6-10

1.6K 69 0
                                    

[11/20, 12:43 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
6

Writting by MARYAM S INDABAWA
MANS

Dis page dedicated to Zainab Umar Kunya, Allah baki zuri'a ta gari Allah ba baku zaman lafiya ke da mijin. U are my Best friend and Sis love Kunya.


***ASALIN LABARIN***
**********
Alhaji Muhammad haifaffen garin Kano ne, Dan agundi iyayen sa ke zaune amman mahaifin sa haifaffen cikin karamar kumar Rimin Gado.

Yayi auren soyayya da matat sa Hajiya Mariya, inda Allah ya azurtasu da ya'yan mata 2, Hafsat ita ce babba sai mai bimata Khadija.

Alhaji Muhammad ba a kasar nan yayi karatun sa ba, kuma ya karanci harkar kasuwanci, inda yana gama karatun sa ya samu aiki, Allah kuma ya rufa masa asiri ya buda masa, inda har shima ya mallaki kamfanin sa guda 2, daya na kayan masarufi ne, dayan kuma kayan sawa ake masa order daga waje,

Alhaji Muhammad mutumin kirki ne, ga taimakon ma bukata, dan duk asabar da lahadi gidan sa cike yake da mabukata, sannan kk a hanya ya ganka yaga kana bukatar taimako zai taimaka maka.

Hajiya Mariya itama yar nan Kano ce, a nan Gwangwazo, tayi karatun NCE din ta, amman sam Alhaji Muhammad yace bazarayi aiki ba, hakura tayi dan dole, tinda ba abinda ta rasa kawai tana son yin aikin ne dan ta bada tata gudumawar, amman tace, ta koyar wa da ya'yan ta. Alhaji Muhammad yace, duk matsayin karatun da take son yi ya mata alkwari zai taaya mata amman yace aiki dai A'ah, wannan yasa ta koma degree din ta anan (FCE) inda take karantar English language,

Hajiya Mariya macece mai mutum da girmama na gaba, ga tausayi ga fara'a baka taba ganin bacin ran ta,

A yadda gidan Alhaji Muhammad yake, Alhaji Muhammad bai rahe iyalin sa da komai na rayuwa, dan duk karshen wata zai debe ya'yan sa da Matar  duk da alokacin babbar shekarar ta 6 kamar 4, zai kaisu suyi shopping duk abjnda suke bukata zai ce su dauka, haka in karshen sati ne in yana da lkkaci zai dibe su suje wajen wasan yara da washen shakata wa, wani lokacin kuma sukai ziyara wajen yan uwan sa.

Yana son ya'yan sa sosai, Hafsat ita ce yar gidan mahaifin ta wato ABBUn ta haka suke kiran shi, inda ita kuma Khadija yar gida UMMUn suce.

Yaran sun tashi cikin gata da kulawa, gashi mahaifansu na daura su akan tarbiyya ta gari, Makaranta mai kyau yasa su daga Arabi har boko, kuma in sun dawo akwai mai musu bitar karatun nasu, yaran badai kokari ba.

Alhaji Muhammad shine babba a wajen mahaifin sa, sai kannen sa 3, maza 2, Sagir, da Salisu, macen kuma Binta,

Hajiya Mariya ita ce Auta a wajen mahaifan ta, Yayan ta 4, Aisha ce babba sai Ado, Tijjani, sai Fatima,
Tin tana karama a hannun yayar ta Aisha ta tashi, dan ita ta aurar da ita, Alhaji Mahmud sunan mijin Aisha, da ya'yan ta maza 3 Ya Muktar shine Babba sai Ya Kamal sai autan su Ya Sani, duk da sa'an Hafsat ne amman ya girme ta kada.
Aisha na da kishiya, Jamila ya'yan ta 2 Aliyu, sai Usman, zaman lpy ake a cikin gidan bamai banbance tsakanin Ya'yan Aisha da Jamika,

Hajiya Mariya zaman lpy suke mai cike da tsafta da girmama juna tsakanin ta da mijin ta, ga ya'yan su da kullum suke kauna da kula dasu.

Shekarar Hafsat 9 mahaifinta Alhaji Muhammad ya rasu sakamakon wani ciwon ciki da ya tasar masa cikin dare kan suje asibiti Allah ya karbi Abun sa,

Gaskiya anyi rashi sosai, dan jama'a ma kuka suka dinga yi bare kuma ya'yan uwan sa da matan sa da ya'yansa, Hafsat kuwa duk da karamcin shekarun ta tayi kuka sosai dan ta shaku da mahaifin su sosai.

Hajiya Mariya kam sosai ta kwanta jinya dan sai da aka hada da taimakon Allah sannan Allah ya yaye mata ciwon, da dakuwar dake ranta.
Hafsat kuwa in tana zaune sai dai kawai tasa kuka, in an tambaye ta tace, Abbun tah, sosai ake tausaya mata, ayi ta lallashin ta har tayi shiru. Duk lokacin da tayi tunanin sa sai ta sa musu kuka, ranar kuwa ko abincu da kyar take ci sai an ta lallashin ta, kuma sai da taci kayan zaki.*******

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now