56-60

860 47 1
                                    

[11/20, 1:10 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾




Page *56*






Ranar da suka sauka a Nigeria murna kamar me. Jirgi suka kara hawa yai Kano dasu.

Ya Kamal ya kira yazo ya dauke su. har dasu Faiza da Khadija aka zo daukar su.

Gida suka nufa kai tsaye. Su Faiza da Khadija kam sai murna suke dan jiki alhamdulilah.

Ya Kamak nayin packin ta bude da sauri ta fice.

" *Ummu nah!* " ta fara kwada mata kira.

Ummu ce ta fito da sauri ta tari yar ta.

"Hafsat Alhamdulilah jki yayi jyau ko?"
"Eh!"

"Aliyu sannun ku da isowa "
"Yauwah Ummu."

Ciki suka shige, inda aka tare su da. Abinci cika kala kala.

Ya Haidar ne yaci amman ita Hafsat duk hankalin ta na kan Faiza da Khadija.

Gidan Ya Kamal, Ya Haidar yaje, Inda Hafsat kuma ta zauna a gida.

Sai dare taga Baraka. Gaisawa sukai sannan tai mata ya jiki.

Bayan fitar Khadija ke bata labarin komai har da tuban Da Abbi yayi. Sosai Hafsat ta tausaya masu.

Allah sarki Abbi na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana baki daya.

Ba abinda Ummu take barin.  Hafsat tayi, komai yi mata ake.kowa kulawa yake bata.

Abbi har daki yaje ya duba Hafsat. Sam Hafsat bata nuna masa komai ba amman Khadija sam ko kallo baya isar ta.

Sosai Hafsat tai mata fada.
"Khadija mene abin kin yafewa Abbii. Kar ki manta *Mijin Ummun* mune fa.
Mece rayuwar da har zaki kullace sa. Allah nason mai yafiya haka nan in baki yafe masa ba kika san me zqkiyi wani shima yaki yafe miki.
Mece duniyar Khdija in yau mune gobe bamu bane. Ya kamata  ki duba yar sa Khairat yadda Allah ya hade kan mu ya daura mana kaunar junan mu."

"Kiyi hakuri Anty Hafsat in na tuna irin tsanar da hada mun da yake da hada mu da Ummu ne abin yana batan rai.
kiga fa shine silar ciwon zuciyar ki."

"To mene Hafsat wani ma silar mutuwar wani yake, kuma ba da niyyar hakan yai ba. Ki yafe masa kema Allah zai yafe miki."

"Shikenan Anty Allah yafe mana gaba daya."
"Ameen ni nasan zuciyar ki mai yafiya ce."
Suka rumgume juna


Me gyara aka kuma dauko wa dan ta dan kara murje ta. Lokaci guda ta kara canja kala bayan wacce tayo.

Kullum sai Ya Haidar yazo kulawa sosai ya cigaba da bata.

Kwanan ta shida Ummu ta fara hada mata kayan ta.
"Ummu kayan me ake hadawa ne?"
"Kayan tafiyar ki mana."

"Ina zani?"
Kallon mamaki Ummu ta tsaya yi mata. Sai kuma tace,
"Ai kinsan yanzu kina da aure dai to gidn mijin ki."

Idon tane ya kawo ruwa, tace.
"Ummu ni wallahi ban son na tafi na barki."
"Hafsat ai tafiya ta zama dole tinda kowa haka yake tafiya yana barin gidan su. Ki sani aure bautar Allah ne Hafsat. Ki zama mace ta gari a wajen mijin ki."

Kuka Hafsat ta fashe dashi.
"Haba Hafsat mene na kukan. can ma ga Anty Fati nan. Mijin ki na son ki haka itama na son ki,"
"Ummu ni wallahi na fasa aure. Ban son barin ki."

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now