31-35

807 51 0
                                    

*MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *31*




Kanta ta dauke ta dan juya tace,
"Ango ina yini. Ya hidima?"
"Ba ruwana da ke tinda kika bataea amaryata rai."

"Ni me nayi mata?"
shiru yayi mata ya juya gefen Faiza, su a magaba kasa kasa.

Juyowa tayi ta cigaba da kallon titi, ji tayi an kama hannun ta, wani sanyi ne ya ratsatta tare da jin tsigar jikin ta na tashi.

Kokarin cire hannun take amman ya rikeem gam, ba komai yake son kalla ba sai idanun ta masu kyau da girma. Amman sam taki dago kanta  kamar tasan abinda yake son gani.

Daga hannun yayi. Yayi wajen bakin sa dashi. Da sauri ta daga kai ta kalle shi. Caraf idanun su ya hade ya shiga cikin na juna.

Gefeb titi yayi da motar. Ido ya lumshe dan ji yayi kamar an dada masa sonta.

Zame hannun ta tayi. Wata tafiya ya ringayi kamar bai son tukin. Har su Hauwa suka je bamu karasa ba.

Ko da muka isa ban san mun isa ba. Na tafi duniyar tunani,dan ashe har su Faiza sun sauka.

Jin rufe mitar ya dawi dani hayyaci na da sauri ya rufe motar. Janyi ni yayi, nayi saurin janye jikina.

"Dan Allah Hafsat ki bani dama zan wanke miki damuwar ki, ni mai son kine da kaunar ki."
Kwankwasa motar akai. Shi ya ja hankalin mu. Glass din yayi kasa dashi.

Ya Nura ne, dariya yayi. Yace,
"Kasan fa jiran ku ango da amarya suke "
"Affuwan kaga wacce ta tsatar damu nan."

Ya fada yana kallon ta, ita duk kunya ta kamata.
"To dai naji ku fito mu shiga." Ya fada yana juyawa.

Kallan ta yayi, yace,
"Muje ko kar kanina ya gaji da jiran yayansa."

Rafar yan dari biyar biyar ba bani guda biyu.
"Kiyiwa Amarya da Ango liki." Ya fada yana fita. Shi ya buden na fito.

Gefen Hauwa nayi. Mu muka shiga da amarya da ango. Anyi ruwan kudi dan ya haidar kamar bai san zafin kudin ba.

Haka ya dinga liku dasu Ya Nura.

Biki yayi kyau daga nan amarya aka mika gidan ta dake rijiyar zaki. Basu da nisa da Hauwa.

Gidan su Faiza muka kwana.

Amarya da Ango bayan anci ansha sukai sallah dan godiya ga Allah da ya nuna masu wannan ranar.
Addu'a sisai Ya Kamal yayi musu na zaman lafiya da zuri'a daiyiba. Daga nan yai mata tambayoyi game da adfini komai ta bashi amsa dai dai gwargwado.
ranar ansha amarci. Sosai suka raya daren su mai albarka.

Washe gari muka hada kayan mu dan tafiya. Amman Momy tace sai gove. Dan yanzu gidan amarya za'a kai mu.

Ni dai raina a bace muka tafi gidan. Dan su Yan biyu a safiyar suka koma dan suna da exam din safe. Sun tafi muna kewar junan mu.

Faiza muka tadda tayi tsaf da ita sai tashin kamshi take ko ina a gyarree.

Hauwa ita taje ta kara jan hankalin Faiza dan ni duk bana cikin tunani na. ina can wata duniya.

Tunani ne tin na ranar daurin aure ke damun kaina. Na rasa ya zanyi ina son naki amince masa amman zuciyata tana sin shi.
Na rasa yadda zanyi lura dani da sukai yasa kuma sukayo Kaina.

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now