POST 27

69 10 2
                                    

"Ummu Aishatu wallahi tun ranar da aka sa bikin Auta ban kara samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyata ba, saboda kina sane bamu da komai kuma babu abinda muka ajiye koda cokalin roba ne, bani da hanyar samun sa kuma ban san in da zan samo ba.!"
       Mai Nani ya karashe maganar da raunin murya. Jikin Umma ya yi sanyi saboda damuwar da Mai Nani yake ciki tana ganin ma har ta fi shi saboda itace za a barwa abin gori a dangin miji, sauke nauyyyan ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce.

"Malam a yadda nake jin zuciyata kai baka kaini bakin cikin wannan al'amarin ba saboda ni ce mace ni ce nake zaune a gida kuma ni ce nake tare da mata, ka ga kenan kananun maganganu ne zan sha sai dai kawai na toshe kunne amma kuma inda gizo ke sakar shi ne Baseera Malam! Auta zata iya kin auran nan a dalilin rashin kayan ɗaki."

"Ni kaina damuwar dake gabana kenan Baseera don in ta falle babu mai iya kamota amma bakomai da kunyar lahira gwara na kiyama ko da tabarma ne zan siya da 'yan kayayyakin aiki na cikin gida, in yaso daga baya sai in bata ɗan abinda ba za'a rasa ba ta cikeshe gyaran ɗakin ko ya kika gani?"
     Cewar Abba Mai Nanin Takalma, shuru Umma ta yi kafin daga bisani ta ce.

"A gaskiya Malam da matsala!"

"Hakuri za ta yi Aishatu saboda bikin fa yau sauran kwana ashirin da takwas kuma babu abinda muka ajiye dangane da bikin."
     
"Shi yasa tun farko nace a ce musu mun ɗaga zuwa nan da wata biyu ko uku amma Malam kaki yarda kuma duk irin faruwar wannan lamarin nake gudu ga shi abinda ake gudun ne zai afku."
     Cewar Umma.

"Hakurin dai shi ne duka zamu haɗu mu yi amma Allah ya sani bani da abinda zan kai Baseera da shi gidan miji."
       Mai Nani ya yi maganar da sanyin murya, tausayin Mai Nani ne ya kama Umma hawaye ne suka cicciko a idonta ta yi kokarin mai da shi sannan ta ce.

"To mu kokarta ko katifa ce mu sai mata gudun gori Malam.!"
      Shuru ya yi sa'annan ya ce.

"Ubangiji ya rufa mana asirin da zuma rufa mata asiri amma gaskiya ko ni ba zan ji daɗin kaita da katifa babu gado ba, amma tunda haka Allah ya tsara min rayuwata babu yarda zanyi bani na ɗaurawa kaina talauci ba kuma ban jin daɗin zama cikin talaucin to amma babu yarda zan yi Aishatu haka Allah yaso ganina kuma na amsa hannu bibbiyu da biyayya, Ubangiji dai yasa kaffarar rayuwarmu kenan duniya da lahira.!"
    Kuri Umma ta yi masa cikin tausayawa rayuwar da suka tsinci kansu sama da shekara talatin da biyar kenan ana abu ɗaya babu jin daɗin rayuwar aure.

"Na sani mijina karka karaya da jarabawar da Ubangiji yake maka wata kila yana maka tanajin rayuwar jindaɗi a nan gaba kaɗan Malam, amma ka yi hakuri da halin da katsinci kanka a ciki komai da sanin Allah.!"
        Da rawar murya Umma ta karashe maganar, janyota jikinshi ya yi yana bata baki har ta dawo cikin nutsuwarta ba wai don nashi zuciyar babu zafi bane ko kuma bai masa ƙuna akan halin da Baseera za ta shiga idan ta buɗi ido babu komai a ɗakin aurenta ba ne amma haka ya daure yake rarrashinta..........

      Sallamar da almajirin ke yi ne ya tasota daga barcin ranar da take yi da muryar barci ta amsa sallamar, sannan yaron ya shaida mata da ana sallama da ita a waje ko da bata tambaya ba tasan Zaid ne saboda yau kwana huɗu kenan ba ta kunna wayarta ba, kuma saboda Chocho yasa ta kashe wayarta domin a 'yan kwanakin nan ko ince tun ranar da aka kawo sadakinta ya fama mata mi ƙin dake zuciyarta sannan ya kuma jaddada mata shi ɗin dai zata aura domin yana dawowa daga tafiya zai fito gidansu asan da shi dalilin da yasa kenan taki kunna wayarta, gyara kanta ta yi sannan ta dauko wani material mai kyau da tsada tasa feshe jikinta ta yi da turaruka daban-daban masu sanyin kamshi, gyalanta tasa kalar kayan sannan ta dauko slippers shoe mai kyau ta zura dogayen kyawawan kafafuwarta ciki, sallamar Umma ta yi da ta fito a ɗakin Abba kallonta Umma ta yi koma komai ta ji daɗin ganin Baseera cikin walwala da annashuwa. Zaune yake cikin bakar mota yasa farar shadda mai ratsin baki-baki a jiki, kalar kayan da ɗinkin zamanin da aka masa suka ƙara fito da cikar haibarsa, tun da ta fito daga gida take kallonsa shima kallonta yake yi yana kara salati da girmama zatin Allah da ya halitta wannan kyakkyawar baiwar domin shi kaɗai, kwankwasa gilashin motar da ta yi ne ya dawo dashi daga duniyar gajimaren tunanin Baseera, zuge gilashin ya yi fuskarshi ɗauke da murmushi ya ce.

