66-70

726 47 0
                                    

[11/20, 1:15 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



Page *66*





A gaban Ummu ta zaunar da ita akan karfet. Ummu tace,
"Haba Anty Fati ai kin gama mata kuma."
"A'ah gata nan dai."

Ta juya ta fita. Su Hauwa ya rage a dakin. Mikewa sukai Ummu ta tsaida su.

"Ku dawo ku zauna dukkan ku"
Dawowa sukai suka zauna suka sa Hafsat a tsakiya.

Kallon su tayi gaba daya sannan ta fara magana.

"Duk abinda zan fada muku nasan kun sani sai dai na kara jan hankalin ku akan sa, da kara nuna muku su."

Shiru sukai. Kan Hafsat a kasa tana zubar hawaye,

"Ku kula da ibadar Allah Musaman kula da sallah akan lokaci tare da kula da kaidojin ta,
Ku kiyaye tsarkin jiki dana tufafi da na muhalli tare da cikakkiyar tsfta a ko wanne lokaci.
ku kasan ce kuna yawaita zikirin Allah da Sallati ga Annabi da godiya ga Allah da istigifari.
Ku yawaita karatun Al kurani a duk lokacin da kuka samu sarari. Ku daure kuna karanta abinda ya sauwaka a kullum.
Duk abinda ya dameki ko ya tayar miki da hankali kada ki dimauta kiyi hakuri. Kuna yawan addua ki gayawa Allah.
Ku girmama mijin ku a ko wanne lokaci kuma kubi duk umarnin da suka baku. Matukar basu sabawa Umarnin Allah da Annabin sa.
Ku kula kwarai ku kiyaye da abinda mijin ku suka fi so. Kuyi kokarin musu wannan abun.
Ku kula da abinda basa so ku guje shi
A duk lokacin da kukai wa mijin ku abinda ya bata musu to kuyi saurin basu hakuri da neman afuwar sa
A duk lokacin da mijin ku ya bata muku rai kada kuyi saurin fushi da tayar masa da hanakali. Ku yi hakurin tare da addu'a.
Amman idan ya zama dole ki fahimtar dashi to ki fahimtar dashi ta cikin ladabi da girmamawa tare da kalmomi marasa tayar da hankali."



Shiru tayi sannnan ta dora,
"Ku guji yawan kai karar mijin ki wurin kowa don gudun tona asirin ku sai dai idan har ya zama dole. Shima sai ki tari iyayrnki ko iyayen sa.
Ku guji sauraren 'yan tsegumi masu kawo miki labarin rayuwar gidn wasu.
Kuma ku rike sirrin gidajen ku.
Ku dauki rayuwa da sauki. Ku yawaita tunanin abinda yake me kyau da wanda baida kyau.
Ku guji yawaita kalle kallen fina finai barkatai da karanta littafi marasa amfani. Mai makon haka kuna karanta al qurani.
ki yawaita addu'a ga Allah dan neman Rahama.
In Allah ya albarkace ku da ya'ya ku.  Kula da tarbiyar su da ibadar su
Duk abinda zaki nema wajen mijin ki kada ki taba zafafawa. In bai miki ba ki yi hakuri in ya mike ki gode masa.
kada ku nuna musu kwokwanton amarsa da gaskiyar sa.
Ku guji yin gasa da Kawaye ki godewa mijin ki akan duk abinda yai miki."


"Ku zama masu alkinta kayan mijin ku. Banda almubazzaranci.
Ku girmama yan uwan mijin ku da iyayen su
Ku na ziyar tar yan uwan ku da na mijin ku.
Ku san kalaman da zaku na fadawa mazajen ku
Ku tabbatar da tsafar jikinku da muhalli da tufafin ku. Ku kula da gashin kan ku, cikin kunne, baki, hammata, da gaban ku.
Kada mijin ku ya shaki wani wani abu maras dadi daga jikin ku
ku daure kunayin Sallah cikin dare
ku nisanci cudanya da maza
Kuna tambayar miji irin abincin da yake so
Ku kasance masu kyawawan hali
Kuna kamala Girki akan lokaci"

"A duk sanda kike magana da mijin ku kada ki daga murya komai bacin ran ku. Ku guji sa'in sa da shi
In Allah ya hadaku da abokiyar zama ki rumgume ta tsakani da Allah to Allah zai kare ki daga kaidin ta.
In zaku fita kuna shiga ta musulunci
Kada ku taba fita daga gida ba tare da cikaken izinin mijin ki ba.
Domin Manzon Allah (SAW) yacr
"Duk matar da ta fita daga gidan mijin ta ba tare da izinin sa ba to har taje ta dawo tana cikin tsinuwar maka'ikun Allah."
dan haka ku kiyaye."

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now