeria limited Old Sokoto Road, Samarun Zaria.
Shi kuma Tahir Politcal Sciences ya karanta wato harkan abunda ya shafi Siyasa. Ya na bautar kasar sa ne shima a wata goverment secondary na cikin Samarun zaria.
Yau litini tun bakwai da Rabi ya fita ya bar Tahir a gida ya na faman nuku nukun sa, Sai da ya biya in da ya fara siyan Danwake mai d'an karen Dad'i ya mika karamar kularsa da ya ke zuwa da ita ga yaran da ba'a rabasu da wasa a kofar gida suka shiga suka amso masa.
Dashi ya tafi wajen aikin nasa. ya riga ya saba tunda ya samu Danwaken nan da shi ya ke tafiya wajen yana karyawa har kuma wani Lokacin ya yi ragowa ya dawo da shi gida. Watarana kuma wani wanda suke aiki a wajen shima hidimar kasar ya ke yi suke ci tare.
Karfe biyu saura ya baro  kamfanin kamar yadda ya saba adaidaita ya hayo zuwa anguwar Tsamiya aka sauke sa a bakin Titi ya gangaro da kafarsa.
Yasan Tahir na rigashi dawowa tunda makarantar sa ta fi kusa gida. Sannan ba tsayawa ya ke a tashi ba da ya gama Darasinsa ya ke gudowa gida Tahir dan Shiririta ne ba komai ya ke ba ma Muhimmanci ba shi dai wayarsa kamar tafi komai muhimmamci a rayuwarsa.
In kaga ciwon da Tahir bai Dauki waya a hannunsa ba to kila sai dai ciwon Ajali mutun ne mai mu'amala da kafafen yad'a zumunta sosai ba irin Sadiq da waya ko hawa irin kafafen nan ba su dame shi ba, Shi dai barsa da kallon Fina Finan korea da turkish Drama suna nan cike a Laptop dinsa ko Tab dinsa. Sai kuma sanin kan Na'ura mai kwakwala wannan tun yana karami ya iya sarrafata tunda ya taso ya gansu ne shima agidan su.
  Dakin a bude Tahir ya barshi Saboda Sabon Iskanci har da su Dage Labule sama a dakin na Fuskantar waje, ga shi cikin Anguwa mai cike da Mutane sai wucewa ake yi ana ganin musu asirin dakin
Ba wannan ya fi bata ma Sadiq rai ba sai ganin yadda Tahir ya yi kaca kaca da Dakin Alhalin kafin fitarsa da Safe sai da ya kimtsa dakin shara ne kad'ai bai yi ba yace sai ya Dawo.
Tun kafin ya shigo ya gimtse fuskarsa Sanye ya ke da Riga da wando,Rigar mai Dogon hannu ce mai ruwan Ash da layi layin blue. Wando kuma jeans ne mai ruwan kasa sai Rufaffen baki takalmin da ke kafarsa bayansa Rataye da Jakar laptop d'insa sai karamar kular da ke hannunsa.
Yana shigowa ba domin sanin Darajan Sallama ba, da ba zai yi ba sai dai yasan Darajanta tunda shi Musulmi ne Murya ba Dad'i yace"Assalamu Alaikum.."
Bai ko jira Tahir dake kwance kan Katifa da ya yi wani da'i da'i ya amsashi ba cikin Fusata yace"Haba Tahir. Haba Tahir meye haka?
Ya fad'a yana kallon Tahir din cikin Takaici.

TSAKA MAI WUYA.!Where stories live. Discover now