21-25

1.1K 51 1
                                    

[11/20, 12:50 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY


BY MARYAM S INDABAWA
MANS


page 21





Yau tun kan na kwanta bacci na fara jin ciwon mara kayan magunguna na duba naga babu maganin da nake sha a ciki, kwanciyya nayi, ina adduar Allah yasa ya zon da sauki.

Cikin dare kuwa ciwo ya tasar min, gashi bana son in tada Khadija da Ummu, ni kadai nayi ta fama kan asuba na gala baita dan bansan ina ina nake ba duk na fita a hayyacina.

Ummu na zaune kan abun sallah, yau sam bata ji motsin tashin mu ba, wannan yasa ta mike ta zo dakinmu.

Ko da tashigo ta ga halin da nake ciki yasa ta rude, tace, "Hafsa lafiya?"
Ganin ba na cikin hankali ne ne yasa ta kuma rudeea dan tasan marata ce tinda na fita a hayyacina haka, amai na dinga yi ina daga kwancen nan.

Ummu waya ta daukobta kira Ya Kamal daga masallaci yayo gida, Ummu da Khadija su suka gyara ni sannan Ummu ta dinga duran ruwan dumi tana gasa min mara.

Ya kamal na zuwa mukayi asibiti, muna zuwa suka amshe ni a shiga dani ana min taimakon gaggawa, ni ce har da su karin ruwa, sannan ya yi min alluarai ya ban gado. Duk da haka Ummu mara ta ta dinga gasa min dan in samu sasauci.

Ranar yini nayi ina baccin wahala, sai dare na tashi, Ummu ita ta kaini bandaki nayi wanka duk jikina ba dadi ga jiri ina gani, na fito na canja kaya, tea ta hadab wanda ko sugar bata zuba min ba, da kyar na iya sha.

Ummu sai sannu take min, bayan nagama ne sai ga sallamar su Hauwa da Ya Nura tare da Ya Kaml da Ummu suka gaisa sukai mata ya mai jiki. Sannan Ummu ta fice, gefena Hauwa tayo, tace,
"Sis kiga wahalar da kike sha amman kinki rage shan zaki ko, dan Allah ki rage,"

Toh,Kadai na iya ce mata, tace, "sannu,"

Waya naji ya Kamal nayi, sai naji yana cewa, Eh gata nan, ina ba lafita muna asibiti," yayi shiru alamar yama sauraron.me ake fada daga can bangaren.
"Eh wayar ta na gida," ya fada yana kara yin shiru,
"Ok to gata," ya mikon wayar yana cewa,
"Ya Haidar ne,"

Na amsa ina karawa a kunne na, murmushin karfin hali nayi, na amshi wayar da sallama murya ta can kasa,
"Yar gida na yajikin?"
"Da sauki,"

"Allah kara sauki, kanwata, me yake damun kine,?" kasa nayi da ido, nace,
"Ciwon ciki ne,"

"Ayyah Sannu Allah sauwake, kace na taho dubiya,"
"Ah haba dai Ya Haidar yau fa kwanan ka shida da tafiya,"

"To mene ai kanwata zan zo duba wa,"
"To ai naji sauki,"

"Da gaske,"
"Eh!"

"To shikenan Allah kara miki lafiya,"
"Ameen,"

"Kinsha dai magani ko?"
"Eh nasha,"

"To me kike so yanzu?"
"Ba komai,"

"Kin tabbata,"
"Eh,"

"To shi kenan bari na barki sai anjima princess," na kashe wayar ina ajiyewa

Sallamar Faiza muka jiyo, muka amsa ta shigo, su Ya Nura ta gaisar tayo wajen mu, ita ma dayan gefen nawa ta zauna, suka sani a tsakiya.

"Sannu Sis ya Jiki?"
"Da sauki, wai wa ya fada muku bani da lafiya ne?"

"Na kira wayar ki shiru, shine na kira Khadija ita take fada mana," murmushi nayi nace, "ai na warke,"

"Tare muke da Momy ma tana wajen Ummu ne,"
"Allah sarki kika taso ta,"

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now