11-15

1.4K 59 1
                                    

[11/20, 12:45 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
11

BY MARYAM S INDABAWA

Manzo Allah (SAW) yace duk wanda ya karanta qulhuwallahu Ahad kafa x10, Allah zai gina masa gida a gidan aljannah...
    

Khadija kuma da yake makarantar kwana take nan First Lady, sai anyi hutu take dawowa.

Abbi baya yawan zama a Kano, kullum yana Kaduna, sau yayi wata 2 ko 3 bai zo ba,

Kayan abinci kuwa sai dai Ummu ta siya, kullum tana cikin tashin hankali, na rashin kulawar Mijin ta, amman sai dai suyi ta tayatada addu'a.

Hafsat ba inda take zuwa daga makaranta sai gida, in kunga Hafsat awaje to Abbi ne ya dawo, shima gidan Ya Muktar kadai take zuwa dake bayan layin su, da matar sa Anty Bikki mai mutunci, tana son Hafsat, ko dan aikin da take tayata gashi Hafsat na burgeta. Au iowa ma Hafsat burge shi take dan a nutse taje ga hankali,

In ba can sai  gidan kakanin ta. In ko an bata mata rai to, tana kebe kan ta ne daga cikin jama'a dan kar zuciya tasa tayi abinda ba daidai ba. Wani lokacin ta kanje tyi karatu ko taje wajen shakatawa ta huta, duk da akwai makranta amman haka take tafiyar ta, su Hauwa kuwa ranar basa jin dadi., haka zasu dameta da waya.


Samari masu ji daa kansu, suke bibiyar Hafsat amman kallo basa isar ta, dan ma wasu naganin kwarjinin ta suna kasa tunkarar ta. Amman duk da haka suna takura ta.

Rashin son cin abincin Hafsat shi ya jawi mata Ulcer, wacce in ta tasar mata kamar zata mutu, amman duk da haka bata iya cin abinci mai yawa, ita dai rabu da ita da kayan zaki da sanyi, dan komai sai ta hada shi da suga take sha wanda kuma in wata yayu lokacin al'adar ta take shan wuya sosai, dan wani lokacin har a asibiti take kwanciya, dan fita take daga hayyacin ta sosai,
Ko tace ta daina da ta warke xata manta da tasha wata wahala, Ummu tayi ta mata fada, sai dai ta bata hakuri.

Ummu ganin Abbu na hanata bawa su Hafsat kudi, wannan yasa ta bude musu ma'ajiyar kudi a bakin duk mai buka yaje ya cira, ita ma duk wata take zuba musu kudi. Sosai su Hafsat suka ji dadi.



***************

Yanzu haka Khadija hutu tazo shima kuma a dai dai lokacin yazo gida shine fa ya addabe su, wanda kullum cikin hayaniyar sa.

Yau Asabar, da safe bayan mun tashi nagama komai, na shige daki dan bana son na hadu da Mijin Ummu nah, wanka nayi na shirya, sannan nayi falo, ina zaune Ummu ta shigo na gaidata,

Kayan kallo na kunna, na dauko wayata.
Ummu tace "har yanzu Khadija bata tashi ba ko," "Eh," kawai tace,

Cikin dakin ta shig, tace, "Khadija wai ke bakya gajiya da bacci ne, har karfe 11 kina fama.
Khadija tace, "Ummu ramuwar baccin makaranta fa nakeyi,"  ta tashi. Ta diro daga kan gadon, ta fada toilet tayo wanka,  ta gyara dakin.



Falo ta shigo ta sami Hafsat, tace, "Anty kin tashi ashe," kai kadai Hafsat ta kada mata,
Tace, "ina kwana," "lpy kin tashi lpy," "lpy Anty nah,"

Tea Ummu ta hado mana, sai gasashen bread da nagasa shi da kwai da kifin gwangwani, tean nasha nace na koshi, Ummu tace sai na cinye dan dole na dinga tusawa har da hawaye na.

Ummu kuwa na ta fada, wai shiyasa kullum nake a rame saboda rashin cin abinci na.

Bayan mun gama sai ga Khairat ta shigo, kai tsaye wajena tayo,  tace,
"Taty ina kwana,"
Nace, "lpy lou Baby na,"

Tace, "uhnm Taty Awawa zaki ban nasha,  ni bana son ta wajen Ummu taku nake so,"

Murmushi Hafsat tayi tace, "Baby na kin fiya shan zaki ko?"

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now