POST 11

65 8 6
                                    

"Kar ka ce min kai ma Badar ta maka ɗiban albarka kamar yadda ta min?"
Saurin girgiza kai ya yi sannan ya zauna a hannun kujerar da ta ke zaune ya ce.

"Mummy wallahi na gan shi, da idona na gan shi ba kuma mafarki ba ne kuma ba gizau ba ne, wannan zahiri ne."

"Haba Sarki kai fa uban kowa ne, bai kamata ka na karaya akan ɗan ƙanƙanin lamarin da bai kai ya kawo ba, kai sai fa ka so zai ƙara kwana a duniyar nan in ku wa ka ƙi dole ya bar duniyar ko da kuwa cikin uwarsa zai koma."
Cewar Fulani Bilkisu.

"Wallahi Mummy ya wuce duk yadda ki ke zato domin na gan shi, kuma ba ganin mafarki ba a zahiri ya zo min, har fada ya shi go."
Cewar Sarki Sameer. Wani shu'umin murmushi Fulani Bilkisu ta yi sannan ta ce.

"Lallai har yanzu kai yaro ne, wai kana tunanin har zai shi go fada kuma a rasa wanda zai gan shi sai kai ka ɗai? Ai wannan zan cen da kunne bai zai ɗauka ba ne Sameer, ka san dai yadda ka sa mu mulkin nan? Kuma na tabbata ka fara ɗanɗan zaƙinta?, ni da ka min kiran gaggawa ma na ɗauka Badar ce ta yi maka rashin mutunshi, tunda ba mutuncin ta gada ba."
Ta yi maganar hankali kwance, ƙuri ya yi mata da ido sannan ya ce.

"Kuma fa maganarki gaskiya ce Mummy wallahi har na ji hankalina ya ta shi, sabo da mulkina na ke dubawa amma yanzu komai ya wuce kuma na gano, a she dai ni ne na ke masa kallo ta fuska da ban."
Da ga nan suka faɗa hirarrakin su na ɗa da uwa.

Wannan Ke Nan

BABI NA UKU

Tun safe ta ke gwada lambar Chocho amma ba ya shi ga, a kalla ta gwada a yau ya kai sau ɗari ko ma sama da hakan, amma duk abu ɗaya ake faɗa mata abin duniya duk sun isheta, ga Zaid sai damunta ya ke da kira, duk dama Zaid ɗin ba laifi ya na da kyau kuma ya na da kuɗi amma dai za ta fi son Chocho ya aureta, yadda su ka fa ra ta re ta na son su gama ta re sabo da babu wanda zai sota a duk yadda ya sa me ta in ba Fahad ba, Umma ce ta shi go ɗakin ta tarar da Baseera ta haɗa kai da gwiwa ta yi saurin taɓo ta haɗe da cewa.

"Lafiyanki ƙalau kuwa?"
Baseera ta yi saurin riƙo hannun Umma sannan ta ce.

"Yanzu Umma ki na kallo fa Yaya Bilal ya ce aure zai min maimakon ki kwaɓe shi sai ki ka bar shi, kuma wallahi tunda dai ya faɗi hakan to tabbas sai ya aiwatar, sannan Umma kina sa ne da Yaya Bilal ba ya magana biyu."
Murmushi Umma ta yi sannan ta ce.

"Baseeratun Umma ki yi hakuri mu ma duk da hakan mu ka fa ra, amma ba ga shi yau ni ce har na ke shirin aurer da ke ba? Don ma kinƙi nutsuwa ne tun farko, da yanzu 'ya'yanki za su kai uku ko huɗu in ba dai kuma haihuwar zamani za ki yi ba."
Turo baki ta yi ta ce.

"Umma ba za ki ga ne abin da na ke hangowa ba wallahi akwai matsala babba, har gwara ku bar ni a gidan nan ban yi aure ba akan abin da nan gaba zai afku, Umma ni kaina ina baƙin cikin wannan ranar, don Allah ki sa baki Yaya Bilal ya bar maganar auren nan don Allah Umma.!"
Ta ka ra she maganar da surnanowar hawaye, da Umma ta ga da gaske take yi sai ta yi saurin jan ye hannayenta da ga na Baseera ta ce.

"Na ga shirme ne duk a maganarki kuma ba ni da lokacin saurarenki Auta, ai ni ma abin farin cikina ne ace yau ina aurer da ke, ko na huta da gorin da ake min a ƙauye kuma ke ma shaida ce duk sa'oinki sun rufa 'ya'yan su, amma ke sai yanzu za ki yi balle kuma kema a sa ran za ki rufa na ki."
Umma ta na kaiwa nan ta yi wa je ta bar Baseera zaune da ƙunan zuci, wanda in da a da ne Umma ta yi maganar nan dariya za ta yi har ta na riƙe ciki wai sa'arta ta rufa 'ya, akasin yau da baƙin ciki ne ya ma ye gur bin dariyarta.

Abba ne ya tattara hankalinsa ga ba ɗaya ya miƙawa Bilal da ke faman rabtako mi shi bayani akan rayuwar da ya yi a makaranta, ya ɗaura da cewa.

