page 98

1.2K 136 8
                                    

*Y'AR FARI*
*بسم الله الرحمن الرحيم*

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on #wattpad@zeeyybawa
#facebook@zaynab bawa novels
#IG@Zyernab Alabura."

*page 98*
*
    Antyce tayi qarfin halin ebo ruwa ta zuba mata, ajiyar zuciya taja dakarfi amma bata bud'e idanuwantaba,

Sai kuma tasake kuka,
bud'e idanuwanta tayi tazubesu akan yaya umar, harara tawatsa Masa, batareda tace komaiba,
Miqewa tayi bata damuda yanda dare yatsalaba yafice daga gidab gabaki d'aya batareda tajira anty kokuma yaya sun tafi tareba,

Dannawa tayi gate d'in yabud'e yashige cikin gidan dasauri, tana wuce harabar gidan tanufi cikin gida, sama tawuce d'akinta kai tsaye,

Zubewa tayi akan bed tashiga rera kukanta mai tsuma raii,
Yaya umar da mata da yara har biyu, sannan kuma da cikin na uku,

  Na shiga uku ta ambata a fili,
Bata dad'eda shigowaba anty tashigo,
Ganin yanda take kuka yasanya jiki. Anty yamutu, wani irin tausayi da son d'iyarta wanda bata ta6a jinsaba a'iya rayuwarta takeji yanzu,

Qarasawa tayi bakin gado, tazauna shafa kan husna tafarayi tanajin itama kamar ta tayata kukan,

Husna! Anty takira sunanta cikin sanyin murya,
D'agowa husna tayi tadubeta da idanuwanta wanda sukayi jazazirr,

Share hawayen kitashi inaso muyi magana,
Bbu musu husna tamiqe zaune tana share hawayenta,
Cikin sigar lallashi da jan hankali anty tace"
Husna menene abun kukan?"
Akan kinason faruq kuma yanada mata?"
Kokuma akan kinasom komawa ga mijinki?"
Za6i yarage gareki husna,
Dan faruq nada mata, bashine hakan yana nufin bakida mazauni cikin zuciyarsaba,
  Kuma dan yanada nata ba hakan yana nufin bazai riqeki da amaba,

Sannan kuma inaso kisani husna,

Kasancewar faruq kikeso hakan bazai hana kiso abdul ba anan gaba,
Dama kawai wannan lamarin yake buqata,
Zaki soshi fiyeda yanda d'an adam zaiyi tunanin zaiso wata irin halitta,

Kinsan yanda nakeji akan bbaanki?"
Ina fata kema kiji haka akan mijinda zaki za6a,
Saboda koda dana lokaci d'aya naga yanayinsa ya canja, nakanji kamar komai na duniya ya canjamun,

Husna akullum nakasance nakanso zuciya idan abu yasgafeki,
Nakan nuna kibi umarnina kawai,
Amma wannan Karon,
Wannan karon natsinci kaina dason farin cikinki,
Wallhy husna cikin biyu duk abunda kika za6a zanyi alfahari dashi sanna na nunawa duniya cewa wannan shine za6in d'iyata,
Banda tacewa awannan lamarin husna,
Amma inaso kitsaya kiyi tunani,
Kiza6i yanda zuciyarki tafi rinjaye,
Kada kiza6i son zuciyarki kiza6i abunda kikesowa zuciyarki,

Kizauna kiyi tunanin iya tsawon lokacinda zaki d'auka,
Nidai ina fata koda mai kika d'auka yazame shine mafi alkhairi cikin rayuwarki,

  Banda wani burinda yawuce naganki cikin farim ciki,
Kizafi kowanne guda d'aya acikinsu, kada kidamu kowanne yana sonki kuma zasu riqeki aman,
Sanna kuma duka sun baki shekaru masu yawa, kingani zasu tsufa kinada kyawunki kamar nida babanki,
  Dariyace tasu6ucewa husna, aikuwa tahauyinta,
Itama antyn darawa tayi kad'an saboda dama tayine dan tasanyata dariyar,
Yanzu share hawayenki, basai kinyi kukaba kawai nazari da addu'a lamarin naki yake buqata,
Maza tashi kiyi wanka sannan kikwanta bacci saboda wannan kukan kada yasanya miki ciwon kai,
Miqewa tayi had'eda fad'in, toh anty yunwa nakeji,
Kishiga wankan zan duba miki abinda zakici,

Yaya daga bakin qofa yanajin duk wani abunda yafaru, cikin zuciyarsa yace" to aii shikenan babu wani abun da zanyi,
Juyawa yayi yanajin lallai anty tacanja tunda har ta'iya zama tayiwa d'iyarta wannan kalaman cikin nutsuwa,
Harda lallashi, sannan kuma bata tilastata akan taza6i mutum d'aya acikinsuba tafad'a mata tazabi abunda take sowa zuciyarta,

Y'AR FARIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant