26-30

871 40 0
                                    

[11/20, 12:53 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFW STORY

BY MARYAM S INDABAWA
MANS

page 26



Dedicated to My student *FATIMA SALISU,* *ZULAIHAT AUWAL,* *HASSANA & USAINA RABI'U,* *FATIMA ABDULLAHI,* *HALIMA AUWAL SHARIF.* love u soo much. U always make me happy.





Da dare bayan mun kwanta sai ga kiran Aliyu nan. Fita nayi dan nasan halin Faiza yanzu zata fara min cah.

Falo na nufa na zauna.
"Baby nah!"
"Na'am, yaya nah.'

"Ya gidan ya gajiyar biki."
"Lafiya. Gajiya tabi jiki.'

"Masha Allah, gobe I yanzu naga Baby na ko?"
"Eh! Mun dade da haduwa ma."

"In kin ganni zaki gane ni."
"Taya zan gane ka ban san ka ba."

"Haka ne! Bari na baki satar amsa. Dan da kin ganni ki gane ni."
"Toh."

"Gobe zan sa farar sadda da babbar riga xan hula mai adon baki, takalmi da agogo duk bakake. Dan haka da kin ga mai irin wannan shigar to gun ki yazo. Sai dai fa ni baki ne, sannan ban da kyau."
"Haba Ya Aliyu. Ni nace mutum mai kyau nake son aura ne,"

"Alhamdulillah matata ta yadda dani koma a ya nake, nagode miki hafsa sai da safe kije ki huta."
"Allah kaimu nagode."

Nayi daki na kwanta. Da tunanin yaya gobe zata kaya gani ga Aliyu.

Ranar daurin aure saddar da Ummu tai mana muka saka, ruwan goro sai zanen ruwan ganye, dinkin riga da siket sun amshe mu. wani ruwan ganyen mayafi muka saka mai duwatsu a jikin sa. Sosai mukai kyau. Da yamman ranar za ayi walima inda Malama Binta Yahuza xatayi lecture.

Tin safe akai mana kwalliya, wacce nace ni baza ai min shafe shafen nan ba. Hoda da jan baki sai ja gira kadai akai min, amman nayi kyau sosai.

Karfe goma mun shirya dan sai anyi sallah juma'a za'a daura auren.

Tin da na tashi nake jin faduwar gaba. Wanda duk ya sauyan yanayi. Faiza taje ta fadawa Momy. Momy da kan ta tazonta dauke ni.

Dakin Dadyn Faiza ta kai ni. Tace in zauna na huta.

2:30 naji karar wayata wadda tai dai dai da fadiwar gaba na. Dauka nayi na duba Aliyu ne,

Ji nayi dukan da kirjina  ya ke ya dado wanda har sai da na dafe shi.
"Hello Princess. Kin tashi lafiya? Gani fa nazo. har an kaini boys quarter's din gidan."
"To gani nan."

Na dade a zaune kafin na iya tashi na fita. Bayan gidan na tafi kai tsaye bayan na fadawa mai aikin su Faiza ina da bako ta kawo masa abinci.

Har lokacin kirjina bai daina dukan uku uku ba.

Da sallama na shiga dakin.
A tsaye na hange shi ya juyan baya. yana amsa waya.

Kallo na kare masa. Gaskiya Aliyu cikaken namiji ne dan tin ta bayan ma hakan ya nuna.
Dogone shi mai cikar haiba, fari ne nagane hakan ta wuyan sa.
tabbas farar shaddar yasa ka da hula mai kyau wacce take da adon baki. Gashi ne kwance akansa mai kyau da sheki.

Kallon sa nake ko kiftawa bana yi, kamar yadda bugun zuciyata bai canja ba. Ga wani sanyi da nake ji sai kace mai zaxxabi.

A hankali ya juyo, ta kafar sa nasan ya juyo tinda kai na a sunkuye yake,  wayar ya katse sannan , yace,
"Wow amman fa amaryata tayi kyau. Dama muma yau ne ranar mu da daga nan sai gidan mu."

Shiru nidai nayi,  murmushi yayi, ya cigaba da magana.
"Hafsa yau dai ga Aliyu Haidar,a gaban ki, yake kyakyawa, sarauniyar yan matan duniya. Ina son ki dago ki kalli mummunan Aliyun ki, kiga ko zaki iya maneji dashi a matsayin mijin ki."

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now