POST 21

79 12 0
                                    

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

In Sha Allahu ina gama NADAMATA! PART ONE, PART TWO din zai zo muku tare da BAN KASHETA BA, amma BAN KASHETA BA na KUDIne shima ONE and TWO ne duk mai so sai ya min magana, sannan ONE and TWO din naira 500 ne amma PART ONE kawai dari 300 ne, babu lallai babu dole ga duk wanda bai so amma duk mai so sai ya min magana ta wannan numbern 07030515774 and zan tura muku da details din, call and private chart is allowed for those that interested please.......

MARIRI

Baseera ce zaune cikin tsakiyan dangi sai ta ya ta murnar auren da zata yi suke yi. Ɗaya daga cikin gwaggwaninta ne wacce suke kira da Gwaggo Ramu ta ce.

"Nasan yadda kike da kyau ɗin nan ga jinin sarauta na yawo a ko wani sassa da gaɓoɓin jikinki ba za ki auri ɗan talaka ba wanda ya gaji talauci tun daga kakan kakanni ba, sai ɗan wani attajirin ko kuma ɗan sarauta irinki ko kuma ɗan wani mai faɗa a ji a can binni."
     Tun da Gwaggo Ramu ta fara magana kyakkyawar murmushi ne bisa fuskarta sannan ta yi fari da idanunta ta ce.

"Wallahi Gwaggo Ramu kamar kin sani ai ni ban gaji talauci ba daga ganin zubin halittar surar jikina ya isa ya isar wa mai kallona daga gidan sarauta na fito sannan 'yar attajiri mai ji da arziki ce ni, sa'annan ni Baseera ban yi kalar matar talaka ba haka babu talakar da talauci ya yi masa ƙatutu ya kwaso talaucin kafafuwarsa ya ce ni zai aura ban gan shi ba kuma ba zan taɓa ganinsa ba wallahi, sannan daɗin daɗa wa Gwaggo Ramu mijin da zai aureni ɗan arziki ne wanda ya gaje shi kuma aikinsa  bai fiya yi a nan kasarmu ba sai kasashen masu jajayen kunnuwa."
       Dariya suka yi saboda yadda take maganar da dudduba jikinta haɗe da fari da idanuwa shi ya ke birge duk wanda yake zaune a gurin. Gwaggo Hansatuwa ta ce.

"Ba a ƙasa kika kwaso ba 'yata saboda ko Aishatu ganin kuɗin ɗan uwanmu ne ya sa ta aure shi, saboda ɗan sarauta ne jinin sarauta wanda ya gaji sarautar Takalma wannan dalilin ne yasa ita ma ƙin jinin talaka sai mai kuɗi."
      Ta karashe maganar da hararar Baseera, murmushi Baseera ta yi saboda ba yau suka saba yada wa juna magana ba, kallon ƙasa da sama Baseera ta yi mata sa'annan ta ce.

"Daɗin abin Ummata nitsatstsiyar mace ce wacce ko wani namiji yake burin samu a matsayin matar aure kuma yake burin ta zame masa uwar 'ya'ya, sannan Ummata da budurcinta Abbana ya sa me ta bawai sauran wani ya samu ba kuma har gaban gobe daraja da ƙimar nan tana manne a idon Abbana tunda bai gaji da ita har ta dawo zaman zawarci ba, sannan bari na nusar dake abin da har yanzu kika kasa gane wa Gwaggo Hansatuwa ita fa Ummata da kike gani ta zame muku kadangaren bakin tulu wallahi kuma kishiyar uwa ce dole a zauna da ita ko ana so ko ba a so, sannan walki ce ita daidai ƙugun ko wacce domi..........."
       Marin da Gwaggo Hansatuwa ta mata ne yasa ta kasa karasar maganar da ta yi niyya, ba a yin bori da sanyin jiki itama Baseera ta yi saurin rama marin, gurin ya kaure da shewa ta yo kan Baseera da duka Gwaggo Ramu ta yi saurin rike ta.

"Don Allah Gwaggo Ramu ki sa ke ta yau ta doke ni da kin sha mamakin dukan da zan miki, haka kawai kun samu a gaba me muka tsare muku waye muka kashe muku da zaku ɗauki tsanar duniya ku ɗaura kan Abbana har mu 'ya'yansa bamu tsira ba, to wallahi yanzu muka fara adashin sai mu ga wanda zai fara kwashe wa nabar rage muku mu zuba mu gani shege ka fasa wallahi ni da ku duk wanda ya raga wa wani kar Allah ya raga masa aikin kawai."
        Gwaggo Hansatuwa ma bakinta bai mutu ba ta in da take shiga ba ta nan take futa ba saboda yau Baseera ta karya mata kadari. Duk abinda suke yi Inna Aisha tana gurin kuma ta ji duk yadda abin ya wakana sa'annan ta ji daɗin amsar da Baseera ta bata ta kuma ƙara yaba wa da zafin naman Baseera. Hayaniyar ce ta farkar da Umma da ga barcin da take yi na tsakanin sallar Azahar da La'asar ta tashi bakinta ɗauke da salatin ma'aiki (SAW), gurin da hayaniyar ya ke fito wa ta nufa da isarta ta taradda Baseera ana rirriketa mamaki ne ya cika mata zuciya sannan ta kada baki ta ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now