"Wallahi Abba watarana ma haka nake kwana ban ci na safe ba balle na dare, wani sa'in ma ruwan da zan yi wanka da shi gagarana take yi, haka zan daka tsami in fesa turare in je aji don kawai na ɗauki darasi kuma a sa sunana a waɗanda su ka zo a ranar amma ba don ina fahimtar abin da ake koyar damu ba."
Jikin Abba ne ya yi sanyi sannan ya ce.

"Amma Babana me yasa ba ka dawo gida ba tun da karatun ba dole ba ne, kuma ba'a haɗa yunwa da komai musamman karatu ba'a karatu da yunwa, ba ka ji an ce ko sallah za ka yi in dai ka na jin yunwa kar ka yi ba? Har sai ka ci abinci ba? To haka karatun ma ya ke."
Murmushi ya yi sannan ya ce.

"Abba idan na dawo gida wannan shekarar da na yi a gida zan ƙara maimatawa, kuma kila wahalar ma ta ninka wanda na gudo domin ta, wannan muke tuna wa yake sa muke ƙin guduwa a makaranta."

"Oh! Ku kuma kalar taku karatun ke nan? Mu dai mun gode Allah da yasa mu ka yi na mu ba mu sha wahala ba, har na gama mu ai karatun daɗi mu ka yi irin na 'ya'yan masar......"
Sai kuma bakin shi ya sarƙe tari ya ka ma shi, da sauri Bilal ya ba shi ruwa ya sha sannan ya ce.

"Abba irin na 'ya'yan me ka ke son faɗa?"
Girgiza kai ya yi sannan ya ce.

"Irin na 'ya'yan masarafan takalma sabo da kasan mu a lokacin mu karatun mu da ban ya ke da sauran yaran garin mu, sabo da duk zuri'ar mu mun fi mai da hankali a karatu ko 'ya'yan mai gari babu a makarantar, sabo da mu gidan mu masarafar takalma ne babu kalar da Babana ba ya sarrafawa har turawan wan cen lokacin ya yi musu takalmi, wannan yasa sunan gidan mu ya ɗaukaka 'yanmatan gidan mu ba sa daɗewa ba su yi aure ba, shi yasa ka ga yanzu ban son Baseera ta je ƙauye sabo da magana irin na mutanen ƙauye akan ta yi kwantai ta za ma gantsantsan babu aure."

"Ai In Sha Allahu lokacin auren Baseera ya yi Abba, ko ni abin ya na damu na ace yarinya kamar wannan ba ta yi aure ba, haka lokacin da na ke makaranta dubu hamsin ta turo min Abba."
Cewar Yaya Bilal. Abba ya yi saurin cewa.

"Dubu hamsin Babana.!"
Ya yi maganar da rawar murya, Yaya Bilal ya gyara zama sannan ya ce

"Abba ka iya tuna lokacin da na ce maka bani da komai a makaranta hatta abincin da zan ci ya gagare ni?"

"Tabbas na tuna don a lokacin ma rasa abin siyarwa na yi yasa na zubawa sarautan Allah ido, da dai kuma na ji ka yi shuru ba ka ƙara min maganar kuɗiin ba sai na yi tunanin ko an fasa yin abin da za'a yi da kuɗin ne."
Da sanyin murya Abba ya yi maganar, Yaya Bilal ya ɗaura da cewa.

"To Abba a 'yan tsakakkanin lokacin ne ta turo min da kuɗin, da na yi magana da Yaya Sani sai ya ce min adashinta ne ta amsa don siyan 'yan kayayyakin su na mata, in auren su ya ta shi shi ne ta ji kana maganar kai da Umma, da ta ga bukatar ta wa ta fi na ta sai ta hakura da siyayyar ta turo min da kuɗin."

"Allahu Akbar Kabiran! Lallai Baseera ta gwada min kai fin basirarta kuma ta yi abin da Annabi (SAW) ya ce a yi, shi ta yi, na tabbata ko mahaifiyarku ba ta san da wannan zan cen ba domin in da ta sani to tabbas za ta sanar da ni, ta yi aikin da ko hagunta bai san ta aikata ba, Allah ya yi miki rahama Baseera ya kare min ke da ga dukkan baƙin cikin da zai fuskantoki a yanzu ko a gaba har karshen rayuwarki Autata, da ku ma ga ba ɗaya.
Su ka amsa da Amin, sannan su ka ci gaba da hirar su amma alkhairin da Baseera ta yi ya na maƙale a zuciyar Abba ya kasa mantawa.

Wannan Ke Nan

Zaid ne zaune yau tun safe babu wanda ya kawo gyaran mota ga shi ya na son ganin Baseera a yau ɗin, sabo da ya kwana biyu ba su haɗu ba, abin duniya duk sun haɗu mi shi goma da ashirin, waigawar da zai yi ya ga hancin EOD fara sai ɗaukan ido take yi a fili ya furta.

"Alhamdulillahi!"

_______________________________

Hmmm comments ya na min kaɗan gaskiya ku ƙara yawan comments in ƙara yawan typing shi ke nan.

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now