POST ONE

370 19 0
                                    


MIKIYA HAUSA WRITERS KADUNA STATE

Almost True Life Story

Basira Sabo Nadabo

PART ONE

POST ONE

Sadaukarwa: Sani Ahmad Giwa

13/08/2019

     BARKAN MU DA SALLAH. TaqabbalAllahu Minna Wa Minkum fans.

KADUNA/ HAYIN RIGASA

Sunana Baseera Bashir Bilal Kawaye na min inkiya da triple B. Na kasance mace mai son ado da kwalliya sannan ina son saurayi dan gaye mai daukar wankan da zan iya shiga da shi cikin kawaye na. Ga ni Allah ya yi ni da son kudi haka ina son zuwa bikin girma da 'ya'yan wane da wane suke halartar bikin, wannan dalilin ya sa bani da kawa 'yar talaka duk da nima Allah bai sa na fito a cikin 'ya'yan masu kudi ba, mahaifina Malam Bashir mai gyaran takalmi ne don da kyar muke iya cin abinci sau uku a rana, d'ayar ma da ya ya ake samun ta balle har uku, wannan ya sa na tsani kaina dana fito a 'yar mai gyaran takalmi, Umma ta surfe ta ke yi a biya ta naira ashirin ko sama da hakan mu uku ne a gurin iyayen mu, Yaya Sani da Yaya Bilal sai ni 'yar autar su kuma ni ce Allah ya yi ni mai dogon buri ga shegen son kudi, ga shi bana kawance da 'yar talaka dai-dai ni don gani nakeyi ajina zai fadi warwas a kasa. Yau ta kama ranar sallah ranar da kowa yake farin ciki da murnar saka sabbin kaya, amma ni a gurina ba hakan bane don bani da abin sakawa, zaune nake a akurkin dakin mu wanda ya kasance ni da Ummata yayin da Abbana da su Yaya Sani dakin su daya. Da kyar muke malejin biyan kudin hayar dakunan guda biyun da muke zaune, kara kallon akwatin karfen da Umma ta bani na zuba kayana a ciki nayi , tsaki nayi mai cin rai daga cikin zuciya ta tsakin ta fito kara tsanar kaina nayi dana fito a gidan talakawa irin Malam Bashir mai gyaran takalmi. Sura da siffar jikina na bi na kalla ba wai nafi kowa kyau ba ne amma kuma ba za a sakani a layin munana ba, sannan ina da diri dai-dai jikina hips dina bayyi yawa ba kuma bai yi kadan ba, ni ba doguwa ba ce kuma ba gajeriya ba, sannan ni ba fara ba, ba kuma za a kirani baka ba, in ina tafiya babu abinda ke jan hankalin maza zuwa gare ni sai yadda kuguna yake juyawa. Ba don ni nake yi da kaina ba sai don haka halittar ta ke, ina da dogon hanci da dan fadaddan baki ba shi da tsawo kuma ba shi da girma, idanuna farare ne tas kamar takarda, ina da gashin ido dara-dara da tsawo haka ma gashin kaina yana da tsayi amma ba har gadon bayana ba, dukiyar fulani na a cike suke dai-dai jikina ni kaina ina na kalla suna birgeni balle kuma maza da yawancin su abinda ke kawo su gurina kenan, ina da son duniya da abinda ke cikin ta amma Allah bai yi ni mai bin maza ba, sai dai d'an abinda ba za a rasa ba kuma ina kiyaye kaina da kokarin kaucewa hakan, ba na saurayi talaka kuma ba na saurayi mai roba-roba sai masu kudi da mota kirar Benze ko Honda EOD, sannan kyakkyawan saurayi ajin farko na shiga biki da kere wa sa'a. Kara kallon kayan nayi don babu wanda zan iya sawa a ciki in fita zuwa in da zani, Umma ce ta shigo tare da 'kare min kallo sannan ta ce.

"Me zan gani haka ke nan Baseeratu?"
      Kallon jikina na fara yi sannan na ce.

"Me kuma na yi Umma don Allah? Kuma ke kullun sai ki dinga ba ta min suna wai Baseeratu haba don Allah!"
    Ta yi maganar kamar mai shirin kuka

"Yo to dama me zan kiraki da shi ko ba da shi ubanki ya yanka miki ragon suna ba?"

"Haba don Allah! Haba yanzu fisabilillahi dan sunan zamanin da ake yayi ma kun kasa samin wai sai tsohon sunan da tuni aka dai na yayin sa wai Baseera, kuma bayan na yarda ina amsawa kuma har da tu kike kara min ni wallahi gidan nan duk kun tsaneni bakwa so na!"
    Sai hawaye sharrrr muryar ta har rawa take yi saboda tsabar bakin ciki, Umma ta tsaya kamar gunki tana kallon ikon Allah ga wani tukikin bakin ciki da ke taso mata ta ce

"Ai bani ce zaki tara da zancen suna ba ubanki me nanin takalmi shi yafi da cewa daki fada masa, domin shi ne ya zaba kuma ya saka miki sunan shiryayyiyar yarinya mai kama da 'ya'yan albarka. Wallahi Baseeratu ki kiyayi duniya wanda bai zo ba ma tana zaman jiran sa balle ke da kika shekara ashirin da hudu a cikin ta."

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now