POST 18

69 10 4
                                    

Hawaye ne suka surnano a idonta ta yi saurin sharce wa sannan ta ce.

"Wallahi Abba duk abinda zan yi ba zan taɓa baku kunya ba, kuma ba zan taɓa yin abinda zai zubar da ƙima da mutuncinku ba, Zaid ne wanda zai aureni ya siya mana gidan a lokacin da Malam Mamman ya taso ka gaba kan maganar gidanmu har yake cewa zai kore mu, shi ne da na ba shi labarin halinda muke ciki sai ya ce in raka shi gurin Malam Mamman to nima ban yi tunanin siyan gidan zai yi ba amma da muka je sai na ga ya biya kuɗin gidan kuma ya ce ya mallaka mana gidan kyauta, tsoro da fargabar abinda zan haifar maka ne yasa na kasa faɗa maka maganar gidan, saboda na sanka da gudun abin hannun mutane kuma ina tunanin za ka ce nice na roke shi ya siya mana gidan wannan dalilin ne yasa ban faɗa maka ba Abbana, don Allah ka yi hakuri hakan ba zai ƙara faru wa ba wannan ma kuskure ne na yi ba zan ƙara maimaita wa ba da yardan Allah.!"
      Ta karashe maganar da rawar murya, sauke ajiyar zuciya ya yi har sai da ta kalle shi sannan ya ce.

"Ke 'yata ce wacce nafi so duk cikin 'ya'yana ba zan taɓa son abinda zai taɓa mutunci da martabarki ba Baseera, ban taɓa zarginki ba haka ban taɓa miki kallon wata halitta da ban ba sai dai ina gudun abinda zai je ya dawo ne sannan maganar gida kuma ban ji daɗi da kika yi gaban kan ki ba saboda shi saurayin zai miki kallon maroƙiya ko kuma ya yi mana kallon maƙasƙanta masu son abin hannun sirikansu, wannan dalilin ne yasa kika ga raina ya ɓaci amma tunda abinda ya faru ke nan bakomai Allah ya ki ya ye gaba tunda wannan dai ya faru."
         Haka suka ci gaba da hirarraki har suka isa Mariri saboda sanin zuwansu yasa samarin kofar gidan saurin taso wa daga in da suke zaune suka nufo in da motar ta tsaya, tsayuwar motar ta yi daidai da fito war Goggo Hansai.
        Goggo Hansai amaryar Sarkin Takalma ne sannan tsohu ce irin tsoffin nan ma su son abin duniya da karyar arziki in dai kana da shi to za ta yi da kai, amma in har baka da shi bata da babban maƙiyi sama da kai, wannan dalilin ne yasa basa shiri da Abba Mai Nani ko fito war da ta yi da biyu ne don ganin dame suka zo, taɓe baki ta yi sannan ta ce.

"Hegu faƙirai waɗannan ko ɓeran masallaci ya san da zaman su ko kunya babu su taso tun daga garin gwauna har Mariri ko kuli-kulin naira biyar 'yar ban za basu iya kawo mana ba sai dai mu a barmu da jigilar ciyar wa."
      Ganin su Mati na kokarin fito da buhu a bayan mota ne yasa ta yi saurin fito wa tare da cewa.

"Lale-lale da mutanen garin gwauna, lale mazajen da ba cefane, lale-lale kishiyata Baseeratu matar gwauna."
     Da harara Baseera ta bita saboda tuntuni sun san Goggo Hansai ba ta sonsu take yi ba haka kuma ta tsanin ganin su a garin wannan dalilin ne yasa Baseera ita ma ba ta raga mata, Umma ce ta yi saurin taɓo Baseera saboda ta ga lokacin da take aikawa Goggo Hansai harara ta ce.

"Don Allah auta kar ki ja mana abin zagi daga zuwan mu saboda ba kan ki abin zai sauka ba kaina komai zai dawo, don Allah ki ta yi kokarin rabu wa dasu lafiya."
       Daidai kunnenta Umma ta yi maganar, saurin sake fuskarta ta yi sannan ta ce.

"Lale Goggo Hansai."
        Cewar Baseera. Ta yi maganar haɗe da rungumar Goggo Hansai ita ma Goggon ta yi saurin rungumarta har tana kara tsawon kafarta, Yaya Sani ne ya tsuguna har ƙasa ya gaisheta amma Yaya Bilal ko arzikin kallon ba ta samu ba balle ta yi tunanin za ta samu  gaisuwa a gurin shi. Ta ce.

"Sarkin Takalmi yau sarautar ne suka motsa to ni bari na kawo gaisuwa."
       Ta tsuguna har ƙasa haɗe da cewa.

"Ina wunie ranka ya daɗe kun iso lafiya?"
      Bai juyo ba balle ya amsa har sai da Abba ya nuna ɓacin ransa sannan ya amsa gaisuwar amma fuskar nan a haɗe kamar hadari, har ƙasa Abba da Umma suka tsuguna tare da gaisheta ta amsa cikin fara'a da sakin fuska abinda bai taɓa faru wa ba ke nan tun da suke zuwa, cikin gidan suka shi ga kowa sai maraba yake musu Inna Aishatu dai ba ta ce komai ba saboda alkunya irin na ɗan fari kasance war Abba Mai Nani ne ɗanta na fari sai mata biyu da suka biyo bayan shi Hajjo da Mairo, Inna Mairo ta rasu tun bayan haihu war Baseera da kwana arba'in da uku sun yi kukan rasuwarta saboda duk cikin dangi ita ce mai faran-faran da mutane ga son mutane kamar Sarkin Takalma sannan sunfi shaƙuwa da Abba, Baseera ce ta ƙarasa kusa da Inna Aishatu ta ce.

