POST 24

77 9 1
                                    

"Hajiya ni fa har yanzu zuciyata taki aminta da zamanki gidan nan saboda a 'yan kwanakin nan mugayen mafarkai nake yi akan ki, kuma ke kinki yarda ki koma gidana da zama ni kuma zuciyata bata aminta da zamanki cikin masarautar nan ba."
Cewar Basma, murmushi Fulani Aishatu ta yi sannan ta ce.

"Yarinya ce ke har yanzu Basma, mugayen mafarkin aikin shaiɗan ne kuma don ya kimtsa miki fitina ne tsakaninki da mutanen arzikin da kike zaune dasu ne, amma ni dai ina cikin koshin lafiya kuma haɗe da kwanciyar hankali babu abin da ke damuna haka kuma babu abin da wani mahalukin zai min ba tare da sanin Allah ba, kamar dai yadda na fada miki ne akwai abin da na fara kuma ba zan daina ba har sai na kai ga gaci, karki tashi hankalinki akan sanin hakikanin wannan aikin duk ranar da na kammala zan sanar da ke."

"Amma Ummie ba kya ganin kina cikin hatsari? Rayuwarki fa a cikin hatsari take Ummie kowa ya sani masarautar nan ba sa kaunarki, yadda suka gama da Yaya kanki fa zasu dawo Don Allah Ummie ki biyoni mubar gidan nan."
Cewar Basma.

"A tarihin masarauta kin taɓa ji ko ganin yadda a ka yi hakan? Uwar gidan sarki ta fita tabar gidan sarauta ba tare da ta yi mugun abu ba? Ko kuma kin taba jin inda uwar gidan sarki ta fita a masarauta saboda mutuwar sarki? Ba a taɓa hakan ba kuma ba za a yi a kaina ba."
Cewar Fulani Aishatu, Basma ta yi saurin cewa cikin harshen nasara

"Amma Ummie everything has modified now even the emirs are modified Ummie."
(Ummie komai an yi masa kwaskwarima har gidajen sarauta Ummie)

"Even they are modified Basma i can't do what you want me to do, for me is a big sin in the aspects of our culture."
(Ko da kuwa an masa kwaskwarima Basma ba zan iya yin abin da kike son na yi ba, babban zunubi ne a al'adarmu.)
Cewar Fulani Aishatu, Basma ta kwantar da muryarta ta ce.

"Ummie don Allah ki fahimce ni rayuwarki ita ce abin dubawa, Abban Yaya ne ya ce na zo na taho dake Ummie shi ma kenan namiji kuma shi yake shi ga cikin majalisar masarautar nan su suka san abubuwan da yake wakana a gidan sarautar nan Ummie."

"In Sha Allahu babu abin da zai sake faru wa da ni Basma a yanzu kam na ci dubu sai ceto don babu mai kara nakasar da zuciyata domin ansha ni kuma na warke."
Cewar Fulani Aishatu. Ta kuma cewa.

"Yauwa na manta ban faɗa miki ba mutumin nan ya zo ya yi min aikin yadda yaka mata amma duk da hakan don Allah ki ce masa ya dawo ina da bukatar taimakonsa a karo ba biyu."
Basma ta ce.

"Ummie again! Haba Ummie duk fa wannan basu ba ne hanyar tsira da za ki tseratar da rayuwarki daga mugayen halayyar masarautar nan ba fa, kuma don Allah Ummie ki faɗa min dalilin sake bukatar mutumin nan don nasan ya gama duk wani aiki da zai yi a ɗakin nan ina kuma zai sake zuwa a yi aikin."
Shuru Fulani Aishatu ta yi duk yadda Basma ta so shawo kan Fulani Aishatu abin ya faskara haka ta hakura ta barta ba don zuciyarta ta aminta da uzurin da ta bayar ba..

Zaune take zaune a gaban shi nutsuwa da imaninta duk ta ɗauki kyautarsu da amanarta ta damka a hannunsa, zaune take bisa tsadadden lashin marun kala ɗiki da kalar kayan sun dace da fatar jikinta kamar yadda ta yadda duk wani aikin Malam Zailani dace ne kuma ita dai kam ta dace da daceccen malami managarci da tasirin aikin da babu algus a cikinta, murmushi ne shimfiɗe a bisa kyakkyawar fuskarta bakinta ya ki rufuwa a yayin da kyakkyan hakorin zinarinta na makkah fari tas ke walkiya da haskaka tsiririn wushiryar dake kara ƙayata jerin zaman hakwararta, ya sharce ƙasar ya sake rubutu a kai amma duk da hakan abin dai yake sake gani har abin yaso razana shi, zufar da ya gangaro zuwa sajen fuskarsa ne ya sharce sannan ya ɗago kansa a hankali ya ƙara kallon Fulani Bilkisu dake zaune fuskarta ɗauke da murmushi sannan ya ce.

"Haƙiƙa Gimbiya Bilkisa kin yi namijin kokari gurin gano mana lokacin da 'yarki take haila to amma in da gizon ke saƙa shi ne abin da kike bukata ba zai yuwu ba har sai kin kawo min pant ɗin da take amfani da shi lokacin hailarta."
Fulani Bilkisu ta yi saurin cewa.

"Haba Malam duk wahalar da na sha gurin gano lokacin ma bai yi ba har sai na sake kawo pant dinta kuma? Gaskiya Malam a wannan gaɓar kam zan iya hakura da aikin domin pants ɗinta gaba daya iri ɗaya ce banbancin kaɗan ne kuma ita ce kaɗai take iya banbance kayanta Malam."
Murmushi ya kuma yi sannan ya ce.

