POST 25

62 8 0
                                    

A yau ne Baba Mai Faskare da Baba Harisu kanin Mai Faskare zasu kai kuɗin auren Zaid da Baseera, tun safe Zaid ya kasa nutsuwa farin ciki ya mamaye zuciyarsa a yayin da annurin fuskarsa suka ƙara ƙawata fuskarsa, sai dai inda gizon ke saƙa shi ne babu motar da zai kai Mai Faskare gidan su Baseera kuma a nashi tunanin zuwansu a mashin mai ƙafa uku kamar zubar da kimarsa ne da kuma rage masa girman daraja a idanun kawun Baseera, wata dabara ce ta faɗo mishi da sauri ya ɗauko wayarsa dake can nesa da shi ya latsa lambar Habib, Habib abokin aikin Zaid ne sai dai shi bai sa rayuwar ƙarya a sana'arsa ba shi yasa Allah ya buɗe masa hanyoyin samu, a girma da iyawa Zaid ya fishi girma a gurin aiki kuma ya fishi iya gyaran mota sosai amma shi Zaid da yake ƙarya ce gabansa babu abinda ya a jiye gida ko mota akasin Habib da a yanzu motar kansa yake hawa sa'annan yana da rabin filoti a Hayin Dan Mani, daga can ɓangaren Habib ya ɗauki wayar da sallama Zaid ya ce.

"Abokina ka yi kuɗi ko neman talaka baka yi."

"Wane ni ai kuɗi saiku Oga Zaid tun da ga shi har daina zuwa gurin aiki ka yi saboda kaci ka tada kai da shi."
       Cewar Habib, murmushi Zaid ya yi sannan ya ce.

"Alhamdulillahi, Habib mun gode wa Allah dama wani ɗan taimako nake nema a gurinka in zan samu.?"
         Habib ya ce.

"Wani irin taimako kenan Oga Zaid? Kuma Allah yasa na yi maka."

"Mota zaka aramin in babu damu wa."
        Shuru Habib ya yi na wasu 'yan daƙiƙu sannan ya ce.

"A gaskiya Oga Zaid motata ta samu matsala yanzu haka tana gareji a zaune to amma akwai wata mota da na amsa aikinta kuma yau muka yi da mutumin yazo ya amsa, tunda kaine Oga Zaid zan ce masa ya bari sai gobe alabarshi zuwa anjima sai na kawo maka motar."
        Bakin Zaid har kunne ya yi ta godiya sannan ya faɗa mishi lokacin da zai kawo masa motar kuma ya tabbatar masa da babu abinda zai hanashi bashi motar sai Ikon Allah.......

Tun safe Yaya Sani da Yaya Bilal suke ta faman gyare-gyaren gidan saboda tarban bakin da zasu kawo kuɗin auren Baseera, Umma kuma abinci take yi a yayin da Baseera take zaune a ɗaki abin duniya duk sun dame ta musamman da yanzu suka gama waya da Chocho kuma yake ƙara shaida mata ta rike alkawarinsa domin ya kusan dawowa kuma da ya dawo zai shigo gidansu don a san da shi, amma duk ba wannan yafi ɗaga mata hankali ba, domin ba tajin ta Chocho saboda tasan yadda za ta tafiyatar da shi abinda ya tsaya mata arai kuma ya hanata sukuni shi ne tunatar da ita kyautar abu mafi girman daraja da ta yi masa a watanin baya sannan ya kara da cewa babu na mijin da zai aureta har ya darajata saboda duk wani namiji burinsa kenan ya samu matarsa cikakkiya, amma ita dai shi ne ya dace da ita kuma dole shi zai aureta don haka ta shirya ma aurensu da ya dawo.

'Yanzu in Zaid ya same ni ba a budurwa ba fa me zai faru? Wani kallo zai min 'yar iska ko karuwa? Me zance da su Abba da Umma a lokacin da suka ji abinda ya faru da ni? Waima Zaid zai iya rufa min asiri kuwa? Ko zai tona min asiri ne duniya tasan haƙiƙanin abinda ya faru da ni? Ummata fa? Abbana da su Yaya Sani na tabbata kashe ni zasu yi, wayyo Allahna Fahad ka cuceni ka gama da rayuwata shi kenan na mutu na lalace.'
       Kukan ya zo mata da karfi yayin da take maganar zuci har sai da Umma tabar abinda take yi ta karasa gurinta da gudu da shigarta ɗakin ta samu Baseera durkushe tana kuka kamar ranta zai fita, tambayar duniyar nan Umma ta mata amma bata iya buɗe baki ta bata amsa ba haka ta fita da sanyin jiki don ita a tunaninta maganar auren da za a yi ne yasa ta kuka bata son rabuwa da su, Umma ta koma kicin tana sharce hawayen da suka surnano mata tausayin 'yarta yaka mata, ba dan tasan auren shi ne daidai ba kuma sunnan Annabi ne (S.A.W) da yau tasa an bar maganar auren har sai ta ɗan ƙara girma don a yanzu take ganin kankantarta da aure amma aikin gama ya gama don babu abinda zai sa a fasa auren nan sai Ikon Rabbi, sharce hawayen da ya surnano mata ta kuma yi sannan ta ci gaba da aikinta ba don daɗin rai ba sai don babu yadda za ta yi ne haka har ta karasa aikin...