"Tsohuwa mai ɗan ƙoƙo Allah kashe ki mu ci gumba."
       Ta ka ra she waƙar da dariya ita ma Inna Aishatu dariya ta yi, Baseera ta ci gaba da cewa.

"Wai har yanzu kunyar ce kike yi? Na dai faɗa miki ni ba 'yarki ba ce ki daina wannan kunyar a kaina."
      Murmushi Inna Aishatu ta yi sannan ta ce.

"Allah shi ne zai shirya min ke har yau ba ki canja ba ni dai ina faɗa miki ni ba kakarki ba ce, Hansai da Lami sune kakanninki amma ba ni ba."
    
"Allah ya kyauta in zama jikarsu ni ke kaɗai ce kakata mutanen da ba sa son mu sannan suke baƙin cikin numfashin da muke yi, shi ne za ki ce ni ce jikarsu?"
     Cewar Baseera, girgiza kai Inna Aishatu ta yi ba ta kuma cewa komai ba haka dai hirar ya tsaya a tsakanin su, don dama hirar ba ta yin tsawo a tsakaninta da jikokinta Baseerar ce ma mai janta da hira ko ba ta so sai ta tamka wannan dalilin yasa Inna Lami da Gaggo Hansai ba sa son zuwarta don ba ta ɗaukar rainin da a ke wa Inna Aishatu.

Wannan Ke Nan

Sai duba ƙasar yake yi amma a bu ɗaya yake gani hankalin shi ya yi mugun tashi, karkkaɓe hannunshi ya yi tare da yin tofi a hannun sannan ya ƙara mai da wa cikin ƙasar amma abin da ya gani da farko har yanzu shi ɗin dai yake gani, a karo na farko da ya buɗe baki ya ce.

"Gimbiya Bilkisa akwai a bu gagarimi dake dunfaroki ke da ɗanki Sameer sannan da sa hannun na kusa dake ne hakan zai faru, domin sai da taimakon wanda yake kusa dake zasu samu nasara har su yi galaba a kan ki to amma abin da na kasa gane wa shi ne wanene wannan mutumin? Ga shi dai yana nuna min kamar mace ce kuma kamar namiji,  jinsin halittar ne har yanzu na kasa banbance wa, amma na fi kyautata zaton mace ce domin da mayafinta sai dai na kasa gane fuskarta saboda lulluɓe take da bakin mayafi kuma wannan bakin shi ne bakin ranar da take nufo ki Gimbiya Bilkisa."
      Shuru ta yi tana dogon tunani a kan wanda ya fi kusanci da ita da har zai iya sa hannu a tona mata asiri sannan ta yi saurin cewa.

"Badar! Hakiƙa Badar ce ka ɗai za ta iya sa hannu a tona min asiri saboda ta sha faɗa min za ta tona min asiri a kan abinda nake yi, tabbas Badar za ta iya yin komai don ganin ta juya min baya."
      Kuri ya yi mata da ido kafin ya fara bubbuga ƙasar ya ɗau minti talatin yana duba wa kafin ya ce.

"Bana tunanin za ta iya yin hakan amma tunda kin ce haka shi ke nan, zan yi aiki a kai bisa sharaɗi guda ɗaya in kin yarda da sharaɗin sai na faɗa miki."
     Ba tare da tunanin abinda zai je ya dawo ba ta ce ta amince.

"Zan kulle bakinta har illa masha'a amma ki sani duk ranar da a ka tone wannan abinda kika sa 'yar tsohuwa binne wa to a wannan ranar asirin da a ka yi wa Badar zai koma kan wanda ya yi, sannan mutumin zai haukace tare da zama mutum mutumi kamar yadda a ka mayar da Badar, kin yarda da hakan? Idan kin yarda yanzu a gabanki zan rufe bakin Badar babu mahaluƙin da zai ƙara jin ko da tarinta ne balle har a kai ga jin magana a bakinta, babu ke babu fargabar abinda ka je ka dawo don mun yi maganin matsalarmu Gimbiya Bilkisa, kin yarda na yi wa 'yar da kika haifa asiri? Asirin da in har ba a tona asirin da a ka binne ba a haka za ta zauna har karshen rayuwarta, aure ba na ta ba ne sannan babu ke babu ƙara ganin dariyar 'yarki to amma a wannan ranar da asirinki zai tonu ki sani 'yarki ba za taji tausayinki ba balle kuma har ki yi tunanin za ta taimaka miki, domin wannan tsanar da ke tattare da asirin zai dira a zuciyarta kuma tsanar kan ki za ta koma Gimbiya Bilkisa, duk da hakan kin yarda kin amince in yi wa 'yarki asiri 'yarki wacce tafi jin ƙanki da tausayinki 'yarki da kullum take burin ta ga kin dawo hanya ma daidaiciya, wacce take son ganinki cikin farin ciki, kin yarda Gimbiya Bilkisa.?"
       Cewar Malam Zailani, shuru ta yi tana tunani a ya yin da zuciyarta suka rabu gida biyu musulmin zuciyar na gargaɗinta a kan kuskuren da za ta tafka amma ɗayan zuciyar kuma tu ni yake mata da in har tabar Badar to tamkar ba razana ce ga rayuwarta, haka zuciyoyinta suka ta tafka muhawara kuma har yanzu ta rasa gane wanda za ta bi saboda duk guda biyun hujjojinsu masu ƙarfi ne.


_______________________________

Wattpad @Basira_Nadabo


Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now