POST 26

64 11 0
                                    

Duk wani lamba da ta san Badar na amfani da shi gurin adana abubuwanta masu amfani ta yi amma duk da hakan abin bai yiwu ba, sannan ko wani akwati ta gwada da lamar da take tunanin Badar za ta iya sawa mabuɗin akwatin, saboda ta duba sif ɗin gaba daya babu ko da underwear balle pants har banɗaki ta shi ga amma babu shanyayyen pants a ciki, yau in zuciyar Fulani Bilkisu ya yi dubu to duk sun ɓaci domin wankin wula ne zai kaita dare sannan abinda take tunanin zai yiwu ne yake son ba ta wuya, sif ɗin ta kuma dawowa ta sauke kayan ciki gaba daya amma babu ko da sabon pants a ciki, hadimarta ta kira da sauri Jamila ta shigo ɗakin cikin girmamawa ta rissina har ƙasa kanta na kallon kyawawan 'yan yatsun hannunta da suka sha shan fulawa, Fulani Bilkisu ta ce.

"Jamila nasan kin san komai dangane da Badar sannan nasan kin san inda take a jiye kayan sawarta don haka umurni nake baki ki faɗa min inda Badar take a jiye panties ɗinta da sauran kayanta na amfanin yau da kullum."
     A ɗan razane Jamila ta ɗaga kai ta kalli Fulani Bilkisu ta yi saurin saukar da kanta ƙasa sa'annan ta ce.

"Allah ya kara miki nasara da nisan kwana, wallahi uwargijiyata ban san inda uwar ɗakina take a jiye kayan amfanita ba musamman kayan amfanin ta ita kadai."

"Kina nufin duk zaman da kike yi a gefenta baki san inda take a jiyar pants ɗinta ba Jamila? Menene amfaninki kusa da ita? Menene amfanin sa mata idon da nace ki yi? To wallahi ki yi hankali da ni ko kuma na mai da ki ƙasƙantacciyar baiwa a gidan nan."
       Fulani Bilkisu ta yi maganar cikin faɗa da hargowa, jikin Jamila ne ya ɗauki rawa kamar mazari ta ce.

"Don Allah ki rufa min asiri ki min rai Uwargijiyata kece hasken dake haskaka idanuna a cikin gidan nan, kece fitila mafi kyawu ƙawata gidan nan kuma kece rufa asirina a gidan nan Uwargijiyata, in kika kore ni ina zani? Wa nake da shi duk faɗin garin nan sama da ke? Ran kowa ya ɓaci in dai naki zai yi haske, kece uwar sarkin garin nan shi ne a masarautar amma sarautar taki ce uwargijiyata, da na ga ɓacin ranki gwara kaf faɗin masarautar nan su kwana da yunwa in aka cire mai martaba Sameer ki min afuwa daga yanzu zan saka ido a kanta sai dai wani hanzari ba gudu ba uwargijiyata bayan wannan kayan da kike gani wallahi ban taɓa ganin pant ɗin uwar ɗakina a waje ba kullum in za ta saka kaya kulle kanta take yi har sai ta gama muke shiga, kuma ko da shigar muka yi ni dai Jamila ban taɓa cin karo da pant ɗin uwar ɗakina ba har yau da kike tambaya ta."
           Tun da Jamila ta fara magana jikin Fulani Bilkisu ya yi sanyi don ba ta taɓa tunanin wannan ranar zaizo mata ba, da tasan da irin wannan ranar da tun yarinta ta janyo 'yarta a jikinta amma yau ga illar rashin janta a jiki nan, haka ta hakura da neman shi ta koma ɗaki ba don ranta ya so ba......

Lokacin da Fulani Bilkisu take binciken ɗakin Badar a daidai wannan lokacin mutumin da Fulani Aishatu tasa aiki ya fara duk wani abinda yasan uwar ɗakin shi ta sa shi, bai ɓata lokaci ba ya yi komai a cikin ƙanƙanin lokaci ya gama har yabar gidan ba tare da sanin kowa ba.......

Yau ma majalisar Sarki Sameer a cike yake ana ta kawo gaisuwa ana fita a durkushe yake tafiya yayin da kayan jikinsa duk a yayyage suke, gashi duk sun rufe masa fuska makaifansa sun yi tsawo, da sannu ya karasa domin kaima Sarki gaisuwa da kyar ya faɗi gaban Sarki ya yi gaisuwa amma Sarkin bai lura da shi ba har sai da ya ce

"Idan kana zaune a nan kana jindaɗi da kwanciyar hankali to fa karka manta da ranar da asirinka zai tonu da kai da wacce take ɗauraka akan hanyar ɓata, kuma ka tanaji rayuwar wulakanci da tozarci domin da ikon Allah sai ka yi kuka da idanunka kamar yadda kasa ni cikin rayuwar ƙunci da tashin hankali kuma ba zan taɓa gushe wa ba har sai na kuntata rayuwarka da ta mahaifiyarka Bilkisu kuma ina son ka sani duk wani motsinka a kan idona ne kuma a tafin hanuna kake sarauta yau in na ga dama sai in aikaka barzawu, to amma ba zan so ku yi mutuwa cikin sauki da kwanciyar hankali ba kuma mafi kusa da kai bisa umurnina take wakanar da duk lamuranta don haka ka taka a sannu yaro."
         Yana gama faɗan haka ya ɓace ba'a sake ganin sa ba kuma duk abinda ya faɗa a kunnen 'yan majalisar Sarki ya yi, tashin shi akan kujerar karagar mulkin cikin firgita da razana ya yi daidai da farkawarsa daga barcin da yake yi ya jike sharkaf da zufa, duk da sanyin ac da ke buga ɗakin hakan bai hana shi sharce zufar dake gangarowa a jikinsa ba, gefen da Sarauniya Nadiya take kwance ya kalla tana barcinta cikin kwanciyar hankali babu damu wa a tattare da ita, banɗaki ya faɗa ya yi wanka sannan ya dawo ɗakin ya koma gurin da ya tashi ya kwanta amma barcin yaki idonsa dole ya tashi ba don yaso ba ɗakin karatu da nazari ya shiga don rage dare, amma da shigarshi sai yake ganin kamar wannan tsohon mutumin ne a zaune a ɗakin da gudu yabar gurin bai tsaya ko ina ba sai kan gado kusa da Nadiya, rungumarta ya yi amma duk wannan abin da yake faru wa bata sani ba a haka har barci ɓarawo ya yi gaba da shi....