  (Dama Takwara Baseera baki shiryawa wannan ranar ba kika wulakantar da jikinki? Ko kuma kina tunanin abinda ya fita zai dawo ne? Dama hausawa suka ce mutunci madara ne in ya zube bai taɓa kwasuwa, Ko kuma mune muke miki kallon bai bai ba a daidai ba kece a kan daidai? Hmmm mu dai 'yan kallo ne.)

Da misalin karfe biyar ta yamma bakar Camryn da Zaid ya ara ta tsaya a kofar gidan Malam Bashir Mai Nani, wayar Baseera Zaid ya kira amma a kashe dole ya hakura da kiran ya samu yaro ya aika a kirata, ba don taso ba kuma ba a daɗin ranta ta fita ba duk wannan abin da take yi Umma tana lura da ita sai dai ta bita da addu'a kawai don ta lura yau 'yarta tana cikin damu wa kuma babu wanda zai fitar da ita dole ta hakura a yi auren tunda itace ta kawo shi, a kofar gida ta tsaya da ta lura da mutane cikin motar cikin gidan ta koma ta faɗa wa Umma su Zaid ne suka zo daga hakan bata kara kalma ko ɗaya ba ta shige ɗaki ta kwanta zuciyarta tana mata ƙuna, sanar da zuwan nasu Umma ta yi Yaya Bilal ya je ya shigo da su bayan gaggaisawa ba tare da ɓata lokaci ba suka faɗa abinda ya kawo su Abba da Yaya Sani da Yaya Bilal suka amsa kuɗin auren bayan 'yar jayayyar da suka yi akan dubu ɗari da hamsin ya yi yawa amma Mai Faskare da kaninsa suka kafe dole sai sun amsa, haka nan suka amsa ba da son ran su ba aka tsayar da ranar aure kwana talatin masu zuwa duk da ba haka Abba ya so ba amma shi Zaid hakan ya bukata a gurin iyayensa kuma Abba yarda ba don rai yaso ba, sun ci sun kuma sha don an daɗe ba a sadu ba Mai Faskare ya ɗauki karamar gorar coke ya tura cikin rigarsa wanda zai kaiwa Zaid shima ya sha, duk yadda Zaid ya so yaga Baseera abin ya gagara kuma saboda ita ya amso aron motar nan amma kuma hakan bai yiwu ba, ko da sakon saka ranar ta iske shi ya yi murna kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha don murna sannan ya kuma hasaso kansa a cikin jerin matasan masu kuɗin shekara mai zuwa....

Da Sallama Umma ta shiga ɗakin ta zauna a gefen gadon da Baseera take zaune ta daɗe tana kallonta idonta a rufe ta sani ba barci take yi ba kawai ta rufe idon ne don ba ta son damu wa, Umma ta kuma jin tausayin 'yarta ya sarketa a zuciya hawaye ne suka cika mata ido ta yi kokarin mai da su sannan ta ce.

"Autata nasan ba barci kike yi kuma kina jin duk abinda zan faɗa miki amma ina son ki sani Baseeratu shi fa aure haka ya gada kuma dukkan mu da hakan muka fara sai dai naki ne ya bani tsoro saboda jiya kina nan kina farin ciki har tsokanarki Mai Nani yake yi, sannan kuma da safen nan ma da walwalarki annuri a kan fuskarki sai kuma na ga akasin hakan a daidai lokacin da iyayen yaron da zaki aura zasu kawo kuɗin aurenki kuma duk kika birkita min tunani da lissafi Baseeratuna, don Allah kar kisa komai a ranki da sannu za ki saba kuma ke kinji daɗi ma a kusa da mu zaki zauna ba wani guri mai nisa za a kaiki ba muna tare a cikin gari ɗaya kuma karki damu in kina son ganina ki kirani zan zo har gidanki na ganki sai na dawo."
       Hawaye ne suka gangaro a idonta Umma tausayin 'yarta ne yake ƙara shigarta sannan ta karasa kusa da Baseera ta ɗaga ta ta zauna sannan ta ce.

"Don Allah Autata ki buɗe idonki ko zan ji sanyi a raina ganinki cikin damu wa babu abinda zai haifar min sai bakin ciki da damu wa, amma in ba kya son ganina cikin damu wa to ki buɗe idonki kuma ki min dariya hankalina ya kwanta kuma in samu nutsuwa a zuciyata."
           A hankali ta buɗe idonta hawaye ya gangaro a idonta ga shi idanun sun yi ja, da kyar ta iya yin murmushin da iya kan shi kan laɓɓanta Umma ta ci gaba da mata nasiha mai ratsa jiki..........

Wannan Ke Nan

_______________________________

Fans sai ku shirya ga fa biki ya kusa sai muje Dubai mu zaɓo anko amma Alhaji Bashir Mai Nani ne za mu ba shi contract ɗin takalmar da zamu sa a gurin bikin, sa'annan duk wacce za ta raka amarya su fara bada sunan su don kar lokacin ya yi Alhaji Zaid Mai Faskare ya kawo jirgin ɗaukan amarya wata tace ba a je da ita mansion ɗin Baseera ba....

KAR KU MANTA DAI NADAMATA! PART 2 ZAI ZO MUKU NE AKAN WATTPAD DINA DON SAMUN LABARIN SAI KU BIYO NI TA HANDLE DINA BASIRA_NADABO

Team BasZad
Team BasFad

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now