1-5

4.8K 149 6
                                    

MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
 

1

Writting by Maryam S Indabawa
MANS

Bismillahir Rahmanir Rahim
Da sunan Allah mai girma da Rahma.

Na fara da sunan Allah mai Rahma mai jinkai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin Muhammad (SAW).

Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadil al fatihi lima uglika wal khayimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki wal hadi ila siradikal mustakim wa'ala alihi hakka qadrihi wal mikdarihil azim.










Wannan littafin naki ne yar uwa, rabin rai, NUSAIBA SULEIMAN INDAVAWA, Allah kara mana kaunar junan mu, Allah daurar da zumuncin mu AMEEN,

Allah baki miji nagari, Allah inganta rayuwar ke da little MEEN, HAUWA'U USMAN (YASMEEN) Ina kaunar ku ina alfahari da ku kannena,

Allah ya faranta muku a duk inda kuke Allah baku zuri'a ta gari AMEEN! Da dukkanin musulman duniya baki daya.







zaune suke shi da abokan sa a babban tsakar gidan, akan carpet suna cin abinci, mikewa yayai ya shiga cikin dakin sa, adai dai lokacin wata kyakyawar budurwa wace bazata wuce shekara 15 ta shigo gidan da sallamar ta gannin da Mutane a tsakar gidan yasa ta cire takalman ta, ta ajiye a soro dan girmamawa.

Karaso war ta ciki kenan shi kuma ya fito daga daki, da gannin ta ya rufe ta da fada.

"Ke baza ki girma ba har yanzu ji yawo ba takalmi,"

Ya fada yana nuna kafar ta, durkusawa tayi tace.

"Yana soro fa takalmin ganin da Mutane yasa na ajiye a can,"

"Karya kike ni wuce ki bani waje."

Daki ta shige inda Yayar ta take, tana matsar kwalla dan tana jin zafin yadda yake mu'amala dasu, amman in 'yar sa ce 'yar shekara 4 yai ta mata dariya amman su sam basa gannin fara'ar sa ko meyasa ohoo?

Antyn ta dake zaune kan kujera tana ta danne dannen wayar ta dan aikin ta kenan kullun.

Tana zaune tana fama da wannan abun, Mahaifiyar su wacce suke kira da UMMU ta kwada mata kira,

"KHADIJA!"

"Na'am,"

Ta amsa da sauri ta fice, ta durkusa tace

"Gani UMMU"

"Ungo maza je ki siyo Ruwa."

Karba tayi ta mike tayi waje dan daman da hijab din ta ajikin ta,

Aiken ta kai wa UMMU, sannan ta fada mata za taje gidan UMMA dan za suyi gwajin rawar gada, da za ayi bikin yar kannin mahiafin su,

Suna cikin yin Gwajin taji yo ana kwada mata Kira.

"KHADIJA! KHADIJA!"

"Na'am"

Ta amsa da karfi, dan katanga daya ce ana iya jiyo wa in an kirata,
Gida tayo tana addu'ar Allah yasa ba kuma wani abu tayi ba.

Ta shigo gidan da Sallama, tin a soro ta fara jiyo mitar sa,

"Ke dama ke kike kara daure mata gindi, ta fita taje tana ta rawa ai da Mahaifin su na da rai da bazai bar ta ba,"

"Haba dan Allah ai bikin yar Kannin. ABBUN su akeyi,"

"Kina ina ke zonan ki shige ciki."

Daki ta wuce inda ta samu Antyn ta na aikin da ta saba, wato danne dannen wayar ta. kallan ta KHADIJA tayi taga duk ranta a bace yake, dan Anty in Akwai abin da ta tsana bai wuce fada ba ki hayaniya.

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now