Da salatin ma'aiki ta farka daga nauyayyan barcin da take yi kuma mafarkin da ta yi ya tsorata ainun, banɗaki ta shiga tare da sabunta wanka ta ɗauro alwala, darduma ta shimfiɗa ta fara jero salloli tare da neman agajin Allah bata tashi ba har sai da taji a zuciyarta ibadarta karɓɓe ne a gurin mai duka sannan ta tashi ta dauko littafi mai girma ta karanta suratur Maryam, ba ta tashi ba har sai da ta yi sallar asuba sannan ta koma ta kwanta, ba ita ta farka ba sai sha ɗaya da minti takwas kanta ne ya yi mata nauyi ta dafa kan tare da salati ɗauke a bakinta, kyawawan kafafuwarta ta ziro wanda suka sha jan lallai da baki ta ɗaura bisa lallausar takalminta mai kama da jikin mage, laushi da 'yar tsanar dake jikin takalmin ma abin kallo ne da son kara kusantarsa har zuciyarka ta raya maka taɓa shi, kicin ta nufa domin samun abin da za ta agaza wa cikinta dake neman agaji, ɗakin Fulani Bilkisu ta nufa Jamila na biye da ita tray ɗauke a hannunta a bisa kafet sannan ta yi gaisuwa tabar ɗakin. Kallonta Fulani Bilkisu ta yi sannan ta ce.

"Ke kuma jiya ina kika je nake nemanki.?"
     Mamaki kwance a fuskar Badar sa'annan ta ce.

"Mummy ban fahimci abinda kike nufi da inda naje ba?"

"Eh abinda nake nufi kenan ina son sanin inda kika je jiya."
       Fulani Bilkisu ta yi maganar a umurce, murmushi Badar ta yi haɗe da cewa.

"Mummy kenan ina tunanin tsufa har ya fara sa ki mance cewa ni cikakkiyar likitar mata ce wacce take fita aiki ba don kuɗi ko wani alfahari ba sai don lada da neman lahirarta."
      Sai da Badar ta tunatar da ita aikinta sannan kunya ya lulluɓe ta, ta sassauta murya sa'annan ta ce.

"Tsokana ce irin na ɗa da uwa na yi miki amma ba don ban san aikinki da kuma inda kike zuwa ba, ina sane da irin sadaukarwar da kike yi haka zalika ina sane da irin gudumuwar da kike bawa marayu da marasa galihu, ki ci gaba da hakan 'yata Allah ba zai taɓa baki kunya ba kuma da yarda da ikonsa Allah zai saka miki da mafificin alkhairinsa tun a duniya."
       Daɗi ne ya mamaye zuciyar Badar sa'annan ta ce.

"Amin Mummy Ubangiji yasa kifi karfin abinda yafi karfinki."
      Fulani ta amsa da Amin da babban murya sannan ta ce.

"Badar 'yata niko ina kike ajiye kananun kayanki na mata.?"
    
"Kananun kaya kuma Mummy.? Ni wallahi mummy in na zauna kusa dake sai dai kin san yadda zamu tashi da faɗa yanzu kuma fisabilillahi me zaki yi da kananun kayana Mummy.?"
        Cewar Badar da ɓacin rai ta yi maganar, Fulani Bilkisu ta ce.

"Wai so nake in duba ko kina da bukatar sabbi saboda yaka mata duk bayan wata uku ko biyu ki canja su saboda kiyayewar lafiyarki ne yasa na tambaya."

"Kuma dai mummy! Ni wallahi kin fara bani tsoro zuciyata ta fara zargin wasu abubuwan fa Mummy! Ranar kin ce lokacin period ɗin ina ta kakkaucewa har sai da kika tursasani na faɗa miki, yau kuma Mummy underwear ɗina kike tambaya ni fa wallahi na kasa ganeki Mummy.!"
       Badar ta yi maganar kamar mai shirin yin kuka, murmushin karfin hali Fulani Bilkisu ta yi na ganin wautarta a fili kuma ta yi saurin tambayar da ba haka ta bi ta ba ta tabbata zata faɗa mata komai, amma a fili sai cewa ta yi.

"Ba don komai nake tambayarki ba 'yata sai don kiyaye lafiyarki."

"To amma Mummy kin manta ni likita ce.?"
         Badar ta yi saurin tarar maganar, rasa abin faɗa Fulani Bilkisu ta yi yasa ba ta kara cewa komai ba kuma abin ya fara bata tsoro abinda take tunanin tafi karfinsa shi ke son fin karfinta........

Ni Basiratu 'yar Nadabo na ce "Uhnmm!"


_______________________________


Please share to your family and friends and don't forget to hit that orange star. If you guys do so i will be proud.

Team BasZad
Team BasFad

Karku manta ku biyoni ta wannan handle ɗin domin samun NADAMATA! Part 2 @Basira_Nadabo.

Wannan shafin naku ne 'yan Wattpad Allah yabar muku ni. Amin

#Share and votes

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now