Jannah

780 31 13
                                    

"Wake up Angel you'll be late for school" Wata farar mata mai kyakkyawar murya ta furta yayin da take shafa fuskar 'yarta. Sake kallon dakin tayi tana mamakin irin tsaftar 'yarta. Tabbas ta yi dacen haihuwa.

"No momma i wanna sleep please let me be". Yarinyar ta zumbura baki tana boye fuskarta cikin pillow. Murmushi tayi hade da girgiza kai tana me tsananin mamakin yarinyar. Tsawon rayuwarta a duniya, bata taba ganin mutum me tsananin son bacci, da abinci da kuma son jiki kamar 'yarta ba. Sai dai kuma tana da tsananin kuzari da ibada.

"Fine no Starbucks today, no shawarma and pizza for a week, no midnight hot chocolates and sundaes for seven days, no waffles and pastas for an entire week and eating broccoli is a must..." ko rufe baki bata yi ba yarinyar ta mike tana tura baki.

"Hasbunallahu wa ni'mal wakil haba momma this is pure torture wallahi wannan ai malnutrition bazai bar ni ba" Da wuri ta mike tana goge idanunta dan sai a lokacin ta sake jin me take fada. Ita a duniya banda Allah da iyayenta babu abin da tafiso kamar abinci.

"Then go freshen up breakfast will be ready. I'll be the one to drop you kafin in je office so hurry up baby kinji?" Mahaifiyarta ta fada tana murmushi. Sanin cewa tayi nasara akan yarta.

Tana zaune akan gadon har sai da ta tabbata ta shiga wanka kuma taji karan shower kafin ta fita daga dakin. Dan ba karamin aikin Jannah bane tayi bacci cikin bathtub.

"Momma I'm ready" Jannah da cikin mintina kalilan tayi shiri cikin dark blue jeans, pink T-shirt, da bakin rigar sanyi hade da bakin mayafi ta fito tana rike da glass na orange juice. "Kin sha madaranki?" Mahaifiyarta ta tambaya tana kankance idanu.

Zubura baki tayi kamar zata yi kuka. "C'mon Mum I'm gonna be thirteen. I'm not a baby anymore" ta hada fuska tana son yin kuka dan bata son yadda ake sata shan madara wai dan healthy growth. "Then I'm not driving you" Mahaifiyarta ta fada babu alamar wasa.

Ganin saura fifteen minutes nine yayi gashi kuma bazata iya zuwa da kafa ba dan ya mata nisa kuma snow na sauka kuma banda haka baza ma a barta taje da kafan ba yasa tayi saurin shanye glass na madaran sannan tabi bayan mahaifiyarta cikin farar Maserati.

"Bye mamma I love you" ta sumbaci goshinta yayin da take kokarin sauka a motar. "Me too sweetheart take care of yourself and idan akwai wani abu just ring me kinji?" Matar ta fada tana shafa rufaffen gashin 'yarta cike da kulawa.

"Sure" Jannah tayi saurin sauka a motan tana dagawa kawayenta hannu.

•••

"Firdausi Ahmad Jalal" Malamin ya Kira sunanta yayin da yake kiran register. "Present Sir" ta amsa kasa kasa gudun abin da zai biyo baya.

"You were absent yesterday?" Dama abin da take gudu kenan. Ta ina zata fara fada mishi dalilin rashin zuwanta? mutuwan kitten ne ya hanata zuwa? Tabas idan ba so take a bata detention ba to sai dai ta san me zata fada.

"I was down with flu" tayi jibgegen karya. Tabbas da mahaifiyarta na nan zata hana ta shan ice cream da fita outing na weekends biyu sanin cewa ta hana ta yin karya

"You are not lying are you?" Mr Francisco ya tambaya ba tare da ya yarda da zancen ta ba. Dan yasan dalibace me tsananin kwazo amma kuma tana da wasa. "Why would I lie Mr Francisco?" Ta yi abin tausayi tana Allah Allah ya fita. Kawarta Hannan da ke gefenta kuwa sai dariya take yi dan tare dasu aka yi jana'izar kuliyar.

•••

Dawowar Jannah gida ta bude kofar ta shigo a gajiye, tana me tsananin kewar big sis dinta.
"

Assalamu alaikum momma" ta doka sallama tun daga bakin kofa. Da yanzu yayarta Rahma na nan zata hau binta tana cewa 'slow down baby sis' Jannah ta ayyana a ranta.

ILLAR MARAICIOnde histórias criam vida. Descubra agora