"Barka da fito wa sarauniyar da tafi matar layin su kyau da fasali."
     Zagayawa ta yi zuwa kujerar mai zaman banza ta zaune sa'annan itama da fara'a ta ce.

"Lale da zuwa masoyina farin cikina haƙiƙa nafi ko wacce mace sa'ar samun miji mai nagarta da haiba, mijina kana da kyawun da inka fito mata za su ta tuntuɓe gurin kallon kyawunka,  babban burina da kuma fatana shi ne Allah ya nuna min ranar da zan zama matarka, a wannan ranar zan nuna maka soyayyar da baka taɓa tunani ba haka zalika zan shayar da kai zumar soyayyata."

"Yau sauran kwana ashirin da takwas ta mallaki komai da ya fito daga gareki sahibata, na tanaji duniyar da zan kaiki domin more amarcinmu, ba za ki taɓa dana sanin aurena ba haka kuma ba za ki taɓa gajiya da ni a kusa dake ba abar kaunata."
      Da murmushi ya yi maganar, Baseera ta ce.

"Na ga har farin ciki kake yi yau sauran kwana ashirin da takwas aurenmu bayan ni ganin kwanakin nake yi tamkar shekara ashirin da takwas ya rage mana."
      A shagwaɓance ta yi maganar, shagwaɓarta ya kara narkar da zuciyarsa har bai son sanda hannunshi ya kamo nata ba, ba ta hanashi ba kuma ba ta ce dashi ya janyen hannun ba, murza hannun ya yi sannan ya ce.

"Bassylurv na tabbata yadda hannunki yake da taushi da ruwa gurin rike wa haka kema zaki kasance mai tau......"
    Ta yi saurin dakatar da shi da cewa.

"Bai kamata don zaka aureni ya zama irin wannan zan cen zai dinga fito wa bakinka ba, biyan sadaki ko sanya rana ba shi bane aure, jira za ka yi har ranar da na zama matarka sannan ka yi yadda kaga dama dani amma ban da yanzu."
      Ta yi maganar haɗe da janye hannunta a cikin nashi hannun har cikin ranta ta ji daɗin kalamansa da kuma rike hannunta da ya yi to amma yin rigakafin da ta yi shi zai kara mata daraja a idon Z Guy. Jikinsa ne ya yi sanyi sannan ya ƙara tabbatar wa kansa 'yar mutunci da martaba zai auro kuma uwar 'ya'yansa sannan kuma 'yar masu kuɗi da rufin asiri, farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa amma a fili sai cewa ya yi.

"Ki yi hakuri ban yi hakan da wani manufa ba kuma ba wai na taɓa hannunki don yin fasiƙanci dake ba ne, sai dan jin daɗin tafin hannunki kuma inda fasiƙanci zan yi dake Bassylurv da ba zan taɓa zuwa gidanku har da maganar aure ba amma ki yi hakuri babyna."

"Ka yi hakuri in kaji haushin abinda na yi maka amma mutuncina nake kare wa da kuma martabar gidanmu."
        Cewar Baseera

"Yaushe Daddy zai dawo tunda bikin ya zo.?"
        Ya yi maganar yana washe baki, gabanta ne ya faɗi amma a fili sai cewa ta yi.

"Ko da wani lokaci daddy zai iya shigo wa ƙasar nan amma mun yi waya ɗazu yake cemin kafin biki zaizo, yauwa ai kasan ƙannen Mummy suna Saudiyya ko? To ɗazu  suka dawo daga Saudiyya kai da kanka in ka ga kayan da suka siyo sai abin ya birgeka."

"Ma Sha Allahu gaskiya daddy ya yi kokari sosai saboda kuɗin jirgi ma ai babban kuɗi ne balle kuma kayan da za a siyo daga can amma ba yau suka dawo tare da kayan ba ko.?
      Da zaƙuwa ya yi tambayar. Ta ce.

"Eh gaskiya sun riga turo kayan kafin daga baya suka biyo jirgi suka dawo shi ne suka zo lokaci ɗaya da kayan."

"Aina san dama sai dai hakan saboda nima duk kayan akwatinki hakan na yi,  shi yasa na yi miki wannan tambayar."
       Murna ce fal kwance kan fuskar Baseera ta yi saurin cewa.

"Ina fatan ba ka samin ƙananan kaya ba saboda ko a gidanmu daddy bai barmu mun saka kayan da zai ƙasƙantar da darajar gidansa ba."
  
"Duk kayan da na saka miki Bassylurv babu na ƙasa da ashirin saboda girmanki ne yammata kisa babban kaya domin kin fito a babban gida."
     Daga haka hirarta su ta ci gaba ko wanne na faɗan irin kayan alatun da yake tanadarwa ɗan uwansa........

Wannan Ke Nan

_______________________________

Team BasZad
Team BasFad

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now