POST 29

59 9 0
                                    

Duk wani ɗan uwa na nesa da na kusa duk sun halarci gidan Mai Faskare kowa ka gani murna ne dauke kan fuskarshi saboda Zaid ya faɗa musu 'yar gidan masu da shi zai aura, kuma 'yar da ubanta yake ganin shigaban ƙasa kai tsaye ba tare da an ba shi izinin hadu wa da shi ba, wannan dalilin yasa duk 'yan uwa na nesa da na kusa halarta bikin Zaid shi kan shi uban gayyar sai gyaran ɗaki yake yi, ba laifi ya gyara ɗakin domin ya canja kofa da window sannan an saka mata roba silip daban-daban daidai karfinsa, kuma ya yi kokarin saka mata fasassun tas a ɗakin da yake ta ce masa tana son fenti mai ruwan ƙasa da fari kuma ko da ya yi dɗakin ya haskaka sosai kwan wutar lantarkin ɗakin ma ba laifi Zaid ya yi kokarin sa ka fari da ruwan shuɗi da an kunna ɗakin zai hau walwali gwanin ban sha'awa, komai ya kammala sauran dangin amarya kawai ake jira su kawo kayan alfarma domin ƙarasa gyaran ɗakin. Habu ne ya zo har gida don su gana da Zaid yako ci sa'ar samunsa a zaune cikin karafaren ɗakin amarya, musabaha suka yi sannan Habu ya zauna kusa da shi haɗe da cewa.

"Babban ango tun kafin zuwan amarya ma ganinka na gagaran mu ina ga kuma amarya ta zo? Nasan sai ka yi wata ma ba ka shiga cikin gida ba in ba wani uzurin gaggawa ko kuma uzurin kanka ko ta amarya ba."
       Murmushi Zaid ya yi sannan ya ce.

"Wallahi abokina abinda yafi ɗaga min hankali kenan, ga shi ko banɗakin wanka banyi ba kuma ka ga ita yarinyar ba ta saba da 'yar tsuguno ba dole sai ta zama irin nasu na 'ya'yan masu kuɗi ban san yadda zai faru ba a ranar da tsuguno ta ka mata a gidan nan."

"Shi yasa tun farkon neman ku nake ba ka shawarar ka nuna mata ko kai waye, da ace ka fito mata a mutum da duk wannan tashin hankalin babu abinda zai dame ka, amma Zaid kaƙi yarda saboda ɗan abinda za ka samu a gurin mahaifinta da kuma ita yarinyar, ga shi yanzu biki sauran sati ɗaya ya rage kuma ko maganar kai lefe ba ka yi amma ya kake ganin za a yi don kare mutumcinka.?"
        Cewar Habu. Zaid ya ce.

"Habu babu abinda za a yi tunda zaman na ɗan lokaci ne kafin in samu kuɗi in kama mana hayar ko da ciki da falo ne."
        Murmushi Habu ya yi tare da girgiza kai sannan ya ce.

"Karfa ka manta 'yar manya ce kuma a ciki ɗaya kuma nan gaba kaɗan ciki da falo za ka kai ta.?"
       Shuru Zaid ya yi sannan ya ce.

"Tun da kai har yanzu ka kasa fahimtar abinda nake son ka fahimta to ni bari na fahimtar da kai, dalilin da yasa zan saka yarinyar nan a ɗakin nan shi ne saboda nasan mahaifinta yana da manyan gidaje na alfarmar masu kiran kansu don tsaru wa da haɗu wa, shi yasa ban ta da hankalina ba gurin ganin dole sai na kama babban ɗaki ko karamin domin ina da tabbacin da munyi aure mahaifinta zai bamu inda zamu zauna, sannan ai kasanta ba ta da kyamar talakawa kuma nasan ba za ta guje ni ba saboda soyayyar dake tsakanin mu."
        Kasa magana Habu ya yi saboda yadda abokinsa ya yi cikin kwaɗayin dukiyar da babu ko naira biyar ɗinsa ciki, amma kuma ya ɗauki son duniya ya ɗaura masa ga shi har buri da karya yasa a cikin auren. Ɓoye mamakinsa ya yi Habu ya ci gaba da cewa.

"Allah ya kyauta, yanzu dai yaushe ne za a kai kayan auren tunda ka ga gidan arziki ne da dattako dole a kai musu lefe da wuri don su duba abinda babu a ciki ala barshi su sun cike maka gurbin gudun 'yan bani na iya."

"A da naso sai bikin ya rage sauran kwana biyu ko uku zan kai musu lefen amma kuma kaima ka kawo shawara mai kyau wata kila in ce akai musu gobe ko jibi hakan ya yi ko.?"
          Cewar Zaid, Habu ya ce.

"Eh ya yi mijin Baseera angon gobe."
       Suka yi dariya suka tafa sannan suka faɗa hirarsu ta kwallo (ball) da ba a iya raba samari har dattijen da shi, basu daɗe da fara hirar ba musu ta kaure a tsakanin su saboda Zaid shi ɗan kungiyar Real Madrid ne, yayin da kuma Habu yake a Barcelona........

Yadda Habu ya ba wa Zaid shawarar kai lefe hakan kuwa ya yi domin bayan maganar su da kwana biyu yasa 'yan uwan shi mata guda uku suka kwaso akwatinan guda biyar da kit, suka zuba a bayan motarsa bai tsaya ko ina ba sai kofar gidan Malam Bashir Bilal Mai Nanin Takalma, duk sun kosa su gansu unguwar masu kuɗi tsayuwar da ya yi yasa ɗaya daga cikin 'yan uwasa cewa.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now