"Gimbiya Bilkisa ban taɓa ganin karayarki ba sai yau, yau ɗin ma akan abin da ke kin san za ki iya in har ni namiji zan iya gano miki kalar ɗan kamfai ta (pant) da za ki kawo min amma kuma duk da hakan Bilkisa ina kara tunatar da ke hatsararrukar dake cikin wannan aikin."

"Malam don Allah kabar faɗa min haka ni wani hatsari ne ban tsallake ba? Kai kanka shaida ne a kan yadda nake galaba akan duk wani abin da nasa a gaba kuma ban taɓa karaya ba har sai na ga na haura tsanin nasara akan wannan abin da nasa a gabana don haka Malam ban damu da hatsarin dake ciki ba ni dai kawai kamin aiki, don wallahi Malam Badar barazana ce a rayuwata kuma na tabbata maka watarana da hannunta za a cutar da ni tun da tana goyon bayan maƙiyana."
Cewar Fulani Bilkisu, Malam ya yi saurin cewa.

"Ita wannan bakar tsuntsuwar hakan za a zuba mata ido? Ba za a ɗauki mataki a kanta ba.?"
Murmushi ta yi domin an sosa mata inda ya ke mata kaiƙayi ta ce.

"Malam nima na kan yi wannan tunanin amma in na tuna babu abin da za ta iya yi sai zuciyata ta yi sanyi domin Malam wannan bakar mujiyar babu me kusantarta a masarautar shi yasa ban damu da ita ba, amma bari mu gama da Badar sai a dawo kanta don yi wa tufkar hanci kar kuma ya kasance muna kitso ne da kwarkwata."

"Da ko kinyi wa kanki salama amma tun da kince Badar ce a gabanki to ta kanta za a fara kuma ba za mu tsaya ba har sai munga bayanta."
Cewar Malam Zailani. Fulani Bilkisu ta ce.

"Malam ka ce zaka faɗa min kalar pant ɗin da zan kawo maka domin ka yi aikin nan kuma ba ka faɗa min amfanin kawo maka pant ɗin ba bayan ka ce min lokacin kawai kake bukata kuma a yanzu haka a cikin yanayin da kake bukata take."
Kallonta ya yi na wasu daƙiƙu sannan ya ce.

"Gimbiya Bilkisa amfanin kawo pant ɗin da ta yi amfani da shi a lokacin hailar shi ne, kamar yadda ta ɗauki wannan pant ɗin ta sa haka aikin da zan yi a jikin wandon da zarar ta sa wandon nan aikina zai fara a take gaɓɓan jikinta zai mutu tun daga ƙafafuwarta har lokacin da pant ɗin zai zauna a jikinta to a wannan lokacin ne hatta bakinta zai mutu sai dai ido, kin ga kenan mun gama da matsalar kuma duk malamin da za a kawo babu mai warkar da ita sai dai ni kaɗai domin matukar wandon yana jikinta to babu mahalukin da zai iya warkar da ita, Gimbiya Bilkisa ki nutsu kuma ki maida hankali sosai gurin lura da wannan pant ɗin karki yarda a canja ko da wanka aka mata to lallai wannan wandon shi ne dai ɗaya tilo da zai zama a jikinta.
Wani shu'umin dariya Fulani Bilkisu ta yi har sai da mataunarta suka bai yana. Malam ya ci gaba da cewa.

"Kalar wandon shi ne baƙi da fari kuma a jikin farin ki lura da kyau akwai ɗigon baƙi daga gefen kusurwar yamma a jikin wandon, ki lura ba gabas ko kudu na ce ba a'a yamma."
Ya katse mata dariyar da take yi domin wannan ɗauko wandon shi ne abu mafi wahala akan gano lokacin hailar.

"Yanzu don Allah Malam ta ya ya zan fara samo wannan pant ɗin bayan duk kalolin wandon nata kenan Malam wallahi duk fari da baƙi ne.?"
Cewar Fulani Bilkisu, Malam ya ce.

"Wannan ai kinfi ni sani saboda 'yarki ce ke zaki san ta yadda za ki kawo min kayan aiki kuma in kin kawo da wuri aiki ya fara da wuri in kuma kika yi nawa ke kin san abin da zai faru domin a yanzu zuciyar 'yarki ta fara watsiwatsi akan canja warki da kuma matsa mata kan son sanin lokacin hailarta, don haka shawara ya rage ga mai shiga rijiya."
Jikin Fulani Bilkisu ya yi sanyi matuka saboda iya saninta da Badar kalar pants ɗinta kenan daidai da rana ɗaya bata taɓa canja wa ba, tun yaranta har girma ga shi yanzu Malam ya bata aiki mafi girma da wahala akan duk aiyukan da yake bata ga dai shi nan da sauki a baki amma gurin aikatawar ne mafi wahala, haka tabar gaban Malam da sanyayyen jiki domin duk dabarun nata sun kulle babu hanyar buɗewa..........

Wannan Ke Nan

_______________________________

Haba Fulani Bilkisu ai wannan aikin sauƙaƙeƙƙe ne ko Mom Islam da Fatima Abdullahi har da Yesmien Yola da sauran fans din NADAMATA! A faɗin duniyar nan zasu ta yaki gano wa, haba aikin mai sauki ne a gurin fans dina fa, kuma nasan kina zaune Mom Islam da Mrs Zainab Jega zasu nemo miki pant ɗin...........

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now