Page 20

1.6K 129 4
                                    

    *Y'AR FARI*
*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*

Written by
              zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on wattpad@zeeyybawa
#facebook@zaynab bawa novels
#IG@Zyernab Alabura

*ya arrahman ya arrahim*

   Assalamu alaikum."
Y'an uwa dan Allah kutaimaka kusanya *safiya abdullahi huguma*  cikin addu'a plz tana buqatar addu'oiinkuu kada kumanta dasanyata cikin addu'a idan kunyii sallolinkuu, Allah kadai yasan bakin wanda zai amsa."
Y'ar uwa Allah yabakii lpy." Allah yasanya ayii cikkn sa'a."

   ****      ****       ****     ****
Wannan shafin nakune ku kadaii *maiimounatuh* da *xeecul* comment d'inku yanamun 100% inajin dad'insa sosaii, kyautan page guda gareku dan kuci gabada sambad'owa comment, Xeecul ina turawa nake la6ewa nafara kallon cmmnt dinki😂Ngd sosaii da qaunarku ga y'ar farii."

***     ****      ****      ****

*page 20*

  Babysis ce tafito daga d'aki hankalinta nakan wayarta,  da earpiece sakale akunnenta tana pressing wayar dake hannunta, hankalinta baiga cikin palour d'in damuwarta d'aya ta isazuwa kitchentad'auko abunda zata d'auko tajuyo, abunda tajuyone yasanyata juyawa tana kallonta, haffiiza ce fad'in kodaii anqii ko anso nima saina haifee d'a agidannan shima yacii gado."

    juyawa babysis tayi gabaki d'aya tana kallon hafiiza wacce keta maida numfashii bayan tagama maganar, kamar maishirin haihuwa, babysis kuwa bata tankaba, tsakii tad'anja, takawarda kanta gefe, miqewa hafiiza tayi zumbur tana kallon babysis tace, ke dan uwarkii dawa kikeyin tsakii ?"

yatsina fuska bbysis tayi hankalinta yanakan hafiiza kawai tana kallonta batardda tatanka taba."
   

   Itama hafiizan kallonta takeyii sosaii takejin haushin yarinyar dan  Babysis tayi tsayii sosaii siririyace batada qiba tayii wanii irin mugun kyau, alamun girma ya bayyana attatareda ita, kallon haffiza takeyii sosaii batace komaiiba tajuya zatabar wajan hafiiza tayi saurin jawota tayi laga-laga zata fad'ii saikuma taja tatsaya, earpiece d'in kunnenta tacire sannan ta tattare hankalinta gabaki d'aya akan hafiiza cikin tsiwa tace maikuma yafaruu dazakii jawonii ?"
   Uwarkiice tafaru, danme zakii bini nida cikinda da kallon banza sannan kuma kija mana tsakii ? "

Kallonta babysis tayi sosaii sannan tace" ciki to aiinii banganishiiba,
  Kama bakii hafiiza tayi tace auubaki ganshiiba to dan uwarkii kokinso ko kink'i saina hafe cikinann agidannan  sainaga tayimun gorii akan cewa gidan ubankune, wata er dariya bbysis tayii sannan tace" Allah koh, toh muna zuba idanuwa, tana fad'in haka tawuce tabar hafiiza tana ciza le66a."

   Kitchen babysis tashiga tad'auki abunda zatayii amfanii dashii tadwo tawuce d'akii batareda taqara kallon  inda hafiiza takeva, hafiiza kuwa kwafa tayii tanajin wanii irin zafii aranta taso ace babysis taqara cewa wanii abuu tamareta sannan kuma tayi mata sharrii wajan mahaifinta dantsan yanda yakeson cikinnan zai iyayin komaii."

Zama tayi gefen mahaifiyarta tanashan yoghourt, kallonta mahafiyarta tayii cikeda dan zargii tace" nikam bbysis wai maiyasa nagankii kwana biyuu cikin farincikine haka, duk wanii abunda mahaifinki yakeyii miki koda kuwa aiikine dayake sakakii akan haffiiza bakii damuwa saima nishad'ii dahakan yake sanyakii, koda kuwa zaginki akayii, ni ina murna da irin farincikinda nake kallonkii amma kuma inatunanin kaman kina riqe hakan cikin zuciyarkine dan Allah babysis kidena damuwa daduk wanii abunda zasuyii kidena riqewa cikin zuciyarkii."

   Batarda damuwa afuskar babysis ba tace" ummii waya fad'a miki  inasanyawa araina ?" aikomaii yawuce knsu suke yiwa, shafo kanta ummii tayi sannan tace toh Allah yayi miki albarka, lumshe idanuwanta tayi sannan ta amsada amin."

Y'AR FARIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora